GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ajiyar zuciya tayi ta kawar dakai mararta nayi mata ciwo har yanzu cije lebanta tayi tace “wayyoh marata ciwo Aunty” dafe mata cikin tayi da sauri tace “sannu Umaimah kinsan qaramin ciki sai a hankali bareke da kika hadu da irin wannan mijin” saida cikin nata ya lafa da ciwo sannan ta kalli Aunty Jameelan tana hawaye tace.

“Ciki fa kikace Aunty na shiga ukuna nikam da wanne zanji wai yaushe ma na tare ko sati biyi banyi ba acemin wani ciki” jitayi an ruqo hanunta ta dago ta kalleshi sai taji wani mugun tsoronsa yana ratsa zuciyarta tayi qoqarin janye hanunta amma yaqi sakar mata yayi mata murmushi yace “sorry Babyn Uncle bada niyyah nayi miki hakan ba kece kikaja da kikayimin gardama” itadai bata iya cemasa komai ba saboda tsoronsa takeji sosai sunkuyawa yayi ya bude rigarta yayi kissing cibiyarta ya dago yace “dama nace mun samu qaruwa kincemin aa to yanzun yar manuniya ta nuna ciki ya tabbata kwana goma sha biyu”

Shiru ta kuma yimasa saboda ita ko mgn ma tsoron yimasa takeyi yanzu yace zai tumurmusheta, zama yayi a kusa da ita yace “waini kurma kinka zamane da bazakiyimin mgn ba saidai kallo kawai?” Yana mgnr yana ruqo hanunta janyewa tayi tasa masa kuka daidai lkcn Aunty Jameelah ta dawo dakin ya miqe a sanyaye ya kalli aunty Jameelah yace “tunda ta farka zamu iya tafiya ko?” Kallonsa tayi da yanayin jin zafi tace “eh ni daganan gda zan wucce sai kaje kayi jinyar matarka” murmushi yayi tare da juyawa ya fice ya lura tunda abinnan ya faru takejin zafinsa wai I me yar’uwa.

Fita yayi ya nemi likitan yazo ya dubata ya rubuta mata wasu magungunan ya basu sallama ya kamota domin tamiqe su tafi amma sai taji qafarta ta riqe daqyar takejan qafar tana hawaye harta isa motar ya bude mata ta shiga itama Jameelah ta shiga yaja suka nufi gdan.
Tunda suka taho babu wanda yace da wani qala tsakaninsu kowa da tunanin da yake saida suka biya ta sultan road din ya ajiye Jameelah a gdansu sannan yayi ribbas da sauri yabar gdan saboda yasan idan yasake Hajiya tagansu ya kadae don zata iya hanashi tafiya da Umaimah gashi jiya yaje gdan Sadiya ya tarar batanan ya kirata a waya bata dagaba qarshe ya tura Mata text tayo masa reply da cewa tatafi Abuja taron NGOs din da take aiki ransa ba qaramin baci yayi da lamarin ba wato kullum lamarin Sadiya qara tatura yakeyi kenan dole zaiyi maganinta a sabon salo tunda shida babu saki a tsarinsa.

Da wannan tunanin suka isa gdan yayi horn getman din ya bude masa ya shiga yayi parking ya bude ya fito tare da budewa Umaiman ya dagata cak ya nufi cikin gdan da ita ya direta saman kujera ya koma ya rufe motarsa ya dawo ya zauna kusa da ita ya dora hanunsa saman cikinta yace.

“Nasan baby na yanajin yunwa sosai ko?” Ya fada da sigar tambaya bata bashi amsa ba saima kawar dakai da tayi yayi murmushi yace “waini ya zanyi ne laifina yayi yawa kowa fushi yakeyi dani” sake kawar dakai tayi ya sake shigewa jikinta yace “wlh Allah ko ki saki ranki mu kuma normal ko na kulle gdannan dagani saike naita baki kina karba ko kinaso ko bakiso”
Da sauri ta dago idonta dake cike da hawaye bakinta na rawa tace “ka rufamin asiri Uncle na tuba bazan sake ba wlh” murmushi yayi yace “idan kika sake fah?” kuka ta saka tace “bazanma sakedin ba wlh”

Miqewa yayi ya cire rigarsa yace “shikenan na yarda amma idan kinka sake kinsan hukunci na” yana fadin haka ya nufi kitchen ya dauko mata fresh milk da snacks ya dawo ya zauna a qasa ya janyota jikinsa ya rinqa bata tanaci a wahale saboda bata sha’awar komai sama data kwanta tayi bacci, saida yaga tana dauke kai tana yatsina fuska sannan ya qyaleta ta kwanta a cinyarsa bacci me nauyi ya dauketa bai tasheta ba shima yaja pillow ya kwanta ya fara baccin harsai yamma liqis sannan ta tashi ta nufi dakinta tayi wanka tayi sallar laasar ta kwanta.

Shigowa yayi ya canza kayansa ya matso gadon yayi kissing lips dinta yace “lkc ya tafi sosai zan tafi gdan Auntynki sai zuwa safiya insha Allah ki kulamin da kanki da Baby na kiyi bacci cikin aminci my heart” yana fadin haka ya zura harshensa cikin bakinta ta lumshe idonta tare da tureshi tana janyo numfashi daqyar tace “don Allah kaje saida safen” murmushi yayi ya juya ya fice daga gdan ya shiga motarsa unguwar dake Layout ne har tayi shiru bakajin komai sai haushin karnuna.

Yana zuwa yayi parking ya shiga gdan da sallamarsa babu kowa a parlourn duk yayi qura murmushin takaici yayi ya bude dakinsa ya shiga yana tunanin kosai yaushene Sadiya zata canza ta zama nutsattsiyar mace da tasan darajar kanta da gdanta? Yauma saida ya gyara dakinsa ya wanke bathroom din sannan ya kwanta zuciyarsa cike da tunanin Babyn Uncle musamman da yasan ba cikakkiyar lfy ce da ita ba.

Wayarsa ya dauka ya kira layinta har tayi Ring ta gama tana gani bata daga ba saida kiran ya shigo a karo na uku sannan ta daga tace “hello Uncle” ajiyar zuciya yayi yace “kiyi hqr na tasheki ko?” Batayi mgn ba sai “uhm” kawai da tace sake cewa yayi “ya jikinki ya baby na” “da sauqi” ta fada a gajarce kafin ya kuma mgn ta kashe wayar gaba daya saboda batason yawan mgn.

Hakan ba qaramin taba masa zuciya yayi ba ya sake kiran wayar yajita a kashe gaba daya yayi qwafa ya ajiye tare da jan bargo yarinyar yaga alamun itama ta qaro wulaqanci saiya saita mata zama zasu daidaita, da wannan tunanin bacci ya daukeshi baisamu ganin Sadiya ba saida safe daya shirya zai fita itama ta fito zata fita har ya fita yaga bazai iya jurewa ba ya koma ya dubeta tanayi masa wani kallon wulaqanci yayi murmushi yace.

“Ban hanaki fita ba amma kisani fitarki itace warwarewar igiyoyin aurena dake kanki na fahimci kullum abin naki qara tatura yake Sadiya saboda haka zabi ya rage naki ko gantali a titi da sunan aiki ko zaman bautar aure” yana fada Mata hakan ya juya ya fice ya barta sake da baki bata taba tunanin haka daga garesa ba saida taji tashin motarsa sannan ta fito harabar gidan a fusace tana doka masa Kira amma ko tsayawa baiyi ba ya fice, kai tsaye gurin aikinsa ya wucce saboda tunda yake baitaba jin zafin abinda Umaimah tayi masa irin jiya ba.

Yana zuwa ya shige office dinsa ya kullo ransa a matuqar bace ga baqin cikin halin Sadiya sannan itama Umaimah ta qaro wulaqanci har lkcn tashi yayi yana jiran yaji ko zata kirashi amma shiru hakan ya qara tunzurashi daya tashi yayi kamar ya wucce gdan Sadiya sai kuma yaga rashin dacewar hakan saboda ko ba komai shine sanadin ciwon nata.
Yayi parking ya shiga gdan itama bata parlourn amma sabanin Sadiya gdan a gyare yake tsaf sai qamshi yake zubawa yayi murmushi ya murda dakin nata ya shiga.

Acan qarshen gadon ya hangeta tana kwance ta rufe duk jikinta da blanket haurawa yayi da sauri ya bude fuskarta idonta a rufe take amma sai hawaye take fitarwa da sauri yakai hanunsa ya taba jikinta yaji zafi sosai cikin tashin hankali ya dagota yana fadin “subhanallahi Baby bakida lfy shine baki fadamin ba” daqyar ta iya bude idonta ta kalleshi hawayen naci gaba da gangarowa.
Wayarsa ya daga ya kira likitansa ya fada masa abinda ake ciki yace gashinan zuwa, yana share mata hawayen yana lallashinta tare da bata hqr da haka Dr Saleem ya iso gdan ya fara dubata saida suka koma asibiti aka sake mata scanning sannan aka bata magungunan tare da shawarwari suka dawo gdan tun safe bataci komai ba sai yanzun daya tsaya yayo mata take away ya ritsata saida taci sannan ya qyaleta ya dauketa ya mayar da ita ya kwantar da ita yanata zuba mata sannu tana kwanciya bacci ya dauketa saboda maganin baccin da aka bata shikuma ya gyaranta kwanciya ya fita ya tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button