BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL
Tsayuwa mukayi bakin titi rayukanmu babu dad’i mussaman ni tunani kawai nake hanyar da zanbi in rama rashin mutumcin da wannan ‘yar iskar tasa akai min a bakin titi don ma mutane nasu ankara ba, da kunyar da zanji sai Allah.
Tunda ta futo daga gurin yake kallon har suka zo suka tsaya bakin titi bai d’auke idonsa daga kanta ranshi in yayi dubu ya b’aci! Ya kalli ‘yan iskan samari yana nazarin su. Meye alakatar dasu ? Da har take biye musu suna shirme a titi ko dai maganar da ‘yan uwanta suka fada a kanta gaskiya ne, in ko hakane tabbas zata fuskanci hukunci a gurin shi, take yaji k’irjinsa tayi masa wani mugun nauyi zuciyarsa na kara fada masa haka ne dama can tana biyewa ‘yan iskan samari su lalube ta, shiyasa ta saba kuma take da sha’awa sosai! Idanunsa sukayi jazuri lips d’insa na kasa ya ciza had’e da dukan kujerar mota da k’arfi! Doh-doh ya juyo da sauri yana kallon ogan nasa alumu sun nuna ogansu ya fad’a tafkin so, a hankali yace.” Sorry sir.”
Da k’yar Rambow ya lallab’ata, ta yarda zata shiga motar, ganin yana k’okarin bude motar ne yasa ya gyara zaman sa had’e da murtuke fuska tamau!!! Da kansa ya bude motar rambow ya k’araso gurin da sauri.. Minti biyu tsakani ya nufi inda matasan samarin suke tsaye ya kirasu jiki a sanyaye suka bi bayansu domin sun fara tsarguwa ido hudu sukayi dashi a take suka zube a gurin. A hankali ya d”ago kanshi yana kallonsu yace.” Me ya had’aku da waccan budurwar.” Da sauri d’aya ya fara yi masa bayani.” Murmushin takaici yayi yace.” Ban yarda ba ko dai buduwarku ce? Ko kuma wani ne saurayin NATA ne ya sanya ku kuyi masa aiki a kanta.” Girgiza kai sukayi suna rantsuwa yace.” Ya sunan wacce ta sanya Ku wannan aiki ? Suka ce “Safiyya sunan ta.” Gyda kansa yayi cike da takaici yace.” Saboda rashin aikin yi kuka zo bakin titi zaku walakanta hallitar Allah ko? Aiko zina zakuyi sai Ku je Ku b’uya a wani gurin kuyi tozarta mutum bashi da dad’i fa.” Duk jikinsu yayi sanyi suka fara bashi hakuri, yace.” Kuje Ku bata hakuri Ku dawo kuji wani Abu.” Aikuwa da sauri naga sun nufo inda muke tsaye.
Mimi tace.” Gwarafa mu San abunyi Asma’u. ” nace ” kyalesu suzo gurinan wallahi sai na ci musu mutumci.” Fuskokinsu da alhini suka tsaya gabana d’ayan yace. ” Kiyi hak……kafin ya karasa na zabga masa mari!! Shima d’ayan ya bude baki kenan zai magana na bashi kyakyawan mari guda nace” dukaninku hakurun me zaku bani.”? Sunkuyar da Kansu sukayi kamar wata zarrariya nace “Ku bani guri don Allah ‘yan iskan banza da wofi.” Simi-simi suka matsa daga gurin.
Duk yana kallon abunda yake faruwa, miskilin murmushi yayi zuciyarsa babu sauk’i ko kad’an yace.” Zaki shigo hannuna ne yarinya.” Kafin suyi magana yace.” Naga komai Ku rabu da ita.” Suka CE.” Insha Allahu.” Shiru yayi na minti biyu kana yace.” Rana ita yau insha Allah sabon company na zai fara aiki saboda haka ina buk’atar ku a gurin za’a baku ‘aikin yi Ku daina wannan shashanci. ” sai da suka kusa fad’uwa saboda godiya kana kallonsu zaka fahimci suna cikin farin ciki godiya kawai suke yi, kudi ya Ciro ya basu tare da sallamar su, suka bar gurin cike da murna da farin ciki.
Zuwa yanzu na tabbatar da yana cikin motar, nace dasu Munnu mu matsa gefe guda ma fara Neman abun hawa domin baza mu shiga motar ba. Aikuwa nesa da motar muka yi. Rambo ya biyo mu a baya kamar wani jela, sai rarrashina yake ni kuma ina botsarewa, a hankali Mimi ta rad’a min a kunne “Asma’u don Allah mu shiga wallahi mugun son ganinsa nake kwana biyu ni nasan halin da nake ciki a kansa duk abunda nake kokari nake.” Kallonta nayi cike da mamaki !! Sai naga idonta ya tara k’walla tausayi ta bani mutuka Mimi tana sona tana damuwa da damuwa ta idan na shiga wani hali tana damuwa sosai,sai inda karfinta ya kare, ta bani tausayi sosai nace “Ku muje to” aikuwa suka biyo bayana. Rambow yaje ya bude mana kofar motar da sauri. Ni na fars shiga, k’amshin mugun turaransa yayi mun sallama, d’auke kaina nayi ban kalli shashen da yake ba, saboda shi kanshi haushisa nake ji sai ya dunga nunawa mutane kamar bai tab’a ganin mu ba wannan ai munafurci ne.
Kusa dashi da nazauna Mimi ta zauna sa Munnu rbow ya bude ya shiga ya zauna kusa da d’an uwansa muka tafi.
Munnu da Mimi duk sunyi sanyi sau sunkuyar da Kansu k’asa suke a hankali naji Munnu tace.” Ina wuni.” Shiru bai amsa ba, da wutsiyar idona na kalli gefan sa, sai naga idanunsa a lumshe tab’e baki nayi.Munnu rashin zuciya ta kara maimatawa “Ina Wuni” wannan karon da d’an k’arfi tayi maganar, idanunsa ya bud’e a hankali ya kalleta tare da fadin” lafiya ‘yan mata ya kike.”? Munnu tace.” Lafiya lau.” Murya a sanyaye Mimi ta gaishe shi ya amsa a sake tare da fadin sunan ta rad’au!! “Mimi me ya kawo gurin nan har kuke rigima da wad’ancan ‘yan iskan kan.” Mimi inda -inda ta fara DOMIN ta rasa abunda zata ce masa, shiru motar tayi ni kuwa sai kauda kaina nake bana so ma na kalle shi ballanta na shiga wan mi yanayi.
Cikin hikima ya zura hannunshi guda ta bayan mayafina naji ya shafo mazaunai na, da sauri!! Na gyara zamana gami da kallon gefan sa hankalina a tashe. Ido ya tsura min! Wanda sukayi ja kad’an. Da sauri na d’auke kaina gabana na fad’uwa.
Har yanzu hannunshi guda na cikin mayafina yana shafa min jiki, in banda ni dashi babu Wanda zai gane hakan. Motsi na fara yi INA duk a k’okarin na buge hannunsa, hakan sai ya bashi damar d’age rigata ta baya ya zura hannunsa a ciki yana shafa cikinsa zuwa ramin cibiya ta… Ji nayi kamar in kurma ihu!!! Na kalle shi da Jan ido! Kauda kansa yayi da sauri ya cire hannunsa had’e da sakin wani shegen murmushi yana cije lips d’insa kamar yanda ya saba.
Jikina yayi wani irin sanyi ina mamakin tacewar wannan guy ta fannin iskanci sai yayi Abu kamar bashi ba, dai-dai ta kaina nayi had’e da d’auke kaina hannu na sai rawa yake.
Hannunta ya tsurwa ido yana kallon kunshin da ya futo yayi rad’au domin har ya soma yin duhu ma saboda lallan yaji had’i zanan fulawar ya futo dara-dara sosai lallan ya burge shi, ya lura yarinyar tana da kyawun fata mussaman a jikinta fuskarta ce me duhu had’e da wasu k’ananun kuraje Wanda yasan ki na meye, mafi aka sari duk budurwar da take fa wannan kurajen fuska kuma tayi magani sunki’ mutuwa to ta bunkici kanta tana da tsantsar sha’awa ne, to itama Asma’u tana dasu a gefe da gefen fuskarta amma basu da yawa.
Munnu aka fara saukewa mukayi sallama da juna ta tafi. Shiru motar sai saukar nuffashi mu ganin munnu ta sauka ne yasa nace da Mimi ta matsa na gyara zamana sosai na rabu da jikinsa, a hankali ya Dan kalle mu ni da Mimi yace.” Mimi na tambaye ki baki bani amsa ba.” Mimi da soyayyar sa ta kusa kassarata ta d’ago kanta cike da kunya tace” munje ayi mana lalle ne sai muka shiga gurin domin ayi mana gyaran fuska shine fa kawai muka gansu sun shigo ciki.”
Murmushi yayi a hankali yace.” Kuma ba samarin ta bane”? Mimi tace” ko d’aya wallahi a sali ma mu bamu tab’a ganinsu ba kawai tsabar iskanci ne.” Dariya yayi gami da d’an Sosa sumar sa as’usuel yace.” Anya kuwa Mimi kin manta halin ‘yar Uwar ki ko.”? Murmushi tayi cike da kunya.
Duk ina jinsu dauke kaina kawai nake Sam! Bana so na kalle shi Allah ya Isa kawai nake masa cikin zuciyata jin damshi a jikin wando na nasan ko menene,tunda ya tab’a min jiki shikkenan nake zubah.