HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Votes and Comments
Plz share

Daga Alƙalamin ƴar Mutanen Gwarzo.✍️o.*_✍️???? *HASKEN RAYUWATA*

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION

PAGE 5️⃣1️⃣➡️5️⃣2️⃣

    Suna shiga cikin masarautar sukayi parking lokaci ɗaya abubuwan dasuka faru da rayuwarshi suka dinga dawowa kansa Doctor Fu'ad ne yayi ƙarfin halin cewa"abokina mun ƙaraso lafiya naga tinda muka taho bakace dani ƙalaba ko wani abun nayimaka".

buɗe idanunsa yayi da suka canza kala tsabar ɓacin ran karya rantsuwarsa da yayi yadawo 9ja yayi akan doctor Fu’ad kamar besan yin magana yace”meka gani bakomai”.
“gani nayi duk yanayinka ya canza”.
cikin ƙosawa da maganar yace”bakomai”.
yafaɗa tare dakai hannu ze buɗe murfin ƙofa tarar numfashinsa Doctor Fu’ad yayi da cewa”matar nan da akayiwa aiki gobe zamu sallameta tace tanason ta ganka tayimaka godiya”.
“okay gobe idan Allah ya kaimu zanzo asibitin naku duba marasa lafiya”.
“okay to Allah yakaimu seka shigo”.
“Ameen”.
nan ya fita daga motar ba tare daya nufi cikin gidaba yabi ta wata haɗaliyar ƙofa da flower ɗinsa a cikin wata jaka yashiga part ɗinsa gani yayi yana nan yadda yabarsa ba abinda aka canzamishi sede kullum da Ammi zata saka a gyaramasashi tsaf asaka turaren wuta wucewa yayi bedroom ɗinsa direct ya aje jakar hannunsa a bedside drower ya zauna gefan gado tare da cewa”wash a karo na farko Hafsat kin karyamun budget na dawo 9ja saboda ke kuma cikin masarautarmu abinda nafi tsana a rayuwata”.
yaƙarasa zancensa a raunane shafa sumar kansa yayi tare da tashi ya tuɓe kayansa ya ɗaura towel yashiga haɗaɗɗen toilet ɗinsa be wani jimaba ya fito yana tsane ruwan jikinsa sannan ya jona handryer ta busarmasa da gashin kansa tsaf ya shafeshi da haɗaɗun mayukansa ya saka kayan daya saba sakawa ya ɗaure gashin kansa kamar kullum ba abinda yike sakawa a jikinsa dabe sakaba ya kalli kansa a madubi yace”yau zan bayyanamiki sirrin zuciyata My Angel”.
yaƙarasa zancensa yana murmushin gefan baki yayi sallar isha’ih sannan ya fita cikin sauri ya nufi part ɗin Ammi.

Kaciɓus sukayi da Fulani a wajan shiga part ɗin Ammi yi yayi kamar begantaba ya wani shareta gabanta ne yayi mugun faɗuwa a zuciyarta tace”kan ubancan mezan gani haka badai wannan ɗan iskan yaronne ya dawo gida ba ammako inhakane dole ne gobe da sassafe naje gurin Boka Matsatstsaku shida yacemun yaronnan bazeƙara marmarin son yazo ƙasarnanba bare yazo segashi haryama sauka a cikin masarautarnan bazan taɓa bari shirina ya rugujeba koda zan rasa zanin ɗaurawa bazan bari ku daidaita da mahaifinkaba inma wannan tsohuwar najadunce ta dawo dakai wannan karon har ita zan haɗa”.
tana ƙarasa maganar ta haɗiyi wani miyau muƙut ta ƙaƙalo murmushin munafunci cikin ƙissa irinta ƴan bariki tace”a’ah wazan gani haka a cikin masarautarnan kamar Son ɗina amma shine zaka dawo koka kirani ka sanar dani inshiryamaka tarbar manyan baƙi”.
fuskarnan kamar kullum a haɗe ba alamar annuri yace”eh Umma nine ya gida ya kwana biyu”.
“lafiya ƙlau Son gaskiya nayi kewarka sosai”.
murmushin dabekai zuciba F2 yayi sakamakon tino lokacin data yimasa sharrin sacemata agogo da yayi yace”nima haka”.
“aiko bara naje na haɗamaka ɗan abin motsa baki kafinka ƙaraso”.
“toh”.
nan ta wuce cikin sauri kuyanginta sukabi bayanta dogon tsuka yaja tare da taɓe baki ya shige part ɗin Ammi.

Samun Ammi yayi da Fatimah suna shan lemon kankana zama yayi kusa da Ammi yace”Ammina shine zaki taho 9ja kokiyimun sallama sede Aunty Fido ke faɗamun “.
yana ƙarasa maganarsa yana wurga ido ta cikin glass ta inda zeganta ta ɓullo ƴa dariya Ammi tayi tare da cewa”ai gani nayi ka fita a fusace basena ɗauka ko wani abun zakayi a wajeba irin wannan kwalliya haka Magajin Malam kodai ka samu wadda kakeso ne ba labari”.
“hmm kede kawai kice kinfi son wannan sarkin cin”.
yafaɗa yana kallon Fatimah dariya gabaki ɗayansu sukayi Fatimah tace”wato Hamma kaima ka zama Yah Abdallah kenan hmm”.
taƙarasa zancenta cikeda shagwaɓa murmushi yayi wanda har seda beauty point ɗinsa suka lotsa yace”sorry sweetheart wasa nikemiki nagane anata shan fruit ɗin ko a kulani”.
“hhhh ya haƙuri Hammana ga Fruit ɗinnan kasha kaji bakaji irin daɗin da sukayiba lokacin da muna U.k kullum shi mukeyi musha kayanmu”.
“hmm bani naji”.
miƙamasa tayi ya ansa yasha girgiza kai yayi tare da cewa”kace sweetheart an iya abun mutane ammafa yayi daɗi”.
“nagode”.
hira sukayi tayi yanaɗan jefamusu baki wata kuma yayi shiru yanata wurga idon ta inda zega Hafsat shiru bata ba labarinta har guraren Sha ɗaya Ammi ta tashi zata shige ɗaki F2 ya miƙe tare da yin tsaki murya a ƙasan maƙoshi yace”Ammi seda safe”.
“toh Allah ya tashemu lafiya gobe zan wuce Adamawa nasan kafin ka tashi daga wannan baccin muntafi sede nacemaka semun dawo kenan”.
“toh Ammi sekun dawo bye sweetheart”.
“bye Hamma have a nice night”.
murmushi gefan baki yayi ya wuce part ɗinsa yana shiga ya jefar da takalminshi yayi a falonsa sannan ya shige bedroom ɗinsa yakai -yakawo yace”amma gaskiya yarinyar nan tana wahalar dani amma kuma ai Ammi tace mutum inyana soyayya sauke komai nasa yakeyi yabi yarinyar hakan yana nufin nima dole sena yada miskilanci sannan zata saurareni kenan to hakan zanyi yana iya Allah yakaimu da safe zanyi ƙoƙari mu haɗu kafin su tafi na faɗamata sirrin zuciyata”.
nan yayita surutansa daga bisani yaje yayi alwalar kwanciya bacci yashiga luntsimemen blanket ɗinsa yashiga duniyar tinani.

Fulani Zainaba kam suna rabuwa da F2 tayi part ɗinta cikin tashin hankali kamar anjehota haka tashiga ɗakinta kallonta Marwan da Maryam sukayi suka haɗa baki gurin cewa”Ummah lafiya muka ganki cikin tashin hankali ko wani abun ne yafarune?”.
“hmm babbanma wani abun kuwa banacemuku boka Matsatsaku yacemun wannan ɗan iskan yaron baze ƙarajin sha’awar zuwa ƙasar nanba “.
“eh “.
“toh gashi can a zeshiga ɓangaren munafukar tsohuwar nan ina ganin itace ta yimasa dole yadawo bara na kira Riƙayya ta temakeni tajemun gurin boka inyaso inta dawo na biyamata kuɗin aikin da za’ah yimata saboda boka yace muddum yadawo to wannan munafukar tsohuwar nan zata iyasawa a karya abinda nayimasa saboda boka yace a tsaye take”.
“aiko Ummah kiyimaza ki kirata setaɗan lallaɓa ta haɗa harda maganin daze jawo hankalin gimbiyata”.
“aiko yanzufa dan ɗazu Maimartaba yagama cemun nanda sati ɗaya zeyi murabus a naɗaka bazeyiwuba yazo da rana tsaka ya lalatamun budget ba wlh inyaso wannan me gaba ɗaya zan masa insa a kasheshi bara na kirata”.
“aiko hakan yayi Ummah Allah yabarmana uwarmu da tafi ta kowa”.
nanta shiga neman layin Ruƙayya seda tayi bugu biyu sannan Ruƙayya ta ɗauka tare da cewa”Hello waye”.
dariya Fulani Zainaba tayi tare da cewa”haba ta wajena nice ayi haƙuri dani wata matsalace ta tasomun nike neman temakonki”.
taɓe baki Ruƙayya tayi kamar tana kallon Fulani dan ita batayi mamakin kiranda Fulani tayimata ba saboda tasan rashin kunya da nuna son kai irinna Zainaba tace”ya akayi inajinki”.
“ina cikin matsala Ruƙayya yaronnan nefa yadawo kasarnan kuma kinsan boka yace muddum yadawo to komai ze iya faruwa shine nikeson ki lallaɓa kijemun gurin boka Matstsaku ki sanar dashi duk halin da nike ciki daga ƙarshe kicemasa so nike wannan karon yaron a kasheshi akuma yiwa wannan tsinanniyar tsuhuwar abunda har gwara ta gwammace ta mutu saboda wahalar da zata dinga ɗan ɗana”.
“toh shikenan da safen zanɗan lallaɓa naje”.
“toh godiya nike indai wannan aikin ya kammala zan baki kuɗi ayimiki aiki a ƙafartaki”.
wani takaicine yazowa Ruƙayya dakyar ta saita kanta tace”toh nagode”.
nansukayi sallama Fulani ta kashe cikin murna tace”nidai nasan aminiyata bazata taɓa yin zuciya daniba kome zanyimata da tanada zuciya da tini bamu kai iyanzuba saboda wannan ƴar barikin karyace batasan inda yikemata ciwoba shiyasa nike morarta san raina”.
“aiko gaskiya Ummah na yadda bata da zuciya kallifa irin abinda kikayimata a asibiti da watace da bazata ɗauki kirankiba kinga itako kina kira harta ɗauka”.
“eyi”.
nan suka dinga hirarsu ta yarda zasu ɓullowa lamarin zuwan F2.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button