HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Bayan sungama taken Nigerain larabci principal yafara magana kamar haka”a gurguje dama ba wani abubane yasa na tara gabaki ɗaya makarantar nanba se inason shedamuku da gobe in Allah yakaimu za’ah fitar da wa’inda za’ai musabaƙar gari dasu shine nakeson kufito da wuri domin so nake ayi komai da wuri a fitar dan haka gobe baza’ai lesson ɗin safe ba saboda ayi da wuri”.
haɗa baki sukai gurin cewa”Allah yakaimu Malam”.
haɗa ido Hafsat tayi da M. Jalaludeen hakan yasashi sakarmata smile aikon akan idon Habibah dake kallonsu jitayi kamar tayiwa Hafsat duka itako Hafsat ƙasa tayi da kanta nan principal ya tambayi Malamai koda me abin faɗa sukace babu nan aka sallamesu kowa ya tafi nan Hafsat ta nufi titi ta jira abin hawa tana samu tahau ta tafi.

Misalin tara na dare zaune Hafsat take tanacin tuwo tana bawa Aminu yayanta labarin haukan dasu Zully suketayi yanata shan dariya sukaji an fasa kururuwa a babban gida kallon juna sukai Aminu yayi tsaki tare da cewa”mtss kawai ankatsemana hirarmu da wani ihun bazan aradu ƴan gidannan sesu kashewa mutum zuciya”.
“katashi muga meyafaru”.
“inma kinje takice zatafi zafi”.
gani sukai Ummita ta fito daga zagaye da sauri ta zagaya hakan yasasu tashi suma suna zagayawa sukaga Habu nata rintuma uban kuka yana cewa”Iyah sunsa ansace mun kekena”.
duba keke Iyah tayi taga tsohon keke kangarwa wato tsurane wannan nan kowa ya fito daga ɓangarensa haɓa Lantana ta kama tare da cewa”Iyah Allah su suka saka a canzamasa tunda suna baƙinciki daba’aba ƴarta ba karki kyalesu”.
“aje tsurar nan nangurin bara Iron yazo bata isaba wlh saboda hassada”.
jin haka yasa Ummita takama hannun ɗiyarta sukai ɓangarensu harara duka ƴan gurin suka bisu da ita ana haka segasu Bappa sun shigo nan Iyah ta fashe da kuka tana cewa”wato shanyeka da akai har yakai in zartar da hukunci kan gaskiya a nunamun iyakata zanzare hannuna akanka Iro”.
“banganeba Iyah meyafaru kike kuka”.
“jibi keken da ƴar gwal ɗinka tasa aka musanyawa Habu marasa asali wayasanima ko ƴar shegece aka gudo nan aka ɓoyemana”.
nanfa gulma ta kauraye gida abinka da gidan yawa Iyah taita cin mutuncin su Lantana da facalolin Ummita na tayata aka dawo kan Hafsat nanma akadasa Ummita naji ba yadda zasuyu dan sunriga sunsaba da cin mutuncinsu da Iyah da mutanen gari sukeyi kan rashin asali.

Washe gari da wuri Hafsat tagama duk abubuwan da zatai ta shirya tahau mota ta nufi makaranta tana isa!!!!

*Warning *
Idan kinsan baki iya comments ba kiyi out dan Allah salin alin kafin na fiddaki dakaina kuma mutanen facebook idan kinsan baki iya vote ba karki karantamun domin rashin comments and vote ka iyasa namaida book ɗinnan na kuɗi.

More Votes and comments
More typing
pz share

Daga Alƙalamin ƴar mutanen Gwarzo._r mutanen Gwarzo.* ✍️???? *HASKEN RAYUWATA*

MALLAKIN
REAL EESHOW

Elegant online writer’s

DUNIYAR LITTATAFAN HAUSA TV
http://ww.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dLOe_AqkiQ

PAGE 0️⃣5️⃣➡️0️⃣6️⃣

     Tana isa a bakin get ta tadda tarin 'yan makara tsaitsaye cikiko harda Habiba suna jiran M. Jalaludeen dayasa a taresu gaban Hafsat ne yabada damm a zuciyarta tana cewa"nashiga uku duk saurin da nakeyi dan karna makara amma seda Iya ta jazamun na makara gashi M. Jalaludeen ne keda duty ya zanyi ".

jiki a sanyaye ta k’arasa inda mutane ke tsaye .

Jamila k’awar Habiba ceta kalli Habiba tace”gafa mutuniyar nan ta makara maga M. ze doketa kokuwa”.
“hmm naga shegiyar bara mugani inko be daketaba mu ya dakemu da semunyi maganinta wlh”.
“Wlh kuwa”.
Hafsat nak’arasawa taba kowa na gurin hannu hartazo gurinsu Habibah k’in amsar hannun tayi tare dayin wata uwar tsaka tace”saboda munafunci da yin abu badan Allah kullum mutum seya nuna yafi kowa sani besan a banza nake kallonshiba”.
murmushi Hafsat tayi tare da matsawa can nesa dasu ta tsaya.

M. Jalaludeen ne yafito hannunsa rik’eda bulala idanunsa ya sauka akan Hafsat dake magana da wata ‘yar class d’insu jiyayi wata kasala ta saukarmasa musamman dayaga tayi wani farrr da idanunta aje sasu yayi duka suka matso cikin kasalaliyar murya yace”meyasa kuka makara bayan kunsan za’ayi muhimmin abu?”.
yak’arasa maganarsa tare da satar kallon Hafsat aiko karaf idanunsu yafad’a cikin najuna saurin k’asa tayi saurinyi da idonta aiko hakan yayi daidai da d’agowar k’awar Habibah Jamila domin bak’aramin mamaki yabataba ta tab’a Habiba tare da cewa”lallai ma wannan mutumin kinsan meyake nufi wato tunda da ‘yar gwal baze doki kowaba da bata da wlh seya dakemu “.
tak’arasa maganarta tare da nunawa Habiba M. jalaludeen yadda yaketa sakin smile wani abune ya tsayawa Habiba a zuciya ko mgn kasayi tayi nan gurin kowa ya fad’i dalilinsa amma Banda Hafsat da kunyarsa dukta lulub’esa takasa d’agowa nan yace”kowa yayi sauri ya nufi class ankusa farawa”.
godiya sukai masa suka tattafi Hafsat tazo dafdashi yace”my love kar a k’ara makara”.
rife fuskarta tayi cikeda kunya ta wuceshi tashiga class nan shima ya wuce abinsa .

Tana shiga ta taddasu Billy da zully suna ganinta suka sakarma juna murmushi tak’arasa seat d’insu ta zauna tare da cewa”wash”.
dariya Zully tayi tare da cewa”ai yanzu muka gama cewa Allah yasa kar a daki ‘yammakara”.
“hmm ai bakusan yadda naji dana tarar na da ‘yammakara Allah ne ya temakemu be dakemuba”.
“amma nayi mamaki sosai dabe dakekuba k’ila dan musabak’ar daza’ah fara ne”.
cewar Billy dake aje hisunul-mulim a hannunta damm gaban Hafsat yabada dakyar ta tattaro nutsuwarta danji tayi yawun bakinta ya k’afe k’af tace”eh nima abunda nace kenan”.
“Hmm to Mrs Ahmad”.
dariya Hafsat tayi tare da cewa”kudai an ragi ‘yar kwata wlh mezanyi da wannan arnen banzan”.
“to mudai kokinaso ko bakyaso mun zab’amikishi yarinya ko zully”.
dariya tayi Zully ce tace”hak’un ‘yar gari wai basu k’ara saki hotuna bane inaso inga Habibinah fa”.
“bara mu duba”.
ta k’arasa fad’a tare da bud’e system d’inda ke gabansu nanta shiga duba new update d’insu seko tayi sa’ah sun saki vedeos nanta shigar musu na farko F2 ne yafito dagashi se Kayan swimming jikinsa duk yasha tatuu rad’a-rad’a gashin kannan yasha gyara se kyalli yakeyi da wani glass shima da alama na swimming din ne ya fad’a ruwa suma sauran da irin shigarsa suka fad’a sukaita nink’ayarsu seda sukai me isarsu sannan F2 ya fito wata mata Tasha wankan mini skirt tazo da towel se karairaya takeyi ana wani tuturo k’irji suma sauran fitowa sukayi kowa da budurwarsu anata shafeshafe inka gansu bazaka d’auka musulmai bane shiko F2 tana bashi ya wuce abinsa cikin takun isa da k’asaita.

“Mitsss aikin banza ni wlh kuna bani mamaki Zully da kuke tsayawa kallon wa’innan sakarkarun ni Banga abinsoba a garesuba da har mata suke sonsu”.
“kece dai bakiga abinsoba mu wlh indai zasu auremu zamu auresu keko Billy?”.
“sosaima kuwa Kuma kema dole ayi dake dan tare muke wannan fighting din gaba d’ayanmu mukeyi ke amma se k’auyanci kikemana zakija mu fasa had’aki da Ahmad d’in wlh”.
“Wlh kuwa danko makkarma semu fasa”.
dariya Hafsat ta tintsire da ita tare da cewa”indai wa’innan sakarkarunne bana yimuku fatan Kuma ku had’u dasu bareni najid’in “.
suna wannan maganar sega M. Jalaludeen ya shigo da sauran Malamai shiru gurin ya d’auka.

M. Shamsu ne ya kalli d’alubai class d’in tare da cewa”baku mantaba yau za’ah fara gudanar da musabak’ar classes Wanda za’ah fitar da wa’inda zasu wakilci Jawahirul-qur’an a garinnan to zamu fara takan class Rap ta fito ta zauna muyi mu fara saboda wasu sun dad’e da farawa”.
damm gaban Hafsat yabada ta kalli su Billy tace”wlh ni tsoro nakeji wlh memakon yafara takan wasu aiba se lallai takainaba”.
“eyi nima dai banso ke Zaki faraba amma bakomai na yarda dake sweetheart zaki iya ai duk mune”.
Billy tak’arasa tare da kwarawa k’awartasu guiwa domin basu tab’ayin musabak’aba sedai tayi musu karatu jiki a sanyaye ta tashi da zabgegen hijabinta cikin nutsuwa ta k’arasa inda kujerar da aka aje take ta zauna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button