BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Governor ya bishi da kallo da baki a sake, waya ya d’auka ya kira shugaban kasuwar k’wari yace.” Yanzu-yanzu a rufe a shaguna kuma a watsa ‘yan tebur da suke kan hanya.

Aikuwa haka ce ta kasance ‘yan kasuwa na hidima da kaswancin su tare da customs kawai sak’on shugaban kasuwa ya riske su, da ya yawun me girma governor, hankali a tashe suka fara rufe shaguna kowa na fad’in.” Albarka cin bakinsa.
Tun kafin ya isa gida labari ya riske shi, ranshi a b’ace ya dauki wayarsa ya kira governor din shi kuma a nashi b’angaran ya dauki wayar da sauri yana wani mugun murmushi ya d’auka Amjad din ya sauko daga kan kudirinsa yasan dai yanzu labari ya same shi, muryar shi sama-sama yace.” Ina kan hanya ta ta komawa gida na samu labarin abunda ya faru yanzu, ina so in fada maka wani abu, daga nan ba zan zame ko INA ba sai gidan redio zanje in warware musu zare da abawa.” Saura kad’an governor yayi hantsile daga kan kujerar da yake zaune baki narawa yace.” Kar ka kashe min waya ka bari kaji abunda zan ce da kai.” Murmushin takaici yayi yace.” A banza abunda baka sani ba shine duk wata shira da ta gabata a tsakanina da kai ina d’auke da ita cikin wayata so a tafin hannuna kake.” governor ya goge wani zazzafan gumi da yake tsatstsafo masa a goshi lallai yaron nan bashi da mutumci wato ya samu zagin da jama’ar gari suke masa kwana biyu ya lafa shine zai dawo dashi, baki na rawa yace.” Kar……..Amjadu ya katse ta hanyar fadin ” baka da abunda zaka ce min a halin yanzu kawai ka janye kudirin ka nima in janye nawa.” Governor yace.” Na janye gobe kowa ya futa kasuwa kai kuma ka saurari abunda zai biyo baya.” Murmushi kawai yayi ya kashe wayar ba tare da yace uffan ba.”
.governor ya tsaya kawai yana kallon fuskar wayarsa yana mamakin yaya akayi yaron ya samu dama akanshi har ya raina shi, da matsayinsa yana matsayin shugaba amma yake kashe masa waya lallai ya zama dole ya hukunta shi.

Rai a bace ya shiga gida ana ta kiran sallahar magariba alwala ya d’aura nan cikin bedroom d’insa yayi sallah, waya ya kira Rambow ya je ya siyo masa abunci domin wata yunwa yake ji,ga uban hayak’in sigari da ya babbakawa cikinshi a mota sai da ya shanye a kwali guda kafin su shigo gida.

Mintuna ashirin tsakani Rambow ya shigo dakin hannunsa rik’e da wata Leda me kyau da k’yalli ya aje masa tare da jira ko akwai wani umarni daga masa hannu kurum yayi alamun ya futa, cike da bin umarni ya futa daga dakin. Ledar take away din ya jawo yana dubawa abuncin be masa ba ya rufe jingina yayi jikin gadon shi yana tunanin yanda za’ayi ya warware wannan Matsalar da take tun karo shi.


11:00 dai-dai abun ya afku gidajan redio na shirin rufewa suka samu labari babu shiri suka tafi domin d’auko rahoto, yana zaune inda yake tun d’azu ya fara jin kira na shigowa wayoyin shi, daukowa yayi yana dubawa Wani d’an kasuwa ne da ya shara ya kira shi suka gaisa hankali a tashe yace.” Yallab’ai Ashe abunda ya faru kenan kai Ubangiji Allah ya tsare ya kiyaye gaba gaskiya muna cikin tashin hankali.” Amjad ya kasa fahimtar maganar sa kawai ya aje wayar ya dauki dayar zance dai guda ake masa, Zumbur ya mike ya futo parlor yana shirin bude kofa ya futa sai suka buga karo da rambow zai shigo hankali a tashe, abunda ya d’auke masa hankali abunda yaji wani Dan jarida na fada a wayar Rambow inda yake cewa” Inna lillahi wa ina ilahi raji’un, a yanzu ne muka samu labarin mummunar gobarar da ta afku a katafaran company nan na Amjadu ABUL Abbas company da ya shahara gurin kawo kaya masu kyau da karko gami da sauk’i da saukakawa talaka…….”

26/October/2019
[11/1, 10:55 PM] .: [10/26, 11:33 PM BABBAN YARO

Mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.

30

Innalillahi wa’inna ilahi raji’un.” shine abunda ya futo daga bakin Amjadu da sauri ya koma bedroom din nasa jikinsa na kyarma! Ya dauki wayarsa yana laluben numbar manager, har wayar ta katse bai d’aga ba, ya kara kira a karo na biyu shiru bai d’auka ba. Parlor ya futo yana kara kiran wayar.wannan karon tana shiga manager ya d’auka babu abunda ya futo daga bakin Amjadu sai “Bashir ina fatan babu Wanda ya rasa ransa ko.”? Manager yace.” Eh yallabai babu Wanda ya rasa ransa sai dai akwai wad’anda suka samu rauni gurin ceton ransu.” Yace.” Maza ka had’a Kansu Ku wuce hospital me zaman kansa ganin zuwa.” Manegar yace.” Insha Allahu haka za’ayi.” Kashe wayar yayi ya dauki dayar da take aje kan bed an kira yafi sau goma, Sam bai tsaya daga wa ba domin yasan duk zance daya ne. Futowa yayi rambow da doh-doh suka rufa masa baya.

Kai tsaye company suka nufa cike da tashin hankali da tarrarabi, kafofin yad’a labarai sun rud’e da zancan ko wacce ka kamo maganar gobarar ake wanda suke fad’in an rasa meye musabbabin ta. Kafin kace kwabo labari ya watsu a birnin kano da kewayen ta, cikin daran ‘yan kasuwa suka dinga futowa daga gidajansu suna jajantawa junansu kungiya wasu sukayi suka nufi company cike da alhini da tashin hankali.

Ido jazur!! Yake bin company ninsa da kallo ya k’one kurmus! Ko ina ka d’aga kai sai hayak’i yana tashi gurin ya hautsine da ‘yan kwana-kwana gami da mutanan gari kowa na bada gudumar sa.” ‘Yan jarida sun kewaye shi sun fi su goma dukaninsu suna son suji ta bakinsa. Duk inda yayi sai sun bishi suna fadin.” Young millionaire Amjadu “Ko zaka fad’a mana wane irin hali kake ciki na wannan Abu da ya faru da company min ka me tarin albarka muna bukatar jin ta bakin ka.” Shiru yayi musu kawai hannusa goye a bayansa yana zaga loko da sako na ko ina hannunsa ya mik’a ya karb’i wayarsa gurin rambow, nan ma ‘yan jarida suka yi masa caaaa!!! Masu d’aukar sa hoto nayi masu vedio nayi masu kafa masa lasifika a dai-dai bakin sa nayi, wai Dole sai sunji me zai ce a wayar.
Numbar Manager ya kira bugu d’aya ya d’auka tare da fad’in.” Ranka ya dad’e.” Cikin jarumta da dakiyar zuciya yace.” Yaya ina fatan babu wata matsala duk Wanda yake bukatar taimakon gaggawa ayi mishi kan lokaci. ” manager yace.” Insha Allah ranka ya dad’e gashinan ma ana musu dressing raunin ka da suka samu.” “Kuna wane hospital ne.”? Manager yace.” Malam. Aminu kano.” Ok ganin zuwa.” Ya fad’a yana kashe wayar.” Yuuuuuuuu!!! Suka bi bayansa tare da sake maimaita masa maganar d’azu. Doh-doh ya juya da sauri yana zare musu ido!! Oho ko a jikinsu, hummm! D’an jarida da nacin tsiya. Wani ne yayi tsagal!! Ta tari gabansa ya kafa masa lasifik’a a baki Tare da fadin.” Ranka ya Dade ka taima kayi mana magana muna mutukar bukatar muji ta bakin ka akan wannan al’amari da ya afku.”!!
Murmushi yayi Wanda kana ganinsa kasan na bakin ciki ne, yace.” Kuna so ku ji ta bakina.”? Duka suka ce k’warai kuwa ranka ya dad’e. Cikin basarwa yace.” Komai dai ya samu bawa daga Allah ne cikar mutum mumini yarda da k’addara me kyau da mara kyau.amma wani abu yakan samu d’an adam wani ya zama shine mujaza faruwan al’amarin,saboda haka ina me tabbatar muku da cewar wannan abun da ya faru to daga sama ne kuma wasu ne suka zama silar faruwan shi, zan muku misali. D’azu misalin k’arfe shida da rabi na yamma kun Sanar a k’afafun yad’a labaran Ku cewar ‘yan kasuwa su dakata da futa sai zuwa ranar da gomnati ta umareshi, kafin awa guda da yad’a labaran Ku kuma Ku k’ara ‘yada wa cewa umarni daga gidan gomnati wannan magana an janye ta, da wannan nake rufe magana ta, dukkanin ku kuje ku tsaya kuyi binkice kanta sai Ku samu abun yad’awa a duniya.” Tsitt!!! Gurin yayi tun sanda ya fara magana har ya k’are kowa na sauraren sa, wucewa yayi da sauri yaran shi suka rufa masa baya. Kafin kace kwabo gurin ya kara hargitsewa kowa na fad’in albarkacin bakinsa, mutane da dama sun fi zargin wannan al’amari daga abokan adawar sa ne, wasu kuma suna zargin daga gidan gomnati ne kowa dai da abunda yake fad’a.
Kai tsaye hospital Malam Aminu kano suka nufa, sai da ya tabbatar da duk Wanda ya samu hadari a jikinsa ya samu kulawa sannan hankalinsa ya kwanta. Suka kara dawo wa company Wanda har yanzu ake aikin gurin tare da futo da kayan da sukayi dame ji wasu a jibgi-jingi wasu sun ci wuta wasu kuma ta fara cinsu basu gama k’one wa ba, sama da k’asa ko ina ka kalla bak’ikirin babu kyawun gani babu wani abun da za’a mora a gurin. Wani ofis ne a harabar gurin, nan yaranshi suka shiga suka gyara mishi dake akwai guraran da wutar bata same su a kasan gurin, nan ya shiga ya kwanta kan wata k’atuwar kujera ya rintse idonsa zuciyarsa kamar zata futo fili.babu Wanda ya fad’o masa a rai sai mahaifin sa, a take ya mik’e ya dauro alwala ya shimfid’a abun sallah dai-dai ta tsayiwarsi yayi gaban sarki jallah wa ala yana mik’a mishi bukatunsa, sosai yayiwa iyayansa addu’a ya shafa, sai yaji zuciyarsa tayi sanyi, a gogon hannunsa ya kalla uku da rabi na dare, har yanzu yana jiyo hayaniya,jama’a a waje da alama har yanzu basu gama futo da kaya ba, mik’ewa yayi ya nufi window tare da dage labulen yana lek’en gurin. Aiki kurum suke kamar kara cab’a gurin suke, ga uban kaya nan dila-dila a watse a harabar gurin duk sunyi dame ji. Ko mawa yayi ya zauna yana tunanin wane mataki zai d’auka kansu Alhaji Hashimu me citta dashi kanshi me girma governor nan.
A takaice dai Amjad da duk wani me kaunar sa a ranar kwana sukayi cike da bakin ciki gami da damuwar abunda ya faru. K’arfe shida dai-dai na safe k’afafun yad’a labarai suka fara labaran su, inda kowa ce tasha ka kunno a lokacin sautin muryar Amjadu ce inda yake yiwa ‘yan jarida baya ni. Tofaaaa!! Gari ya haustine kowa na zagin me girma governor tare da fadin cewar da sanya hannunsa haka ta faru tunda shi Amjadu a baya nin da yayi yayi magana me kamar jiryewa Wanda hausawa suke cewa me kamar Wanka. Tuni k’ananun’yan kasuwa suka shirya zanga-zanga tare da makamai da tayoyi suka nufi gidan gomnati. Matasan gari marasa aikin yi suma suka rufa musu baya. Hankalin me girma governor ya kai k’oluluwar tashi! Sam! Ba zaici haka jama’ar gari zasu tada hankalin su ba, tuni ya baza matakan tsaro cewar a tsare hanya kar a bari kowa ya k’araso a rufe titi gami da dakatar da ababen hawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button