BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL
B’ata fuska yayi had’e da gyara zaman sa sosai cikin motar yace.” Duk abunda kika fada zaki iya yi iya zama na dake na fuskanci halayyar ki, tab’e baki yayi yayi k’asa da muryarsa had’e da fadin ” nima da wasa nake miki me zan ji a wannan bakin naki me cike da tsiwa da rashin mutumci.” Nace.” Oho! Dai Dan dai baka samu bane.” A d’age yace.” Ko na samu bana so a kai kasuwa dama dan naga kamar kina so ne yasa na fadin haka, kanki kika cuta.” Yanda ya fad’i maganar yasa na fahimci nade tabar kunya yake da hauka, ganin yak’i yarda mu hada ido dashi nace.” Ni dai bude min kofa na futa.”! Handbag d’ina ya d’auka dake kan cinya ta ya bude lalube yake min cikin jakar babu ko kwabo sai cingum dina da wayata da kwanata biyu babu chaji saboda matsalar NEPA….. Wayar ya d’auka yana dubawa fuskarsa d’auke da murmushi ko name ye oho!! Yace.” Wannan matacciyar wayar meye amfanin ta a gurin ki.”? Kaina na sunkuyar kasa cike da kunya da taikaci wannam guy dan tonan asiri ne, ko ina ruwansa da wayata oho!!! Yace.” Magana nake mata masu daraja.” Ba tare da na kalle shi ba nace.” Wayata tana da amfani a gurina tunda ana kirana kuma nima ina kira da ita babu ruwanka da ita….. Kai tsaye yace.” Yar da ita zanyi kawai domin bata da amfani gashinan a kashe babu chaji!! K’okarin cillata waje yake ta window motar, cikin azama! Na rike hannunsa ina fadin kar ka jefar mun da waya domin tana yi min rana…” Muje in siya miki wata.” Yafad’a bayan ya jefar da wayar waje, cikin tsantsar takaici nace.” Kai duk fa inda kasa gaba na sani wallahi duk wayon ka wato kwadayin waya yasa na bika ka kaini gidan ka kayi iskanci dani to na gane.”!!! Kallonta yake cike da nazari wato ita tana zargin zai kaita gidansa da wata munufa Wanda shi kuma har ga Allah ba haka bane a zuciyarsa yayi niyyar siya mata wayar. Gyada kansa yayi yace.” Ko yanzu ina da damar da zanyi duk abunda nake so dake a cikin motar nan, na k’yaleni ne kawai saboda son raina lukatan baya na samu dama akanki sosai bai sa na keta miki mutumci ba, so ki cire wannan maganar daga ranki duk sanda kika kara zagina da haka ranar zan baki mamaki wallahi, har sai na Kai ki gidana zai yi iskanci da ke, gaki a gabana baki karfina ba, ke kanki nafi ki sanin wacece ke. Kike min wannan maganar bazan. “
Yanda ya kausasa harshe yake magana yasa na soma yin sanyi, zumb’ura bakina nayi had’e da cewa”Ni duk ba wannan nagaji da zaman motar nan ka salla me ni.” Ina kallonshi ya bude wani guri a cikin motar ya futo da d’aurin kudi guda uku ya tusa min a handbag jefo min yayi cinya ta tare da fadin ” kika kuskura kika watsar min da kudi cikin motar nan sai ranki ya b’aci! Yana gama maganar sa ya bude murfin motar… Futowa nayi ba tare da nace mishi komai ba, wayata na fara k’okarin hadawa batir yayi nasa guri haka ma layi ka na.
Sai da suka futo da kayan tsaf! Suka jibge min su gaba suka shiga motar da sauri suka bar gurin… Yara na fara kira da gudu suka nufo ni na basu umarnin d’aukar min kayan muka tsallaka titi tare dasu.
Aunty Hauwa da Mimi Umma na zaune a tsakar gida sun baza kaya suna dubawa suna hirata ko ina na tsaya oho!! Sai sukaji sallama ta, dukaninsu suka dinga bin yaran dake sauke kaya da kallo cike da mamaki na salami yaran.” Aunty Hauwa tace.” Wato Dan ubanki nitsa kikayi ciki kika barmu da wahala muna Neman ki.” Nace.” Aunty Hauwa wace irin nitsa kuma ni da kuka barni a waje,, nayi neman duniya ban gan Ku ba.”
Jawo kan ta farayi tana sambato! Cike da mamaki ta d’ago kai tana kallona had’e da fadin “Yana ga ledar Muddansi&Brots kuma.” Shiru nayi. Take ta fara zazzage kayan suna dubawa cike da mamaki.
Umma tace.” Asma’u duk a gurin kika samu wannan kayan, naga duk sabbi ne babu inda ya b’aci.” Nace” A’a Umma me gurin ne ya siya mun su
Da sauri autn Haa tace.” Kamar yaya me gurin? Kuna nufin Amjadu? D’aga kaina nayi cike da tsarguwa Mimi tayi saurin kallona jin abunda nace. Aunt Tace.” Baki da hankali a ina zaki ganshi har ya siya miki wannan kayan.”. Nace.” Wallahi shine ya siya min, ya ganni a waje cikin rana mutane na turmutsutsu shine yace.” Na shiga mota muje a siya min yaga ina bukatar suttura,shine fa mukaje muddanssr&brothers na sharada yace in zab’i duk abunda nake so, ni ko na duba mana anko mu.” Kallona suke tunda na fara maganar sun kasa cewa komai. Nace ” kunga ma kud’in da ya bani.” Zazzage jakar nayi kud’in suka fado kasa, da sauri aunt ta d’auka tana zare ido, lissafawa ta fara yi duk dauri d’aya dubu Hamsin ne, dubu dari kenan. Umma tace.” Zan ci ubanki Asma’u ki fada min gaskiya ko budurcin ki kika siyar gama naga take-taken ki kwana biyunan ,ni Sam ban yarda da cewa wannan yaron ne ya baki kudi nan ba, na fi tunanin yawon ki ki ka tafi.” Kuka na fashe dashi sosai INA rantse wa da girman Allah, aunt Hauwa tace.” Gaskiya nima nayi mamaki Asma’u ta yaya har zaku had’u da mutum irin wannan yayi miki siyayya akwai dai abunda kika b’oye.” Kallonta nayi ina goge hawaye nace.” Aunt kema abunda zaki ce kenan.”? Tace” eh mana nasan halin ki fa da shegiyar k’aryar tsiya dama da akwai inda kikayi niyyar zuwa shine yasa kika ki binmu ciki ko.” Ina kuka nace” Allah ne shaidata wallahi ni babu wani Dan iskan namiji da na bawa kaina.”
Umma ta kalli aunt ranta a bace tace” kira min Aminu a waya yazo ya fi ubanta ko ta fad’i gaskiya. ” aunt ta dauko wayarta da sauri ta fara kiran numbar Aminu, da gudu na tashi na shige dakinmu ina kukan takaici.
Minti goma tsakani sai ga Yaya Aminu ya shigo nan suka Zayyane masa komai, a fusace! Ya shigo dakinmu yana fadin”futo ko na ci ubanki.” Sanin muguwar zuciyarsa yasa na mike zaune harara ya watsa min yace.” Muje tsakar gida ki fada min uban da ya baki dubu Dari.” Ina kuka na futo duk suka zuba min ido, bulala katuwa ya dauko a daki ya tsaya a kaina yana huci, gami da fadin”Dan ubanki gidan uwarwa kike je.” Shiru nayi ina kuka ya daga bulalar ya zabga min a jikina, ihu na kurma Mimi tayo kaina had’e da rungume ni tana kuka had’e da rokon Ya Aminu.Bulalar ya daga had’e da zabga mana dani da Mimi din muka rungume juna muna kuka yace.” Ni ubanku zan ci munafukai kawai bakinku daya Ashe ? Wato talaucin namu har ya kai kuje gurin samari Ku rokesu kudi ko? Ina ce jiya nace zan baku kud’in Atamapar ko zaki fada min ko sai na karya ki.”!!!! Ya k’arashe maganar had’e da sake shimfid’a mana bulalar a fatar jikinmu…….Cikin kuka nace.” Ya Isa!! Haka nace ya isa haka ka daina dukanmu alhalin bamu aikata abunda ake zargimu dashi, idan ni baku yarda dani ba to ita Mimi meye laifin ta, da zaka dinga dukanta.”!!!!! Hannu ya kawo ya buge min bakina yace.” Zagina zakiyi ne Dan ubanki. ” da k’arfi nace.” Ni ba zagin ka zanyi ba gaskiya ce na fada maka, idan baku yarda ba, Ku tashi muje gidansa tunda dai ba b’oyayye bane sai Ku tambayshiiiii.”. Yace” ai ko baki fada sai munje dama ai an ce mane min mata ne, koma dai meye zai fada mana, talauci si ba hauka bane”!! Ya karasa maganar had’e da jefar da bulalar yana kuka. Ni da Mimi muka rungume juna muna kuka.
Umma tace” Maza tattare kayan da ta shigo dasu ki mai dasu ledar su had’e da kud’in bayan sallahr magariba sai kuje har inda yake muji, nifa nafi zarginta ita Asma’un karya kawai take masa domin zuciya tana bani yaron bazai aikata wani aikin assha ba.” Cikin zuciyata nace” Umma domin ba ki San waye Amjadu bane yanzu da yaya na kwaci kaina daga hannunsa.