GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

A parlourn ya tarar da hakimar tasa zaune da rigar bacci a jikinta yaran suka taso da gudu suka rungumeshi suna fadin “Good morning sweet heart” murmushi yayi ya dagosu dukkansu yace “morning my kids kunyi sallah kuwa?” Maliha ce tace “da asuba mukayi Aunty ta sabar mana da tashin asuba” murmushin sa ya fadada yace “Allah Sarki Aunty Allah yayi Mata albarka daku da ita” suka amsa da “amin” Sadiya takai qololuwar qufula da watsin baqar sharar da yayi da ita ta lura duk abinda takeyi donya kulata kamar ma baya gani saboda haka ta zabura ta miqe tace “nida ba yar albarka ba a tsinemin mana aikin banza da wofi dadin abin ba uwar wanice ta haifamin yayan ba nina haifi abuna kuma wlh dakai da danginka duka sai kun gane kunci amanata idan ma ba tsoroba don Allah ka dawo da ita gdan nan mana banza ragon namiji kawai ashe ma iskancinka na qarya ne”
Sosai kalaman nata sun sosai zuciyarsa amma saiya dake saboda bayason biye Mata su zama mahaukata a gaban yaran hanyar kitchen ya nufa kawai yaji yaran sun zunduma wani ihu ya juyo da sauri yaga abin mamaki Sadiya ce dare dare akan Maliha tana jibgarta kamar jaka wani kukan kura yayi ya dira gaban Sadiya ya dauketa da wani irin mari daya sata kifiwa a qasa ta saki qara kafin ta ankara ya zare belt din jikin wandonsa ya fara jibgarta da gurin qarfen kamar Allah ya aikosa saida yayi mata tilis yaji ko ihun ta daina sannan ya qyaleta yana huci yaja hanun yaran da suketa kuka suma ya fice dasu a mota ya zubasu ya just cikin gdan ya dauko ATM card dinsa yaja motar a fusace ya fice daga gdan.
Kai tsaye gdansu ya nufa cikin saa daga Hajiya har Daddy da Umaiman suna parlour yaranne suka fara shiga Umaimah tayi wani tsalle ta rungumesu tana dariya tace “wayyohh yarana nayi missing dinku for long time” kuka sukeyi sosai suna qara shigewa jikinta binsu tarinqayi tana cajesu jikinsu duk yayi taruwar jini ta rungumesu ta fashe da kuka tace “waye
yayi muku dukannan Nihail wanne azzalumin ne ya dakarmin ku Allah ya isa tsakanina dashi koma wane” daidai lkcn ya shigo parlourn janye da trolly din kayan yaran idonsa qyar akan Umaimah da taketa rafzar kuka yaran suna tayata tanata zuba Allah ya isa suna amsawa da amin, ajiyar zuciya ya sauke me qarfi ya zauna kusa da Umaiman ya dago kanta shima idonsa taf da hawaye yace.
“Kinasonsu Babyn Uncle?” daga masa kai tayi da sauri ya sauke ajiyar zuciya idonsa cikin nata yace “nabar mikisu halak malak Babyn Uncle nasan bazasu taba kuka ba indai kina raye kuma bazanyi nadama ba nayi kyauta a inda ake buqatarta” miqewa yayi zai fita Hajiya ta qwalla masa kira ya tsaya cak tace “kadawo ka debi yayanka ka mayar dasu gurin uwarsu bazaka tafi ka dora mata wahala ba wacce ma tayi a baya ta isa Allah yabada lada” juyowa yayi idanunsa cikin na Umaimah data qarawa kukanta sauti tana qanqame da yaran yace “kiyi hqr Hajiya wlh Sadiya batada hankali zata iya kashesu akansu take hucce duk wani abu dake damun zuciyarta ta dakesu ta zagesu ta hanasu abinci yunwa harta fara kamasu don Allah kada kice aa Hajiya kiyimin wannan alfarmar plz” ya fada idanunsa na zubar da hawaye ba Umaimah ba ita kanta Hajiyan ta kadu da ganin hawayen nasa amma saita dake tace.
“Idanma kashesu zatayi ka kaisu ta kashesu aiba wani ya haifa matasu ba kuma uban waye yace uban nasu yayi abinda zaa hucce akan yayansa saboda haka Umaimah ba baiwar uwarka bace bata ubanka ba kabarta ma da ciwon abinda kayi mata maza ka bacemin da gani anan kaida tsummokaran yayanka kafin naci mutuncinka” cije lebansa yayi jikinsa na bari ya tako parlourn a matuqar fusace ya kai hanunsa zai rabata da yaran ta qanqamesu ta yanda babu me iya rabata dasu ran Hajiya ne ya qara baci ta daka mata tsawa tace “ki sakar masa yayansa yasan yanda zaiyi dasu ko kuma ki tashi ki bishi tunda ke bakisan ciwon kanki ba” cikin kuka ta miqe da Maliha a hanunta ta riqe hanun Nihal tace “na yarda da duk abinda da kika zaba mana Hajiya amma bazan taba yarda a rabani da yayana ba yayan da naci wahalarsu tun bansan kaina ba yayan da nakejin qaunarsu tana yawo a cikin jinina wlh Hajiya na amince zasubar miki gdanki kuma na aminci zan bishi mu tafi tare nasan bazanyi nadama ba haba Hajiya ku tausaya masa mana ya zaiyi da rainon yara da wanne zaiji”…….
UMMUH HAIRAN CE…✍????
????RILLIANT WRITERS ASSOCIATION ????
( Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers)
GIDAN UNCLE
( Love and romantic story)
SHORT AND TRUE LIFE STORY
MALLAKAR
????????
FAUZIYYA TASI’U UMAR
®FAUZAH
Wattpad???????? realfauzah
www.fauzahtasiu41@gmail.com
PAGE THIRTEEN
Daddy ne ya dago ya sanya hanu ya yafito Umaimah da take shirin juyawa tabi Hameed din ta koma riqe da yaran ta zauna kusa dashi tana kuka me ban tausayi dafa kanta yayi yace “kiyi zamanki anan da yaranki itama Hajiyan bacin raine yasa tace kibishi sukam ai basune sukayi miki laifi ba” ajiyar zuciya tayi tace “na gode Daddy” ta miqe ta shige dakinta ta zaunar dasu ta sake fitowa ta dauki kayansu ta koma wanka tayi musu ta shiryasu tare da nufar kitchen ta hado musu tea sukasha sannan suka kwanta dukkansu suka fara bacci har ita sai rana sosai ta tashi lkcn Hajiya tana kitchen tana girkin rana ta shiga ta kama mata sukayi suka gama so da qaunar yarinyar takeji yana qara ratsa zuciyarta har cikin ranta batajin dadin abinda takeyiwa tilon dan nata namiji amma babu yanda zatayi itama Umaimah tanada haqqi a qwata mata yancinta a gurinsa yasan cewa ba kadara ce me sauqin samu ba abinda yake bata haushi da ita tanayin hakan dominta amma taqi bata hadin kai ta lura nan gaba kadan ma a gabansu zata iya rungumeshi saboda bataga alamun ruwa a idon Umaimah ba.
Saida suka gama girkin suka jera a dinning sannan ta shiga ciki ta taso yaran tayi musu brush suka zauna cin abinci Hajiyan ma ta saki jiki sosai dasu kamar ba itace me cewa a fice dasu daga gdanba bayan sunci abincin sunyi sallah suka dauko qur’ani ta fara yi musu qari suna biyawa sosai suke burge Hajiya tanajin dama Umaimah itace uwar jikokin nata, ranar yini sukayi suna shirmensu sai dare sukaje suka kwanta gadon tabarwa yaran ita ta sauke qaramar katifa a qasa ta rufesu tare dayi musu addu’a tana kwanciya bacci ya dauketa saboda sosai shirmen yaran ya gajiyar da ita.
Jitayi numfashinta baya fita sosai ta fara shure² tare da qifqifta ido saboda hasken data gani a idonta bude idonta tayi idanunta suka fada cikinna Hameed daya hade bakinta da nasa yana tsotsa tureshi ta farayi tana qoqarin tashi ya riqe hanunta duka biyun yaci gaba da tsotsar Sweet lips dinta tana fitar da numfashi daqyar ya jima yana tsotse Mata bakin kafin ya saki ya sanya harshensa saman dokin wuyanta yana lasa tare da hura t iska me kashe jiki lumshe idonta tayi tare da sauke ajiyar zuciya cikin wata rikitacciyar murya ta Kira sunansa dakatawa yayi da abinda yake ya kalleta jin yanda ta Kira sunan nasa kai tsaye lumshe idonta tayi tace “banason haka don Allah kana ganin halin da muke ciki dagani har kai Kai wai mesaya bakaji ne kacika taurin kai kanaso yauma Hajiya tazo ta ritsamu a haka kasa na shiga uku ni kadai don kai naga ba gudun abin kunya kakeyi ba”ajiyar zuciya yayi ya kamo weast dinta sosai yana qara dora bakinsa a wuyanta ya sauke mata wani kiss me kashe jiki cikin sexy sound dinsa yace.