BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Ina Suawaiba mahaifiyar Hafsa yayar Aisha ce wato mahaifiyar Amjadu itace babba a d’akinsa Hafsa kenan a matsayin kanwarsa take.
Kallon da take masa ne ya dame shi kwata-kwata a rayuwarsa ya tsani kallo shi kam, b’ata fuska yayi ya mik’e tsaye tare da kallon agogon hannunsa, ya kalli Granny tare da fad’in ni zan tafi.” Cike da mamaki tace” zaka tafi kamar yaya? Baza ka tsaya ka ci mutumin naka ba gashi na kwad’anta maka.” Tana nufin zogale. Girgiza kansa yayi kawai ya nufi hanyar futa, kallo tabi shi dashi cike da takaici tace.” Ka tsaya ka ragewa Kanwar ta hanya mana.” Ba tare da ya wai wayo ba yace.” Ki bata kud’in abun hawa mana.” Yayo fucewarsa ya gane manufar granny na aje yarinyar da tayi Dama wancan satin da yazo ta fada masa tayi masa budurwa lallai granny tana da aiki a gabanta.
Hafsa kuwa ji tayi kamar ta tashi ta dawo dashi domin Sam bata gaji da kallonsa ba, ita dai Allah ya sanya mata k’aunarsa a ranta tana fatan Allah ya sa granny tace dole ya aure ta tunda ta lura Sam bata gabansa amma tayi mamaki sosai yanda ya amsa mata gaisuwarta a sake ta d’auka yana da girman Kai ashe ba haka yake ba.
Yana futa wayar shi ta fara k’ara dubawa yayi cike da mamaki numbar me girma governor ya gani, sai da ta kusa katse wa sannan ya daga wayar da muryarsa irin ta jarumai, suka gaisa da shi cikin nutsuwa daga d’ayan b’angaran me girima governor yace.” Kazo Gidan gwamnati musalin k’arfe biyar na yamma ina Neman ka.” Yace.” Insha Allah inan tafe.” Sallama sukayi gaba dayansu kowa ya kashe wayarsa. Murmushin gefan baki yayi kawai yasan karshen zancan wato shime governor yana goyawa su Me citta baya kenan , lallai dole ya tashi tsaye akan haka.
Tunda nayi masa wannan ganin shikkenan na nemi kuzari na na rasa haka muka shiga gida jikina babu k’wari Mimi CE kawai take ta murna tana baya Umma labari, itama sai murna take tace.” Nasan kun kwaso yunwa to ga abunci can cikin Fula’s a kicin yau har nama na siya muku na sanya muku a miya.” Mimi ta tashi da sauri taje ta d’auko mana, tare da d’ebo mana ruwa me sanyi na cikin randa, cin abuncin kawai nakeyi kwata-kwata bana jin tes d’insa a bakina, ganin Umma tana kallona a fakaice yasa na fara yak’e INA biyewa Mimi muna ta labari. Mimi tace.” Umma kinga ankon da muka futar za muyi.” Umma ta karb’a tana dubawa tace.” Aikuwa dai atampar tayi kyau kuma daga ni me tsada CE.” Nace.” Umma ai material din yafi ta tsada shi dubu goma sha biyu ne fa.” Umma ta b’ude bakinta cike da mamaki tace.” Da ubanku ina zan samu kud’in siya muki har dubu ashirin da hudu bayan kud’in dinki.” Nayi karaf nace.” Umma gaba daya Dana lissafa kud’in sun kai dubu arba’in da bakwai da atampar da material din da shaddar.” Umma ta gyad’a kawai tare da fadin ” kun shirya ruguza ni kenan yo ni ina naga dubu arba’in har da bakwai a Hamsin kad’an ne babu, so kuke in rusa jarina inyi muku anko kunga daga baya sai mu koma mu tsuguna muna tsotsar tsamiya.” Jin abunda Umma tace yasa gabana fad’uwa dan gaskiya bana kaunar harkar k’aranta a rayuwa ta bana so ace ba muyi ko wane anko ba, in San samu ne ma da sabbin takalimi da jaka da mayafi.” B’ata fuska nayi ina cin abuncin kamar bana so. Ta kalle ni a nutse tace. ” naga kin b’ata fuska don ubanki so kike in siya muku anko ni kuma Ku karya ni ko, to bazan siya duka ba, Ku zab’i daya a cikin guda ukun, dama si kullum abunda ake fada muku kenan Sana’a tana da dad’i da kuna Sanar Ku da duk babu abunda zai gagareku, ko kuyi bakwa yi da aunty Ku tasan duk hanyar da zata bi ta nemi kudi saboda haka ni babu ruwana.” Shiru mukayi duk murnar mu ta koma ciki. Wasu hawaye ne suka fara zubo min na takaici! Mimi ma ina kallo idonta duk ya ciki mda k’walla Umma tace “kuyi kukan jina ma ni babu ruwana.” Yaya Aminu ne ya shigo dakin da sallama a bakinsa Umma ta amsa masa ya zauna yana kallonmu cike da mamaki hankalin shi yafi karkata kan Mimi yace.” Meye suke kuka.” Nan Umma ta warware masa abunda yake faruwa.
Dariya yasa tare da nuna Mimi da hannu yace.” Sam kuka baya yi miki kyau gwara ma ki daina.”Mimi ta zumb’ura bakinta yace.” Nawa ne kud’in atampar.”? Da sauri nace” dubu hudu ce .” yace.” To zan bada shikkenan ko.” Sakin fuska mukayi dukaninmu nace “to shaddar fa.”? Hararata yayi yace.” Wannan kuma sai Ku nemi Wanda zai siya muku.” Mimi tace.” Asma’u ina ganin in muka samu guda biyu ma ai mungode Allah.” Shiru nayi mata domin ba haka naso ba.” Umma tace “sai Ku nemi kud’in dinki don wallahi kuka d’auko dinki me tsada me cin kayan dinki to bazan biya ba.” Nace. ” Umma kinsan shi material din fa dole sai anyi masa bauta an siyi shafi da sauransu gaskiya zai ci kudi sosai, bayan haka kuma don Allah ki siya mana sabbin takalma”. Hararata tayi kawai ta juya suna magana da Ya Aminu.
Biyar dai_dai yana gidan gomnati nan aka yi masa ido har ofis dine me girma governor ya zauna kan wata lumtsime miyar kujera suka gaisa a tsana ke, me girma governor ya kallashi sai ya ji gabansa na fad’uwa ganin yanda Yaro yayi masa mugun kwarjini, yace.” Bisimillah ga ruwa kasha.” Amjad yayi murmushi tare da fadin.” Nagode me girma shugaba.” Bayan yasha ruwan ne me girma governor ya kalle shi a nutse yace.” Hausawa suka ce maganar gizo bata wuce ta k’ok’i na San ka fahimci dalilin da yasa na kira ka.”? Yace.” Ban fahimci komai ba ina Neman Karin bayani.” Governor ya gyara zama tare da fadin.” Har yanzu muna kan bakanmu na ka rushe company naka ko kuma ka tsawwala farashin kayanka, saboda ni kaina na zauna nayi nazari da tunani ba ‘yan kasuwa kad’ai abun yake tab’awa ba har da gomnati ina fatan ka fahimta, gomnati na karb’ar haraji a hannun ‘yan kasuwa idan ba k’ara farashin kayan ka ba to tabbas zamu tsawwala wa ‘yan kasuwa kud’in haraji kuma za mu rushe shagunanmu Wanda gomnati ta gina zamu kori duk wani dan tebur da Wanda bashi da shago zamu watsa su daga kan titi, wannan shine matakin da muka d’auka.
Ido jazur! Ya d’ago kansa yana kallon governor din yace.”Allah shi baka nasara da kanka kake wannan ikirarin? Wato har kamanta ranar rantsuwa kenan ? Ka manta ranar da ka dafa alk’urani me girma ka rantse dashi? Ka manta ranar zab’e da wahalar da talakawa suka sha akanka rana zafi sanyi ruwa talaka ya tsaya kai dafata ya dangwala maka kuri’a duk ka manta wannan ranar me girma Governor. ” ya k’arasa maganar tasa cike da tuhuma.”
Me girma governor yaji duk jikinsa yayi sanyi jin yaron yana so yayi masa warwara nan take ya fara nad’e tabarmar kunya ta hanyar buga tebur din dake gabansa yace.” Duk wannan abunda kake fada basu shafeka ba, lokacin zab’e na futo da kudi Wanda ni kaina bansan iya adadinsu ba, an rabawa talaka INA so ka sani talaka a yanzu ya fi bukatar ka bashi Dari biyar ko ka bashi sabulun Wanka sink’i d’aya akan ‘yan cinsa, saboda haka rik’e alkawari da sauransu duk bai shafe ka ni dai ga hukuncin da na yanke! Idan kuma kak’i karb’a kai kanka sai mun rusa ka da duk abunda kake tak’ama dashi.”
Murmushi me ciwo yayi ido jazur yake kallon governor din yace.” Ita kuma rantsuwar da kayi fa? Allah ba abun wasa bane.”
Governor ya daga masa hannu a fusace! Yace.” Kai kasan Allah ne ? Dubi askin dake kanka, duk abunda kake muna da labarin sa ka bude hotal har guda biyu ana tata iskanci a ciki kai kanka kana iskancin ka da mata zaka zo kana fada min Allah anan gurin.” Murmushi Amjad yayi cike da takaici wai shi governor zaiyi wa gurin yana Neman mata, mutumin da kowa yasan shi mugun asharari ne me mugun son mata da shaye-shaye shiyasa lokacin zab’e ‘yan daba ya baza ko ina suna raba kudi tare da tsorata alumma da jajayen idonsu mik’ewa yayi a fusace! Ya kalle shi yace.” Ina nan kan bakana babu gudu babu ja da baya company kuma yana zaune daram! Sannan kuma bazan kara farashin kaya na ba.” Yana gama maganar sa ya futa daga ofis din cikin zafi.!