BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Daf! Da zan shiga ciki. Na hango rambow yana buge mutane dake kan hanya tare da fadin” tunda dai magana ta fatar baki batai muku ba to bari a gwada muku k’arfi da bulala duk idon Ku ya rufe, ana ta magana tun d’azu Ku bada hanya za a wuce kun ki Ku bayar.”
Aikuwa sai mutane suka fara bud’e hanya cike da tsoro ganin babu Imani a don rambow.
Kafin in ankara na hango shi ya tawo cikin yanayin tafiyar sa ta jaruman maza doh-doh a bayansa da wasu ‘yan jarida guda uku masu mugun nacin tsiya sunk’i tafiya. Neman gurin b’oya nake duk na gigice, da ganinshi Sam! Na tsani raini, nan take na fara Dana sanin zuwana gurin , bayana na waiwaye babu gurin b’uya mutane ne cukunsu suna Neman bangaje ni in fad’i saboda son ganin shi, ‘yan matan dake gurin kuwa kamar su shid’e dan dad’i sai kara zura kai sukeyi tun kafin ya k’araso gurin ya hautsine da ihu!! Kowa na fad’ar albarka cin bakinsa akan sa,, nayi diri-diri dani gashi dai hanya ta rabu biyu gashi ina kusa da gete, daf da zai k’araso na sunkuyar da kaina kasa cike da takaici nake bin kojalallan hijabin jikina da kallo duk ya kode Allah ya isa nayiwa aunt Hauwa.

Dai-dai saiti na wani Dan jarida ya tsaida shi dole ya tsaya yana bashi amsa dai-dai da abunda ya tambaye shi.

Dan jaridar yace.”* Young millionaire muna son mun san cewar yanda kake da masoya gaba da baya shin kana sha’awar siyasa ko kuwa domin ga dukkanin alamu matasa da dattawa na mutukar kaunarka kuma kai ma zakayi kyau da mulki domin anfi bukatar jajirtattu irin Ku..” Wannan maganar tasa ya tsaya yana basu amsa kamar haka.

Sam!sam bana sha’awar siyasa bani da ra’ayin ta domin babu komai a cikinta sai zubewar mutumci bayan haka kuma ka dauki alk’awari ka kasa cikawa bana sha’awar mulki ko wane iri ne shine magana ta gurin ya hautsine da sowa matasa na fadin “Mu muna sonka kuma zamu tsaya maka lokacin zab’e.” Abun mamaki har ‘yan matan dake gurin ma ihu suke yi cike da rashin kamun kai. Takaici yasa na kasa dago kai na kalle su, Allah-Allah nake ya bar gurin. To shima nashi b’angaran haka ne lallai ya yarda da aikin Jarida su ne suke tsokalowa mutum tsuliyar doh-doh yana zaman zaman sa zasu jawo masa wata uwa Siyasa sun ki su k’yale shi sai tambayar kwakwa suke masa……….Dama abunda suke so su ji kenan daga bakinsa don haka sai suka k’yale shi. Gani ya kusanto inda nake tsaye yasa na kara sauke kaina kasa kamar wata muna fuka, ya karaso cike da jarumanta yana dagawa mutane hannu fuskarsa a sake, take sosai. Wani matashin saurayin ne majiyin k’arfi ya ingiza ni gaba duk a. K’okarin shi na lallai sai Amjadu ya ganshi
Saura kad’an kaina ya daki k’irjinsa nayi saurin rik’e gefan rigar shi Dan kar hakan ta kasance, gabana ya dunga bugawa fatt!!!fatt!! Kasa d’ago kaina nayi i n kale shi domin nasan k’aryar b’oye b’oye ta kare, Allah ya Isa kwai nake wa saurayin nan……………. Gefen fuskarta ya kalla ya gane ta, mamaki fal! Cikin zuciyarsa me ya kawo ta gurin nan cikin garadan maza don tashi kamun kai…Fuska!! Yayi kamar bai tab’a ganin ta ba ya mugun had’e fuskarsa tam!! Ya wuce abunsa! Ya ransa na binshi a baya, jama’a sai a sauka lafiya suke masa.

Zama yayi cikin motar zuciyarsa babu dad’i, ya kalli Rambow murya a sama yace”waccan yarinyar me ya kawo ta gurin nan.?” Rbow ya diririce! Ganin yanda ogan nasa ya tsare shi da ido! Yace.” Boss myebe tazo itama ta samu rabonta ne.” Cike da taikaci yace.” Jeka zo min da ita.” Rambow ya tafi da sauri! Dube-dube kawai yake a gurin bai ganta ba, ciki ya shiga nanma ya dunga ware ido cikin jama’a babu ita, ciki ya shiga sosai yana dubawa.

Ni ko na shiga ciki sosai ina Neman su auntn Hauwa sun bace min cikin mutane, nan cike da takaici da haushi na futo daga wani sako inda naga wasu mata sun taro a gurin suna jidar kaya, hanyar futa na nufa raina a dugunzume ! Ina jin takaicin kallon banzan da guy nan yayi ya ma nuna kamar be sanni ba lallai ma!! Ga takaicin su aunt Hauwa ya hana ni magana. Kawai naga an tari gabana. Ina daga kaina muka hada ido da Rambow naji faduwar gaba, amma dake ina da taurin rai! Nace.” Meye haka.” Yace.” Boss ne Yace.” Kizo.” Harararsa nayi nace “ni matsa don Allah ‘yan uwana nake nema mu tafi gida.” Rbow yace.” Yace in kiyi gaddama to in daukoki aka in kai masa ke..”
[10/28, 10:35 AM] .: Shek’e ke na kalle shi na sha kunu mutuk’a nace.” Bisimillah sai ka d’aukar masa ni ka kai masa wallahi idan baka matsa min daga nan ba zan maka ihun kwarto in tonawa uban gidan naka asiri a gaban bainar jama’ar da suke ganin mutumcin sa.” Ganin yanda nake zare ido ne yasa rambow Ciro wayarsa ina jinsa yana fadin” Boss gatanan tana gadda had’e da surutai.” Ban ji me ya ce ba, kawai naga rbow ya mik’o min wayar. A banza ce na kalle shi shi da wayar na watsar tafiya na fara yi, rambow ya biyo ni a baya, ganin rbow ya nufo kofar futa ne yasa jama’ar dake kan hanya suka bud’e hanya na wuce huff!!! Da sauri na b’uya bayan wata mata, aikuwa yaron ta dake goye a bayanta ya kwala ihu ta juyo da sauri tana k’okarin sauke shi, wannan ya bawa Rambo damar gani na. Tsaki nayi na futo daga bayan matar domin bana so jama’ar dake gurin su fuskanci wani Abu,kawai sai nayi gaba, to dake suma hankalinsa na kan duba kaya Sam! Babu Wanda ya damu dani.

Tunda ta doso bakin titin yake kallonta yaga fuskarta sai shaining take ta wani kara bak’i. Tsaki yaja cikin zuciyarsa yace.” Saboda rashin abinyi ta futo daga gida sai kace korarriya ko ‘yar gudun hijira. Daba Dan yayi mata kyakyawan sani ba Sam ba zai ce ita CE ba. Yana kallon rambow nayi mata magana ta share shi. A fili yace “dama irinku munana kun fi wulakanci.

Asma’u kuwa kai tsaye titi ta nufa ta fara tafiya domin yanzu hankalinta yayi Gida ta nemi su aunt Hauwa ta rasa ga Uwar yunwa na damunta gefe guda kuma matsanancin tsoron rbow ya fara shigar ta ganin da tayi yana bin ta duk inda ta sanya k’afar ta sai kace tsohon maye titi ta mik’a sosai tana Neman a dai-dai ta sahu. Tsoro take kar mutane sum ganta da rambow din.

Umarni ya bawa doh-doh kan ya ja motar a hankali ya fara Jan motar har suka iso daf! Da ita, sauke gilashin motar yayi . gabana ya fad’i nayi saurin kauda kaina gami da kara sauri!!! Rbow ya tari gabana cike da b’acin rai! Yace
” kawai ki bi umarni shine mutumci ki domin duk Babur din da kika tsayar baza mu barshi ya d’auke ki ba, kije kiji me oga zai fada miki.”

Babu yanda na iya haka na koma baya fuskata kirne……. Na tsaya gaban motar INA kallonsa gami da fadin “gani” girgiza Kai yayi fuskarsa a had’e yace.” Shiga mota mu tafi.”

Shiga mota mu tafi.” Na maimamata maganar da yayi a fili cikin sigar tambaya.?
Kai ya gyda min yana wani lumshe min mutsiyatan idanunsa masu dafi.! Kai tsaye! Nace” ina zaka kaini in na shiga motar taka.”? Kallona ya danyi a fakaice yace.” Gidanku. Naga rana tayi kingaji ga alamu nan sun nuna fuskar ki sai maiko take sai kace an toya mankuli.
Da sauri! Sanya gefan hijab dina na hau gogewa ina zabga masa muguwar harara. Murmushi naga yayi ya Dan kanne min ido daya cike da iya shege! Kauda kaina nayi cike da takaici nayi gaba da sauri!! Hannusa ya zuro ta tagar motar da k’arfi ya rike min gefan hijab dina, yana fad’in ” yarinya za’a taimake ta tana k’i saboda tsabar gaddama idan baki shigo ba zan zo in d’auke ki a ka”. Yanda ya fad’i maganar yasa na juyo ina kallonsa a fusace!!! Nace “Sakar min hijabi na.” Shan kunu ! Yayi sosai ya kalli rbow yana masa magana da ido! Tsorata nayi ganin rambow yayo kaina gadan-gadan, da sauri na bude mota na shiga! Gefe naga ya matsa yana d’an ya mutse fuskarsa bai ce komai ba Rambow ya maida murfin ya rufe ya zagaya kusa da doh-doh ya zauna sannan muka tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button