HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Wani tuƙuƙin baƙin cikinsu Abbakar ne ya turniƙe zuciyar F2 yayinda wani haushinsu yakamashi harya kasa control ɗin kansa ya saki wata uwar tsuka yana huci kamar wani kumurci ya haye sama ba tare da yace musu komaiba da kallo duk suka bisa harya ɓacema ganinsu Adam yace”naga F2 haye sama a fusace kamar bashine yagama murmushi ba”.
“wlh kuwa nima mamakine ya kamani kodai ya tino da Amminsa ne?”.
“gaskiya a’ah kodai maganar da mukeyi ce ta ɓatamasa raine”.
“a’ah sede in tinowa yayi da Amminsa kai sanin kankane F2 ba shiga harkar mace yakeba “.
“haka ne kam ni wlh idan naga duk mood ɗinsa ya canza se inji duk banji daɗiba”.
“wlh kuwa to kutaho mutafi mubarshi ya huce”.
nan suka tafi kowa jikinsa a mace.

F2 ko na shiga bedroom ɗinsa ya faɗa kan bed ɗinsa ya lumshe sexy eyes ɗinsa tinowa yayi da haɗe ran da yayiwa su Ahmad a fili yace”meyasa nayimusu hakan akan wannan yarinyar mara kunya karfa su zata sonta nike dan akwaisu da fassara mema zanyi da wannan kwailar dako ƙirjin kirki bata dashi “.
tinowa yayi da ranar da sukaje siyen turare jiyayi wani murmushin da be shirya yinsaba ya suɓucemasa a zuciyarsa yace”to kuma meyasa raina ya ɓaci dan ana ƙoƙarin ɓatamata tarbiyya “.
wata zuciyar ce tace”kawai dan kana tausayin iyayenta ne kar a ɓatamusu tarbiyyar yarinya amma badon mara kunyar ba”.
nan yayita maganganunsa har bacci ya awon gaba dashi.

Zaune suke a main falo ana hira wayar Aunty Fido ta shiga ringing ɗauka tayi tare da cewa”salamu Alaikum”.
“wa’alaiki salam “.
“Ammi anyini lafiya”.
“lafiya ƙlau ya daughters ɗina”.
kallonsu Hafsat Aunty Fido tayi tare da cewa”lafiyarsu ƙlau Ammi”.
“masha Allah dama Admission ɗinsu ne ya fito shine nace bara na sanar dake”.
“wow masha Allah yanzu to yaushe za’ah kaisu kenan yaushe sukace zasu fara lecture”.
“Monday sukace”.
“a’ah Ammi kice abun yazo kenan gobefa”.
“eh wlh seki shirya da safe ki kaisu Abdallah yayimusu registration”.
“toh Allah yakaimu “.
“Ameen”.
nan sukayi sallama kallon su Hafsat Aunty Fido tayi tare da cewa”Admission ɗinku ya fito”.
tsalle sukayi nan ta sanar dasu gobe za’ah kaisu sosai suka nuna farin cikinsu.

Addu’arh tashi daga barci yayi tare da miƙewa ya tuɓe kayansa ya ɗaura towel yashiga toilet be wani jimaba ya fito sanye da rigar wanka zama yayi akan kujerar dressing mirrior ya busar da gashin kansa sannan yashiga shafa be wani da daɗeba ya isa gaban wardrobe ɗinsa ya ɗakko wata haɗaɗiyar white arman suite white me tsadar gaske ya saka ya ɗaura necktiet red ya zura takalmi red agogo red yasaka ɗan kunne nanya wani fito kamar me shirin gasar kyau ya isa gaban madubi ya feshe jikinsa da turarukansa masu daɗin ƙamshi ya fita a falo yasamu su Ahmad sun dawo kallonshi sukayi da mamakin irin kwalliyar da yaci kamar bashi bane ya haye yakejin haushi ba har ze wuce Abbakar yace”bro kayi kyau sosai “.
murmushin gefe baki yayi tare da cewa”thanks”.
ya wuce da niyyar fita Adam yace”ina zuwa haka bro”.
a taƙaice yace”yanzu zan dawo”.
“ok na ɗaukama zance zaka danaga kasha wanka da wannan yammacin”.
hararshi yayi nan gabaki ɗaya sukayi dariya shima dariyar yayi ya wuce abinsa be wuce ko inaba se a Airport yahau jirgi ya nufi Saudia.

Yana zuwa yashiga motar hotel ɗin da ya kama suka nufi Riyadh sunzo wucewa ta gurin mall ɗin daya siyi turaruka yace”zanshiga store ɗinnan”.
“toh ranka shidaɗe “.
drivern yafaɗa tare da yin parking ya zaga ya buɗemasa ƙofa cikeda jan class ya fita yayinda ƴammatan gurin duk suka ruɗe ganin F2 shikaɗai ba tare daya kula kowa ba ya wuce ya shiga tsintar kansa yayi dason ganin gurin daya ganta nan zuciyarsa taita azazzalarsa dayaje gurin nanko ya nufi gurin a tinaninsa ko ze ganta yana zuwa yaga wayam a fili ya furta”innalillahi wa’inna ilaihi raji’un meke shirin faruwa danine haka kan wannan yarinyar ? “.
jiyayi ance”wacece wannan haka da har tashiga zuciyar Hammana ta sacemasa zuciya”.
damm gaban F2 yabada sakamakon jin muryar Abdallah haɗe rai yayi tare da cewa”yaushe kazo nan gurin”.
yaƙarasa zancensa cikin ƙara haɗe rai dan karya yimasa magana murmushi Abdallah yayi yace”na gama siyayyar Fatima kenan zanfita naji wasu ƴammata na cewa ga F2 shine na tambaya akacemun nan kayo”.
“ok ina ita sweetheart ɗin take ita?”.
“tana gidan Aunty gobe zata dawo kusa dakai ai”.
“ok nima zan biya gidan Auntyn se muyi sallama da My Only na”.
“Hamma baka bani amsar tambayata ba”.
yi yayi kamar bejisaba yafara tafiya bin bayansa shima suka hau lift tv gurin ce aka hasko maimacin musabaƙa inda aka hasko Hafsat tana karatu kafeta yayi da idanunsa dake maƙale da baƙin glass jin Abdallah yayi yace”Hamma kaga wannan yarinyar nan da take karatunnan budurwar Hafiz ce ita yakeson ya aura shima yana ɗan ƙarasa lefe da be gamaba idan muka fita kwa gaisa”.
F2 jiyayi abu yazo ya tsayamasa a wuya yanayinsa lokaci ɗaya ya canza dariya takusa suɓucewa Abdallah na ganin yadda yanayin ɗan uwansa ya canza har suka sauka daga lift ɗin bece komaiba nan ya nufi hanyar fita Abdallah dake dariya ƙasa-ƙasa yace”a’ah Hamma ka fasa siyayyar ne naga kana niyyar fita?”.
“kana da damuwa Abdallah eh nafasa”.
“toh Hammana”.
nan yayi gaba yabi bayansa yana dariya abokin Abdallah wato Hafiz yana ganinsu ya fito daga mota yaƙarasa gurinsu yaɗan duƙa tare da cewa”ina yini Yah Farouk”.
F2 ko tsintar kansa yayi dajin duk duniya bashida maƙiyi kamar Hafiz ƙin amsawa yayi tare da nuna kamar bejiba yayi gaba ya barsu Abdallah bin bayansa Abdallah yayi tare da cewa”Hamma Hafiz na gaidakai baka amsa ba “.
cikin zallar kishin dake damunsa ba tare daya saniba yace”dolene sena amsa bazan amsaba”.
yaƙarasa tare da buɗe mota ba tare daya bari an buɗemasaba ya shiga nan driver yaja da niyyar su nufi cikin Riyadh cikin muryar ɓacin rai yace”ka maidani Airport”.
“toh sir”.
nanya juya yakaishi Airport.

Yana tafiya Abdallah yashiga dariya yaƙarasa gurin Hafiz dake mamakin abinda yayan nasu yayimasa yace”kadena mamaki Hamma fa yafaɗa soyayyar matarshi ba tare daya saniba bakaga yaƙi kulakaba cemasa nayi budurwarka ce Aunty Hafsat shinefa yaƙi amsa gaisuwarka”.
“hhhhh gaskiya yabani dariya kace kishi ke damunsa”.
“sosaima kuwa lokacin ramuwarmu yayi abin mamaki wai yau Hamma yasa dogon wando a jikinsa tab dole Aunty Fido tasha labari”.
nan sukayita dariyarsu seda sukayi me isarsu sannan suka tafi.

fitowa Aunty fido tayi ta samu Fatimah a falo tana waya ƙasa-ƙasa murmushi tayi ta ƙarasa gurinta cikin tafiyar sanɗa harta isa bayanta bata saniba shauƙin soyayyar da take ciki ji Aunty Fido tayi Fatimah tace”I love you my heart desire”.
bazato taji ance”yayi masoyan asali”.
a razane Fatimah ta kashe wayarta jikina ɓari tayi ƙasa da kanta murmushi Aunty Fido tayi ta zauna kusa da ita takamo hannunta tace”ɗiyata ki kwantar da hankalinki ba abinda zan miki inason ki faɗamun dawa kike wannan wayar inaso ne insani kinsan yanzu zamani ya canza dolene a matsayina na Auntynki insan dawa kike tare”.
cikin jin kunya tana wasa da yatsun hannunta tace”ammm da Yah Amin ɗinsu Aunty Hafsat nake waya”.
murmushi Aunty Fido ta faɗaɗa tace”masha Allah kice ƴar gida za’ayi kenan to Allah ya shigemana ya tabbatar da alkhairi kinji daughter”.
sosai Fatimah taji daɗin maganganun Aunty Fido cikin jin kunya tace “Ameen Aunty”.
sakkowa yake daga stairs ɗin falo da sauri ze fita yana ɗaura agogo yaji Aunty Fido tace”Son gani nan kake wani sanɗa”.
Salman dake tinanin bakowa a falone ya juya tare da ƙaƙalo murmushi tare da cewa”Aunty ɗauka kina part ɗin Dady”.
“a’ah gani nan”.
nanya ƙarasa ya zauna cikeda soyayya Aunty Fido tace”Son meke damunka da kake ƙoƙarin salwantar mana da rayuwarka”.
ƙasa yayi da kansa tare da cewa”Aunty bakomai”.
“ban yaddaba ɗago ka kalleni”.
ɗaga kai yayi ya kalleta a zuciyarsa yana tino maganganun Abbah a zuciyarsa yace “Aunty kiyi haƙuri bazan iya faɗamikiba”.
a fili kuma tsintar kansa yayi da yimata ƙarya yace”Aunty wata yarinya nake mugun so ita kuma bata sona”.
murmushi Aunty Fido tayi tare da cewa”ka kwantar da hankalinka kayita addu’ah kana neman zaɓin Allah insha Allahu zata soka “.
“toh Aunty nagode”.
“bakomai Son kadena sama kanka damuwa karta haifarmaka da wata matsalar”.
“toh Aunty”.
nan taita yimasa nasiha su Abdallah ne suka shigo zama sukayi Abdallah yace”Aunty Hamma yazo gidannan”.
“a’ah yadai turomin da text zezo”.
“hhhhh haɗuwa mukayi dashi a store yaje gurin turaruka yana shauƙin ƙauna “.
dariya gabaki ɗaya sukayi nan yabasu labarin komai sukaita dariya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button