BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

A hankali naji yace. ” Rambow mik’o min turaran k’amshin nan.” Wani durmeman turare rbow ya miko masa cikin kwalinsa ya bude ya hau fesawa cikin motar ya dawo kaina yana min feshi, saurin kauda kaina nayi ina kare fuskata, lokaci kankani na fara atishawa, sai da motar ta d’umame da kamshi sannan a maida turaran cikin kwalinsa.

Yanzu na gane dalilinsa na fesa turare cikin motar wato yana nufin wari nake kome? Aikuwa kafin in gama tunani na naji shi yana fadin.” Duk kin sauya min k’amshin motar da warin rana ‘yan mata masu daraja.” Shiru kamar ruwa ya cinye ni, ji nake kamar in d’aura hannu aka in ta kurma ihu! Ko nasamu sassauci a zuciyata nace ban tab’a ganin Mara mutumci ba irin guy nan wallahi.

Ni ko nace Ashe babu dad’i Asma’u ita Hafsa ba mutum bace kenan????

Kafin in gama tunani na naji shi yana fad’in” muje gida ki dauki a jiyar ki dama Neman ki nake.” Kallonsa nayi da idona da ya fara ciko da kwallah nace” wace ajiyr ? Kaga malam ka kaini gida kamar yanda kace cikar mutum rike alkawari.” Murmushin gefan baki yayi na kauda kaina ganin yanda yayi wani bala’in kyau kullum kara mishi kyau ake da kwarjini yadin jikinsa yayi masa bala’in kyau!!! Yace.” Kin manta ne kawai amma muje zan nuna miki ko meye? Nace.” Babu inda zanje ni.”

“owk wai ma me ya kawo ki gurinan ne kina a matsayin mace me daraja kin zo kina bugun kirji da gogayya da maza wannan shine darajar.”? Ya fada cikin sigar tambaya gashi ya wani sha kunu!
Rashin abun cewa ne yasa nayi shiru ina sadda kaina kasa nasan dai wannan tambayar da yake min ta rainin hankali ce tunda dai ya san ko meye ya kawo ni………”Uhum ke nake sauraro.”? Yafad’a cikin wani irin hosky voice, ji nayi jikina ya soma rawa muryar da yayi amfani da ita tayi bala’in tasiri a gare ni…. Shiru nayi kawai yace.” Ok na fahimta.” Yanda ya fad’i maganar yasa na d’ago Kai ina kallonshi cike da jin haushi nace” kar kayi tunanin muma munzo ne domin mu d’ebi sharar company nin ka, ko d’aya hanya ce ta biyo damu ni da ‘yan uwana.” Na k’arashe maganar a daburce!! Wani kallo yayi min kana ganin kallon kasan na iskan ci ne a hankali yace.” Allah ko.”? Nace.” K’warai kuwa domin ni banzo nan domin in samu sutturar sawa a jikina ba tunda ina dasu.” Munafukin murmushi yayi yace.” Shiyasa naga kin dage kina gogayya da garada kina turmutsawa cikin jama’a domin ki shiga to me zaki shiga kiyi uhummmmm.”!!!!!! Wasu tagwayen hawaye ne suke k’okarin tsinke min.sai na aro dauriya da jarumta na kalle shi had’e da kankance idona nace.” Eh hakane to yanzu ai sai ka duba ka gani ko na d’auko wani Abu da na shiga ciki. Ma ‘yan uwana nake nema mu tafi gid…………. Katse ni yayi ta hanyar fad’in” wannan duk preetandig din da kike bashi da amfani ni dai nasan duk Wanda yazo gurina to akwai abunda ya kawo shi.” Da sauri na bude handbag dita na Ciro kud’in ankon mu cikin gadara nace.” Kaga kudinmu nan yanzu haka kasuwa zamu shiga muyi siyayyar kayan sawarmu babu abunda kayan ka zasuyi mana.” Kud’in ya wafce!! Daga hannuna.” Na kalle shi a tsorace! Cikin aljuhu ya zura. Nace “me kake nufi”? Ba tare da ya kalle ni ba yace.” Nima Dan kasuwa ne bayan haka kuma dama na karye makiya sun taso ni a gaba ina Neman jari ki taimaka ki bar min su.” Nasan Neman magana yake kawai sai naja bakina nayi shiru.

Shima shiru yayi bai sake cewa komai ba, minti biyar a tsakani wayarsa ta fara k’ara, d’auka yayi cike da karsashi yayi sallama, naji yana fad’in”Kanwa takar tsami kwarnafi ya kwanta me citta burinku ya cika.” Banji abunda yake ce masa, sai dai ganin da nayi ya zabura!!! Had’e da dukan glass din motar da hannunsa yace.” Da kai da shi me girma governor dukanin Ku a tafin hannuna kuke wallahi akawai ranar tonan asiri. Kuma Ku zuba ido nan da sati guda kuga abunda zai faru.”

Yana gama maganar shi ya kashe wayar gaba daya yana wani irin huci!
Kallonshi nayi a sace sai naga fuskarsa a had’e kamar bai tab’a dariya ba, kauda kaina nayi kurrum ina sak’e -sak’e a zuciyata a game dashi.

Shiru motar sai gudu take zubawa kan kwalta babu Wanda yayi magana, a hankali naji yace.” Doh-doh juya da motar nan muje Mudansir and brothers dake Sharad’a kwanar ganduje.” Da sauri doh-doh ya juya motar yana fadin “Yes sir” ni dai shiru kawai nayi ina bin titi da kallo har muka Isa make kenan gurin inda naga manya manya motoci a fake a gurin had’e da had’addan ‘yan mata masu aji da waye wa wasu na shiga wasu na futowa.

Parking yayi gurin da aka tana da ya futo da sauri had’e da budewa oganshi motar ya futo fuskar nan kamar hadari ya kalle ni cike da bada umarni yace.” Futo mu shiga ciki ji zab’i duk abunda yayi miki.”

Gabana ya fad’i! Na hau duba jikina cike da tsarguwa. Shima kallona yake yi minti biyu yace.” Ki futo mana ai naji dad’i da kika sanyo wannan hijabin domin ya kara miki masifar muni nasan babu Wanda zakiyi wa kwarjini.” Hararsa nayi tare da cewa.” Ce maka akayi ina bukatar wani Abu a gurin nan.” Girgiza kai yayi yace.” Baki fada ba ni nayi niyar siya miki ai nasan kin fi k’arfin su Big girl.””””” Yanda ya fad’i maganar a tsaye yasa na gane shagub’e yayi min. Cike da takaici na bude motar na futo duk sai na tsargu da kaina sai gyara hijab nake ina goge fuskata cikin wayancewa.

Gaba yayi cikin takunshi na jarumai na bi bayansa kamar munafuka, su rbow suka rufa mana baya.tunda muka doso kofar shiga mutane sukayi mana chaaaa!! Da ido sosai mussaman ‘yan Matan dake gurin kai har da Matan aure ma, ma’aikatan gurin sai kwasar gaisuwa a gurinsa, yana amsawa ta hanyar daga masu hannu, ganin yanda ‘yan Matan suke kallonsa ne ya bani haushi wasu kuma sai watsa min kallon kyama suke yi cike da raini da takaicin ganinmu tare dashi, sunkuyar da kaina nayi a zuciyata nace”Allah yasa dai kar jama’ar dake gurinan suma suyi min kallon ‘yar gudun hijira…..

28/October/2019
[11/1, 10:55 PM] .: BABBAN YARO

Mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.

32

Masu tsaron kofar ne suka mik’e tsaye cike da girma mawa suke gaishe shi ya amsa a nutse, had.e da hawa stepe domin shiga ciki bayansa nake bi kamar munafuka, muka shiga, da sauri rambow ya d’auko masa wata lafiyyayer kujera ya zauna yana d’an nazarin gurin a nutse yace.” Ku shiga da ita ciki duk abunda take so ta d’auka.” Rambow yace.” OK sir.” Suka yi gaba ni kuma na tsaya, so nake mu hada ido dashi ya k’i ya kalleni har yanzu ina jin ciwon rashin mutum cin da yayi min a mota, na fi minti uku a tsaye bai ce min komai ba, nace” bani kudina .” ko kallo ban ishe ba. Ya d’auko wayarsa yana dubawa, k’aramin tsaki naja nabi bayan su Rambow ….. Shi kuwa Amjadu a tsarge yake zaune s gurin yasan dama dole haka zata kasance dashi a rayuwarsa ya tsani kallo wallahi bai San me yasa ba mata suke damunshi da kallon tsiya, tsaki yayi ya mik’e da sassarfa ya futa daga gurin, kai tsaye mota ya nufa

Yana barin gurin jama’a suka fara surutu wasu ‘yan mata dake gefena naji suna fad’in” Ikon Allah ko meye alak’ar young millionaire da wannan ‘yar talakawan dube ta don Allah wata mummuna da ita.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button