HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Bayan fitarsu Hafsat Hajjo tace”nifa ina ganin kamar aikawa Firddausi su Saudia sa koyi abubuwa kafin a zanawa Hafsat jarabawar november -december sun koyi wani abun se kawai a nemamusu karatu a Oxford tare su zauna a ɗaya daga cikin gidajen maimartaba a ganina”.
“aiko dai kin kawo shawara hakan ko za’ayi kinga setaje tayi musabaƙar daga can amma jibima za’ah kaita Abuja gurin karramar da za’ayimata kinga tana dawowa sesu wuce da Abdallah”.
“hakan yayi kuwa”.
nan suka tsaya a haka nan Jakadiya ta tafi tabar aminan sunata hirarsu sega su Hafsat sunshigo dukda Hafsat tana cikin ɓacin Marwan amma seta make nan tayimusu sannu Fatimah tace”kuje ku cinye ku wanke kwanukan ku mayarmata”.
“toh godiya muke gimbiya Fatimah”.
nan sukayi sama .

4:00pm
Billy da Zully ke tsaye a bakin ƙofar me babban ɗaki suna jira a dawo daga yomusu iso suna nan tsaye sega sarkin ƙofa yace”ku shiga”.
“toh mungode”.
nan suka shiga ciki ɗaga idon da Billy da zatayi taci karo da haɗaɗen photon F2 a zuciyarta tace”kenan F2 shine Umar kenan”.
Baya tafarayi hawaye na zuba a idanunta cikin murna Hafsat ta ruga da niyyar rungumeta ta!!!!!!

Tallah! Tallah!! Tallah!!!
Ina kuke masoyana na haƙiƙa kufito ku nunamun ƙauna ta hanyar siyan littafina mesuna BAR RAINA ALLURA (ITAMA ƘARFE CE) cikin farashi me sauƙi #200 kacal ta Asusun Bankin 2411022356 Zenith Bank Aisha Ibrahim aiko da shedar biyanki ta wannan number 08108362334 ko transfer VTU ta wannan number 08108362334 masoyana na Niger ku turo da katin Airtel ta wannan number 08108362334 sena jiku.

Nagode sosai da addu’o’inku ga mahaifiyata Allah yasaka da Alkhairi wannan pages ɗin nakune masoyana na haƙiƙa sonso fisabilillah ina fatan kowa yayi sallah lafiya Allah ya maimaitamana

Votes and Comments
Plz share

Daga Alƙalamin ƴar Mutanen Gwarzo.✍️n Gwarzo.*_ ✍️???? *HASKEN RAYUWATA*

MALLAKIN
REAL EESHOW

SUBSCRIBE
DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION

Wannan pages ɗin nakine Haseenan Masoya kiyi yadda kikeso dashi much love.

PAGE 2️⃣5️⃣➡️2️⃣6️⃣

     Zata goce kenan wata zuciyar tace"karki aikata haka Billy kitunafa babbar aminiyarkice wadda zata iya yimiki komai a rayuwa meye dan kinbarmata F2 wanda bemasan kinayiba itama datasan F2 ne da bazata aureshiba".

rungumeta Hafsat tayi inda Billy ta raɗamata a kunne tace”kice sweetheart ashe F2 shine mijinki”.
“eh shine sweetheart nima bansan shi bane kiyi haƙuri danasan shine da bazan taɓa bari ayi aurennanba”.
share hawaye Billy tayi tare da cewa”ki kwantar da hankalinki ƙawata nasan da kinsan F2 ne da bazaki taɓa aurensaba kidena damun kanki dama Allah yayi ba mijina bane kumama ai bemasan ina yiba wannan yazama sirri dagani seke se Zully mubar zancennan Allah yazaɓamana muma miji nagari”.
“toh Ameen ƙawata nagode sosai da kika fahimceni Allah yabarmu tare”.
“Ameen”.
nan suka saki juna ta rungume Zully sannan suka ƙarasa ɗayan falon dasu Ammi suke zaune itada Hajjo ƙarasawa sukayi har inda suke suka duƙa har ƙasa suka ce”Ina yininku”.
faɗaɗa murmushinsu sukayi tare da haɗa baki sukace”anyini lafiya baƙin yamma amma dai kwana zakuyimana ko”.
murmushi Zully tayi tare da cewa”masha Allah wlh wannance dukta ɓatamun lokaci tin safe naje gidansu Umminsu bata nan seda ta dawo sannan muka taho ba kwana zamuyiba yanzu zamu zo mu juya”.
“ayya aida kunsani kun taho da niyyar kwana da se gobe a kaiku”.
Hafsat ce tace”Ammi rabu dasu dolema su kwana yaza’ai sunsan ba kwana zasuyiba amma se yanzu zasuzo ai ni inda nice kwanakima zanje inyimusu”.
“kinji Zully wai kwanaki zatayimana itada ko son ta matsa daga gurin Ummita batasonyi kullum sede ta wuni bata taɓa kwanarmanaba ita ke cewa haka”.

Murmushi su Ammi sukayi Hajjo tace”kudeyi haƙuri ku kwanarmata tace itama zataje gidajenku ta kwana ko kishiyar nima indai shigarmiki dukda kin kwacemun mijina”.
murmushi Hafsat tayi tace”ai Hajjo ban kwacemiki shiba nina barmiki shima”.
“toh shikenan godiya nake koda yake tsoro kawai kikeji dan kinga nafiki kyau shine kika wayince”.
dariya duka sukayi nan Fatimah tace”kinji Hajjo ke ai kinyi mishi tsofa mezeyi da tsohuwa”.
dariya nan akayi nan Ammi tace”kushiga kunbar baƙinku a tsaye kushiga dasu ciki”.
“toh”.
nan suka wuce ciki inda Fatimah ta wuce dasu wani haɗaɗen falo baki da fari me kamar hadari-hadari kalle-kalle suka shigayi seda Hafsat tace”ku zauna man sarakan kallo”.
“ke barmu muga aljannar duniya da kike ciki”.
dariya Fatimah tayi tare da cewa”Aunty bara nasaka akawomusu abin motsa baki “.
“toh sekin dawo”.
nanta ta tafi zama sukayi Billy ta kalli Hafsat tace”gaskiya sweetheart ke me sa’ah ce a rayuwa Zully kalli irin wannan aljannar duniyar da muke fata abu yafara tabbatuwa to kingani keda muke cemiki munmiki Ahmad kike cewa a’ah ashe me gayya me aikima zaki aura to muma kiyi ƙoƙari ki haɗamu da abokansa maci duniyarmu muma da tsinke”.
Hafsat a zuciyarta tace”hmm bakusanma angon besan da aurenba da kunsan rayuwar da zanyi da bakuce hakaba”.
taɓata taji anyi hakan yasata firgigit kallonta Billy tayi tare da cewa”lafiya ƙawata keko meke damunki haka dukda irin wannan aljannar duniyar da kike ciki”.
murmushi Hafsat tayi tace”wlh bakomai kawai dai ina tinanin yanzu kome Ummita takeyi da Bappah oho gashi nayi missing ɗin Yah Aminu shima”.
“suna cikin ƙoshin lafiya insha Allahu ki kwantar da hankalinki”.
“Allah yasa”.
“Ameen kikuma dena cema Yayah Aminu kikoma cewa a gayance Al’amin kinsandai yanzu ba da bace a gidan ƴan gayu kike kokoso kike a rainamu eye”.
“wannan haka yake Billy komai a riƙa yinsa na girma bana ƙauyanciba”.
dariya sosai Hafsat tayi ta gode Allah sannan tace”Allah ƴan gayu masu wankada sugar”.
“faɗi ki ƙara yarinya baki isa kinja an rainamanakeba ehe”.
dariya tayi sosai tace”amma gaskiya nayi missing ɗinku sosai wlh harkun fara sani nishaɗi”.
jisukayi kuyangi sunce”salamu alaikum”.
“wa’alaiku salam kushigo”.
nan suka shiga ko wacce da kwanukan kayan alatu suka jere a gabansu Zully se zuwa can sega Fatimah tashigo cikin wasu english wears skirt da riga bakinta ɗauke da sallama ta zauna kusa da Hafsat murmushi Hafsat tayi tace”wai sis harkin kuma yin wanka kamar wata agwagwa”.
“kai Aunty wai agwagwa”.
“barta tashaƙata lokacinkine Fatimah ci zamaninki karki tsaya ƙauyancin”.
“wlh kuwa Aunty Billy”.
“atoh”.
Zully tafaɗa tare da kai farfesun naman rago bakinta nan sukaci sukasha ba kunya seda suka taƙe cikinsu sannan Fatimah tace”Aunty bara naje gidansu ƙawata na amso takarduna nadawo”.
“toh sekin dawo dan Allah sis karki daɗe”.
“toh Aunty”.
“kai amma Fatimah kema ƴar hannu ce ko”.
dariya Fatimah tayi tare da cewa”eh mana Billy ainima duk haka nike”.
wani daɗine yakama Billy jin acemata Aunty yasata cewa”kace duk haka muke “.
“eyi”.
nan Hafsat tace”toh Allah ya shiryamunku”.
“Ameen”.
nan Fatimah ta tafi suka cigaba da hirarsu zuwa can Billy tace”ke Zully kizofa musan nayi kar dare yayimana a gidan mutane”.
hararta Hafsat tayi tace”bako inda zakuje”.
“aiko in hakane sede ki tambayarmana su Mamah wlh inkece zasu barmu”.
“toh ku bani no sena kira a wayar Fatimah inta dawo”.
“gama keypad ɗina”.
Zully ta miƙamata cikin zumuɗi tasanarwa dasu mamansu ba musu suka amince da zummar washe gari sukoma da wuri nan tayimusu godiya sukayi sallama suka cigaba da hirarsu cikeda so da ƙauna.

Zaune yake a office ɗinsa yana making ɗin exams tashigo da zumbulelen hijab ɗinta bakinta ɗaukeda sallama ba tare daya ɗagoba ya amsa ƙarasawa tayi har kusa da kujerarsa ta duƙa tare da cewa”Malam ina yini”.
aje making ɗinda yakeyi yayi tare da kallon Habibah kamar zega wani abun yace”lafiya ƙlau ki zauna akan kujeraman”.
“toh Malam nagode”.
“bakomai”.
tashi tayi ta zauna akakujera tayi ƙasa da kanta tanata tinane-tinane yayinda ƙirjinta keta dukan tara-tara a zuciyarta tana cewa”nashiga uku nasan wa’innan ƴan iskan yaran ne suka faɗamasa nina kada wannan yarinyar shine ya kirani yaci ubana”.
tana wannan zancen taji yayi gyaran murya kuuuu cikinta yabayar amma seta make jitayi yace”Habibah baki kyauta ba duk abubuwan da kikayiwa Hafsat shi ɗan adam ba’ah yimasa haka domin bakasan ranar da zeyimaka kuma bakasan irin baiwar da Allah yayimishiba koba komai yarinyar bameson fitina bace kowa yayi fishi da baƙo yaji kunya ashe dama kan nace inasonta kikemata haka Habibah ni meyasa baki tareni kinmunba segashi dukda irin abubuwan da kikayimata ta iya roƙata dan Allah na aureki sannan kuma ta bani ɗaya daga cikin kujerun makkan data samu”.
saurin ɗaga kai Habibah tayi murya na rawa tace”ita Hafsat ɗin tana ina”.
taƙarasa maganarta kamar zatayi kuka murmushi yayi tare da cewa”Hafsat tana ɗakin mijinta”.
hawayene suka fara zubomata tace”a gaskiya na cusgunawa rayuwar Hafsat sosai tunda aka kawota makarantarmu musamman danaga da ni nakeyin firt position tazo takoma ita kemana ina mugun sonka duk class ɗinmu ba wanda besaniba kaikuma duk alamun dana nunamaka seka nunamun baka ganeba daga ƙarshema ka kirata ka faɗamata kanasonta tundaga ranar nikuma naƙara tsanarta amma banji daɗin wannan abu dana aikataba kayimun kwatancen gidanta naje na bata haƙuri”.
murmushin takaicin abubuwan data aikata M. Jalaludeen yayi tare da cewa”Habibah kenan ai yanzu wutsiyar raƙumi tayi nisa da ƙasa domin yanzu zancen da nikemiki Hafsat babban ɗan sarkin jihar kano take aure barima kiga hotonshi inyomiki downloading ɗinsa shiyasa mahaƙurci mawadaci”.
hawayene ya zubowa Habibah tace”yanzu ni dama zanganta dana bata haƙuri akan abubuwan dana aikatamata ai jibi zakuje bikin karramata dan Allah ka temaka ku tafi dani nabata haƙuri”.
“toh shikenan Allah yakaimu zanyi ƙoƙari naga muntafi tare kin bata haƙuri”.
“nagode”.
nanya shiga download aiko nan take hotunan F2 haɗaɗu dayayi update suka bayyana ya waigarmata da waya yace”toh sweetheart kinga mijinta”.
murmushi tayi alamar kunya ta rife fuskarta dariya yayi me sauti yace”nabaki kunyako sorry my Baby kalli kigani”.
“toh”.
nanta kalla ganinshi tayi yayi mugun kyau nan take tafara raina kanta tace”Malam aiko na taɓa ganin hotunan wannan a system ɗin da Bilkisu ke zuwa da ita suna kalla”.
“to shine mijinta”.
“masha Allah , Allah yabasu zaman lafiya”.
“Ameen”.
nan suka shiga hirarsu ta masoya cikin nishaɗi yayinda Habibah keta danasanin abinda ƙawarta Jamilah taita sakata tana yima Hafsat.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button