BABBAN YARO COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL

Hon! Mukaji da k’arfi dukaninmu muka juya da sauri! Gabana ya fad’i ganin motarsa, Aunt tace.” Allah yasa shine.” A hankali nace “shine ma” duk suka kalle ni cike da mamaki.

Gefe muka matsa me gadi ya bude get din motar ta silala ta shiga ciki, karninkan da suke kwance a gurin suka mike da gudu suka nufi motar, dake akwai haske ko ina a gurin muna kallon abunda yake faruwa daga waje. Ya Aminu ya kaskantar da murya yana rarrashin me gadi kan yaje ya sanar da shi tunda ya dawo.

Yace.’ Da kunyi hakuri gobe Ku dawo domin nasan a gajiye ya dawo ko baku San abunda ya faru dashi bane.”? Ya Aminu yace.” Mun sani shiyasa ma muka zo muyi masa jaje.” Me gadi ya kalli Aminu cike da mamaki minti biyu yace.” Bari in fada masa.” Ya Aminu yayi masa godiya ya wuce ya barmu tsaye bakin get muna hangosa ya isa gurin shi yana daf da shiga part din shi. Tsayuwa naga yayi yana kallomu, minti biyu ya nufo inda mike wannan dog din nasa da nagani farkon fara gani na dashi ya biyo bayansa, tare dasu rambow. Tun kafin ya k’araso na sunkuyar da kaina kasa.

Shi ko Amjadu tun kafin ya isa gurinsu ya gane ta, ko cikin mata dubu yarinyar zata shiga yana iya gane ta, ballanta guri da haske futulo dal-dal tamkar rana, mamaki yake me ya kawo ta gidan shi, kuma? Ya karasa fuskarsa babu yabo babu fallasa. Da sauri Ya Aminu ya mik’a masa hannu alamun su gaisa, ba tare da girman kai ba ya mik’a masa NASA sukayi musabaha, kamar bai sanmu ba nida Mimi haka ya nuna ya kalli aunt da Aminu a nutse yace.” Ina fatan lafiya ko.” Ya Aminu ya diririrce domin guy yayi masa mugun kwarjini ashe jinsa kawai yake a baki wannan shine jinka yafi ganin ka, duk taurin kai gami da dakiya irin na Aminu sai da ya risina. Ya sunkuyar da kai tare da fadin” Yallab’ai magana ce take tafe damu ina fatan babu damuwa.” Ni ya kalla ina kallonsa a fakaice ya d’auke idonsa daga kaina yace.” Babu matsala amma ku shigo ciki ko.” Aminu yace.” Godiya muke.” Wuce wa yayi ciki muka bi bayansa tuni dog d’insa ya fara wani irin ihu! Yana tsalle zai cafke ni! Da gudu na matsa ina zare ido!! Wan!wan!wan!wan! Dog din kawai yake yayo kaina tare da kama bakin hijabina da yake Jan k’asa!! Ihu!! Na kurma ina k’ank’ame jikina guri guda.” Cikin tsawa naji yace.” Tegar”!! Stop.”! Daina haushin yayi ya tsaya yana kallona. A hankali ya ja siririn tsaki ya kalli Ya Aminu tare da fad’in “wannan black din abun da ya gani a jikinta ne yasa yake tunanin ko Anjalina ce.” Wato matar shi, cikin dizgi! Ya Aminu yace.” Dama ya cije ta ai da mun huta da halin taurin kai. Ita b’aka ta kama ta sanya b’akin abu ba dole karnuka su biki ba.” Babu abunda yace yayi gaba muka bishi a baya gabana sai bugawa yake yi na tsinewa dog din nan yafi sauri dari, shima Ya Aminu yanzu wani mugun haushin sa nake ji

Rambow ya bude masa kofa ya shiga muma muka shiga, ina kallon aunt Hauwa sai kalle-kalle take a parlor ni da Mimi dama gidan ba bakonmu bane, shi kanshi Ya Aminu zare ido kawai yake yi sai kallon parlor yake yi
Bedroom dinsa naga ya nufa, na kauda kaina zuciyata na tuna min abunda ya faru dani da shi kwana biyu da suka wuce.

Muna zaune kimanin mintuna ashirin babu Wanda yacewa da Dan uwansa uffan! Dukaninnu jiran futawar sa muke. K’amshin tura ransa ne ya tabbatar mana da ya iso, tunda na daga kaina sau daya ban sake kallonsa ba, saboda nasan na tsananta to Zan iya tonawa kaina asiri.. Yana sanye da wasu had’addun kayan shan iska black and White rigar sharara k’irjinsa a bude shi kuma wandon iya kacin sa gwiwa da alama Wanka yayi ganin yanda fuskarsa take shek’i gashin girar shi da danshin ruwa, zama yayi kan kujerar dake fuskanta ta, ya kalli Aminu a nutse yace. ” na barku ko kuyi hakuri nayi Wanka ne.” Ya Aminu yace.” Babu komai yallaby.” Yace.” Ok ina jinka.” Cikin daburcewa Ya Aminu ya fara magana kamar haka.

“Yallab’ai waccan yarinyar dake zaune kujerarar dake kallon ka, k’anwar mu, ce d’azu misalin k’arfe hudu bayan an idar da sallahr la’asar kenan ta shigo mana gida da kudi da kaya wai Kaine ka bata, shine hankalin mahaifiyar mu ya tashi tace bata yarda da ita ba, Dole tace azo a tambaye ka.”

Sunkuyar da kaina nayi zuciyata kamar tayi bundiga wai ni ake wa wannan tozarcin humm! Lallai ya Aminu.

Ta kasan idona nake kallonshi yana Dan satar kallona, ya kalli Aminu tare da fadin” Abunda nake so na fahimta anan shine dama can yarinyar tana bin maza ne ? Ko ko kuna zargina da ita ne.”? Yadda ya fad’i maganar zaka san ranshi a bace yake. Ya Aminu yayi saurin cewa”Ko daya Yallab’ai ita yarinyar muke zargi ba kai ba.”. Shiru parlor yayi mintuna biyar sannan yace.” Duk abunda tazo ta fada muku a gida hakane nine na siya mata kaya kuma nine na bata KUDI don ra’ayina ba don wani abu ba, saboda haka Ku daina tuhumar ta, a kan aikata alfasha, naji dad’i da samun ku iyayen jajurtattu gaskiya na yaba k’okarin Ku.” Ya Aminu yayi murmushi had’e da godiya, aunty Hauwa ma sai washe baki take..Mik’ewa yayi yace.” Ni zan shiga ciki Ku sauka lafiya kai idan kun futa doh-doh na tsaye a waje kace injini ya kai Ku har gida.” Ya Aminu yace” godiya mukeyi” hannu kurum ya daga masa ya shige bedroom dinsa.

Jiki a sanyaye na mik’e tsaye sosai nake mamakin halin ko in kula da guy nan yake nuna mini in ya ganni cikin mutane sai ya nuna sam bai sanni ba, yanzu ma dubi yanda yake wani shan kamshi ba, tab’e bakina nayi na futa daga parlor cike da taikacin wulakamcin da yayi mana, gaba nayi kawai ina jin ya Aminu ya tsaya yana fadawa doh-doh sak’on da oganshi yace..

Aunt hauwa ta kwala mib kira nayi nisa ma ina daf da fita tace.” Kizo mu shiga mota mana ko baki ji abunda aka ce ba.” Ba tare da nace komai ba na dawo da baya, sai da suka gama shiga tsaf! Sannan na shiga doh-doh ya ja motar muka futa daga gidan.


Tsaf Ya Aminu ya zayyanawa Umma komai tayi hamdala gami da godewa Allah, ta kalle ni tare da fadin”Allah ya cece ki wallahi.” Ni dai shiru kawai nayi ina mamakin halin Ya Aminu, aunty hauwa tace.” Mara mutunci gurin siyar kayan ko ki tuna dani ko Isilam baki tuna ba balle ki siya mata ko pant ne.” Shan kunu nayi domi itama aunt hausshin ta nake ji.Mik’ewa nayi ba Tare da nace mata komai ba. Hararata tayi tace.” Sai kije kiyi tayi ai gaskiya ce dole a fada miki..

Dakinmu na shiga na kwanta kan katifa gami da rintse idona suffar sa kawai nake tunawa lokacin da ya futo daga bed d’insa, a d’azu tsigar jina ta tashi da idona ya hasko min k’irjinsa na cije leb’ena gabana na fad’uwa da na tuno abunda yace da Ya Aminu wai yayi min siyayya ne ba don wani dalili ba kawai ra’ayin sa ne. Wannan kalma da ya fada sam ba tayi min dad’i ba.. Mimi ta shigo dakin tana buge gurin kwanciya tare da fadin “bakiyi sallah ba kinzo kin kwanta.” Mik’ewa zaune nayi nace.” Mimi Wanka ma nake so nayi hummm! Ai ni yau ‘yan gidan nan sun bani mamaki .” Mimi tace.” Wane mamaki kuma”? Cike da takaici nace” baki ga irin zargin da suke min ba Mimi.”?

Murmushi tayi kawai ta cigaba da gyara shimfid’a na mike zuciyata babu dad’i na futa, ina kallon aunt Hauwa zata tafi suna sallama da Umma Ya Aminu na tsaye yana jiranta DOMIN ya raka ta hanya saboda dare ya fara yi, ko kallonsu banyi ba na dauki bokiti na cika da ruwa na shiga band’aki abuna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49Next page

Leave a Reply

Back to top button