BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Ta gefanta tace.” Kin San guy fa yana da tausayi da tausayawa talaka mybe kawai tausayi ta bashi ganin bata da sutturar arziki yasa ya kawo ta ta zab’a amma nasan yanda yake da kyau uwa uba dukiya babu abunda zai ci da wannan abar dube ta fa ki gani kamar kwancan hauka.”
[10/28, 5:44 PM] .: Wani k’ululun bak’in ciki ne yazo ya tokare min a mak’ogwaro na,wai me ‘yan mata suka d’auki mutumin nan ? Ya ilahi sai kace shi kad’ai ne namiji a duniyar nan da har suke wannan maganganun, raina a dugunzume na isa inda suke, wacce tayi maganar na nuna da hannuna cikin kaushin murya nace.” Ke ki kishaga taitayin ki, duk naji irin surutun da kuke a kaina to bari kuji wallahi nafi Ku iskanci idan tak’amar Ku a kano kuke to nima haka kuma ni ‘yar bakin kasuwa ce karewar tashan ci dai-dai nake daku, duk muni na ban kai ki ba ke maganar banza kawai dube ki fuskar ki a k’one da bleccing. ” ina huci!! Na karasa maganar. Cike da mamaki suke kallona wacce nayi wa rashin mutumci tayo kaina a fusace! Kamar zata Doke ni!! Dayar tayi saurin rik’e hannunta tana hana ta, kallon banza nayi musu nace.” Tsautsayi yasa ki hannun ki ya taba jikina wallahi sai na karya shi.” Dariya suka saka had’e da zare ido naji d’ayar na cewa “Kema Safiyya me zai sa ka ki tsaya fada da wannan kucakar salon ta gogo miki karzuwa talauci ne kawai yake damunta shiyasa ta zauce!!!! Suka kwashe da dariya. A zafafe! Na futar da hannuna na tsinka ma me maganar mari, ina kallon d’ayar nace” kice takk!! Kema ki samu rabon ki.” Shiru sukayi cike da mamaki suke kallona,, su Rbow suka k’araso gurin da sauri suna tambayar ba’asi banza nayi musu na matsa gefe gami da duba kaya kamar gaske har yanzu ban dauki komai ba.

Ina jinsu suna fada musu abunda ya faru wacce na Mara din tana share hawaye tare da cin alwashi a kaina ko kallo bata ishe ni ba, rambow ne ya tasa su a gaba har gurin biyan kudi suka biya sai da ya tabbatar sun shiga motar su sannan ya dawo gare ni yana min hayaniya, zare masa ido nayi cike da jin haushi nace “ni nace ina bukatar kayan gurin nan da za’a kawo ni har wasu banzaye su zage ni kuma in kyalesu bazai yi wu ba, kar ka dame ni.”

Cike da mamaki rambow yake bin yarinyar da kallo chaaaa!!! Gaskiya tana da tsiwa!! Babu Wanda zai yi maganin ta sai Amjadu gurin ya bari kawai cike da jin haushin ta

Gaba nayi ina duba kaya burina kurum in hango material irin na ankon mu in d’auka tuna ya karb’e min kudina, da k’yar na hangu irin shi nacewa yaron gurin ya d’auko da sauri ya d’auko yana warware wa nace.” Yanka Mana yado goma, sha biyar,har Munnu sai ta samu. Aikuwa da sauri ya fara yankawa ya nade sosai had’e da dauko wata k’atuwar Leda ya zura ya d’auko landing din shi ya yanka shima ya sanya a Leda da ban, karb’a nayi na bar gurin na nufi gurin takalma wasu plate na hango set uku had’e da jakkunan su golden ne sai shaki suke da alama fatar da akayi su mai tsada CE, nace wa yaron dake gurin ya Ciro duk ukun aikuwa ya Ciro da sauri ya dauko wata doguwar lede me tambari sunan Mai gurin wato Mudansir and brothers ya zura su dama jakar bata da girma sosai nan ya mik’o min nace” ka biyo ni dasu a baya don bazan iya d’auka ba.” Aikuwa jiki na kyarma ya mike da sauri ni kuma na nufi gurin sark’oki wasu lafiyyayun Fashion na d’aukar mana sunji stons sai k’yalli suke da walwali daga zasu ja kudi masu kyau!! Nasa yaron gurin ya ciro mana agogo uku na zallar fata multi coular, gaba nayi yaro ya biyo bayana hannunsa nike nike gurin mayafai na nufa, nan ma na duba kalar material dinmu wato purple nace ya dauko guda uku jiki na kyarma ya dauko masu mugun tsada… Daga haka kawai na kad’a kaina nayi han har futa, rambow da doh-doh suka taso daga inda suke suka biyo bayanmu ni da Dan dakona suka karb’i kayan a hannunsa,, INA futa tana kara daure fuska tamau!! Na isa gurin motar tare da tsayawa tunani nake ina yake Sam banyi tunani yana cikin motar ba tunda me bakin glass ce tintac Rambow ya bude bayan motar ya zuba kayan ya rufe da sauri ya bude murfin motar. Gabana ya fad’i ganin shi a ciki nace Ashe yana kallonmu da duk abunda muke shiga nayi ina d’auke kaina, sautin wak’ar Joy ne yake tashi a hankali me taken Because love me shiru nayi ina sauraran wak’ar ko wane baiti kalaman soyyaya ne, muryar Joy akwai sanyi da saka nutsuwa sai naji wani irin yanayi a jikina nayi kasak’e ina sauraron wakar……… Shiru bai ce komai ba yana kwance cikin motar idanunsa a lumshe! Na saci kallonsa kad’an.. Sai naga bakinshi yana motsi da alama wak’ar yake bi…

28/October/2019
[11/1, 10:55 PM] .: BABBAN YARO

Mallakar_BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD’IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.

33

 V

Sai da motar ta fara tafiya kan kwalata sannan ya bude lumsassun idonsa yana Dan gyara zaman shi. Agogon hannun shi naga ya kalla ya Dan girgiza kansa, kallona yayi nayi saurin d’auke kaina ganin yanda idonsa yayi ja, cikin kasalalliyar murya yace.” Kin samu abunda kike so.” Banza nayi dashi kamar ban San yana gurin ba.” A hankali yace.” Mata masu daraja ina magana fa.” Cike da takaici na kalle shi had’e da cewa”tunda ka karb’e min kudina ai dole in dauki abun kudina kuma dole ka biyasu.” Babu yabo babu fallasa yace. ” ni ko duka kayan gurin kika ce kina so sai in siya miki mutukar zaki min Abu daya.” Ya karashe maganr a hankali saboda su Rbow. A hangunce na kalle shi muka hada ido a karo na biyu, gani nayi idonsa ya kankamce ba kamar d’azu ba, nace” wane Abu ne.” Da idon shi ya nuna bakina.” Na kasa fahimtar sa, yace.” Kin gane ko”? Girgiza kai nayi cike da tsarguwa ganin yanda ya kurawa fuskata ido kome yake kallo oho!! Hannu ya kawo zai tab’a leb’ena nayi saurin gocewa ina watsa masa harara. Takure jikina nayi jikin kujera gabana na fad’uwa domin yanzu na fahimci abunda yake nufi.

Shima fuska! Yayi kamar bashi ba, ya dauko wayarsa yana latsawa ammafa fuskar nan tasa babu dad’i
Daf da zamu shiga layin mu nace “a sauke ni anan ya Isa.” Umarni ya bawa doh-doh yayo parking yana tsayawa na soma k’okarin bude motar da sauri ya rike min hannuna. Cike da bada umarni yace.” Doh-doh Ku bamu guri zamuyi magana.” Aikuwa suka futa daga motar da sauri. Ni kuwa ai tuni na fara rawar disco jin yanda yake murzamin hannuna, so nake ince ya sake ni na kasa fad’i

Fuskarta ya juyo da tafukan hannunsa ya kurawa bakina ido a hankali yace.” Ki zo muje gida ki dauki pant dinki kinji!!!! Na fuzge fuskarta da sauri ina addu’a kar Allah ya bashi nasara a kaina, yace.” Meye haka kike ni babu abunda zan miki kawai ina so in rage damuwar da take damuna ne.” Muryarta na rawa nace”kaji tsoran Allah Wanda ya hallice ka ka bude min kofa na futa.”. Sosa sumar shi yayi yana min munafukin kallo yace.” Zan bude miki yanzu amma ki bani in sha.” Na kasa fahimta me yake nufi. “Kinji!!!!!!* Yafadi maganar cikin wani irin voice tuni naji kuzari ya sare jikina ya soma sanyi,, nace ” ban fahimce ka ba.”? Bakina ya nuna da idonsa yana lumshe min su. Suma ne kawai banyi ba a gurin tsigar jikina ta mike sha’awar shi ta yunk’oro min sosai, nima sai naji ina sha’awar abun. Nasihar Umma na tuna hankalina ya tashi sosai nace.” Ni ba ‘yar iska bace au!! Yanzu nagane nufin ka shiyasa kace dole sai kayi min siyyaya wato badan Allah bane ko? To ko ka bude min mota ko in Tara maka jama’a a gurin nan, nan dai unguwar mu CE,wallahi yanzu zansan ya a fasa maka gilashin mota a raka da dutse.” Na k’arashe maganar cikin tsiwa tare da girgiza jiki cikin sigar rashin mutumci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button