HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Ɗaure ta fito da towel a ƙirjinta tsane ruwan jikinta tayi tashafa ɗan lotion ɗinta kaɗan sannan ta fesa turare ta saka wasu sleeping dress riga da wando ta haye gadonta taja blanket kunna data ɗinta tayi taga mutane duk sunmata magana mammayarmusu da amsa tayi sannan ta kashe data zata aje wayar kenan wayar tahau ringing ganin wata speacial number tayi tana yawo akan screen ɗin wayarta mamakine ya kamata tace”ni Hafsat waye yike kirana misalin sha ɗaya ko waye oho nidai bazan ɗaukaba haka kurum inje ƴan shan jinine”.
bata ɗaukaba har kiran ya tsinke ƙara shigowa kiran yayi nanma bata ɗaukaba se ana ukun sannan ta ɗauka cikin siririyar muryarta me daɗin sauraro tace”salamu Alaikum”.
jin muryarsa yasashi lokaci ɗaya yaji yashiga wani irin yanayi inda tindaga ƙafarsa har tsakiyar kansa yaji wani irin yarrrrr lumshe ido yayi yashiga duniyar tinani Hafsat ko jin anyi shiru yasata ƙara cewa”Salamu Alaikum waye anata sallama yayi shiru kowayema li’ilafi aniyarka ta bika inma ɗan shan jinine kuma ko litre ɗaya ka shamun ban yafeba”.
tana gama faɗar haka kittt ta kashe wayarta dariya sosai F2 yaci yace”wannan yarinyar akwai tsiwa”.
seda yayi me isarshi sannan yashiga galery ɗinsa yashiga ganin hotunanta a haka bacci yayi awon gaba dashi.

12:00pm
Zazzaune kowa yake a gurin walima Sheikh Abubakar nata wa’azi bayan angama Abbih ya anshi loudspeaker yace”Assalamu Alaikum dukkan yabo da godiya su ƙara tabbata ga fiyayyen hallita Annabi muhammad (s.a.w) Allah nagodemaka daka nunamun wannan rana ta walimar ganin ɗiyata data ɓace tin tana ƙarama segashi cikin ikon Allah anganta a inda ba’azataba inda cikin ƙudurar ubangiji ya haɗata da mutanen arziƙi suka riƙemun ita cikin mutunci daga ƙarshe suka auramata danda suka haifa cikin ikon Allah har Allah ya azurtasu da yara guda biyu mace da namiji Hafsat da Al’ameen cikin ikon Allah ,Allah ya haɗa auren Hafsat da Farouk ba kunji wani ikon Allah ba abinda zamucewa Allah se godiya a ƙarshe ina yima mijin Sa’adatu albishir da na naɗashi Galadima a wannan masarauta tamu me albarka da gida sannan da jari me tsoka itakuma mahaifyarsa Hajara anbata gida itama sannan da kuɗi masu tsoka nagode da abinda suka yiwa ɗiyata dukda basusan ko ita waceceba naji daɗi kwarai da gaske”.
fadawa ne suka haɗa baki gurin cewa”godiya yike babbar giwa Allah yaƙara ɗaukaka”.
tashi Bappah yayi yana kukan farinciki yana godiya bayan ankammala aka shiga ciye-ciye Iyah ba abinda take se kalle-kallen hanshaƙan masu hannu da shuni a zuciyarta tace”kai amma gaskiya aradun Allah jahilci beyiba inata yiwa yarinya me ƙashin arziƙi tsiyar rashin asali ashe itaceko keda asali wanda muko kama hanyarsu bamuyiba Allah na godemaka da bata faɗamusuba aida naji kunya gaskiya wannan yarinya da haƙuri take tamaida komai-bakomaibane”.
tana zancen zuci taji Hafsat nacewa”Iyah lafiya naga kinshiga duniyar tinani”.
“lafiya ƙlau ja’ira yaki nan nima inaso kiɗan fara koyamun karatu kona sallah intsira dashi dan banajin daɗin jahilcin da nike ciki tinkafin angon naki yazo ya tafi dake inɗan ƙaru”.
“toh shikenan Iyah bara a idarda sallah la’asar semuyi”.
“toh nagode Allah yayi albarka wai ina ƴar uwarki Furera ta shigene tin ɗazu rabonda naganta”.
“hmm Iyah tana waje tana zance da Yah Salman”.
cikin nishaɗi Iyah tace”badai Salmanu ɗan mijin Firddausi kike nifiba”.
tafaɗa tana kama baki dariya Hafsat tayi tace”eh shi Iyah tinda kukaje suka jone da ita”.
“a’ah to Allah ya tabbatar da alkhairi “.
“Ameeen Iyarmu bara nashiga cikin gida”.
“toh shikenan”.
nanta wuce Hajjo nata nunasu itada Al’ameen gun ƙawayenta har bayan la’asar sannan jama’ah sukayi sauƙi.

Yana idarda sallar Asuba yafita yashiga kewayen ganinsu Ammi suka fita zasu tafi yana ganin Ammi yashiga wayar ƙarya alamar daga Masallaci ya dawo murmushinsu na manya tayi tace”haba yaro kayi ka gama indai kan Hafsat ne kozanbaka ita seka yada wannan girman kan naka dan bazanbaka itaba ta daɗin rai”.
har zasu wuce yaƙarasa gurinta cikin girmamawa yace”Ammina barka da asuba”.
“barka Son ya kwanan baƙunta”.
“aiba baƙunta bane Ammi gidanmune harzaku tafi”.
yafaɗa yana waige-waigen ta inda zega Hafsat ƴar dariya Ammi tayi tace”eh har zamu tafi Son seka tawo”.
“toh Ammi sena tawo”.
“toh Son”.
nansuka tafi shikuma yakoma part ɗinsa cike da kewar Hafsat domin yanzu jiyike tarigada ta zamemasa jinin jikinsa jiyike inbata baze iya rayuwaba yanata tinanin inda ze ganta a haka har wani bacci yayi awon gaba dashi.

10:30am
ya fito yasha wanka kamar wanda zeje gasar kyau cikin tafiyarnan tasa ta ƙasaita ya fita yashiga mota drivernsa yakaisa Airport yashiga Jet ɗinsu suka nufi Adamawa suna isa yana shirin fita wayarshi tayi ƙara gani yayi sunan Adam murmushin gefan baki yayi tare da ɗagawa ba tare da yayi maganaba Adam ne yace”Bro ina ka kwanane ko a gidan Aunty Fido”.
“a’ah ina 9ja ana taron Ummita so nike a gama na dawo”.
“okay bro seka dawo take care”.
“thanks”.
nanya kashe ya sauka aka kaishi masarautar nanma yayita zuba ido ba Hafsat ba labarinta shida beson hayaniya hakanan ya zauna cikin mutane koze ganta amma shiru hankalinsa baƙaramun tashi yayiba lokaci ɗaya ya rame bashida abinda yikeso ya gani kamar Hafsat amma bata ba dalilinta ɓangaren Hafsat ko tanajin ance F2 ya iso duk inda tasan zasu haɗu ta dena bi ta dena fita daga bedroom ɗinta inwani abun zatayi sede tasa Fatimah tasaka ƴan aiki si yomata har taron ya watse yayi su Ummita suka tare a danƙareren mansion ɗinsu a cikin garin Adamawa F2 bega Hafsat ba kullum cikin damuwa dasu Ammi zasu tafima binsu yayi kozeganta bata ba alamarta tin yana iya ɓoye damuwarsa harya kasance se kaji yayi magana shi a tinaninsa a zuci yikeyi seka tambayesa ya haɗe rai yace bakomai duk iya dabarar dazeyiwa Fatimah ya gane Hafsat na nan yayi amma bega alamun tana nanba.

Bayan kwana biyu Ruƙayyace ke shigowa riƙeda ƴar jakarta tana ɗingisa ƙafa Fulani dake zaune tana danna wayace tace”a’ah aminiyata sannu da zuwa dama yanzu zankiraki inji yadda kukayi da boka ashe ƴar halak kina hanya sannunki da zuwa”.
zama Ruƙayya tayi tace”wash nagaji seda nayi kwana biyu yanamiki aiki sannan yace komai ya kammalu shiyasa zakiji inkin kira wayata bata shiga”.
“hakane kam dama inata tinanin lafiya najiki shiru to ayimun bayani danni so nike nanda gobe yaronnan ya wuce barzahu”.
dariya Ruƙayya tayi tace”waike da wuri haka to bara nayimiki jawabi wannan maganin yace kullum zaki dinga zubashi a kan gadon yaron dakuma na mahaifinsa harna tsawon kwana bakwai yace zakisha mamakin rana ta bakwan saboda a ranar ɗanki zezama sarki ya auri Hafsat sannan kuma a ranar Farouku ze mutu a ranar Maimartaba ze tsani gawarshi daga ƙarshe yadda beyiwa uwarshi sallah ba haka shima bazemasa”.
cikin farinciki Fulani tace”kace ranar akwai shan-shagali danni harna ƙagu naga ranar tazo naga ƙarahen Khadijat na huta suma sauran watsasu duniya zanyi suje can su ƙarata suyita watsewarsu”.
wani shu’umin murmushi Ruƙayya tayimata tare da miƙewa tana ɗingishi tace”nizan tafi ƙawata inda matsala ki kirani yace karfa ayi missing ɗin ko kwana ɗaya kullum zakije gadajensu ki yarfa da sabuwar tsintsiya ki dawo har kwana bakwai karki bari wani kuma ya ganki”.
“toh aminiyata godiya nike zan turomiki sa kuɗin nanda sati biyu”.
“toh shikenan nagode”.
nan Ruƙayya ta ɗingisa ta tafi tana dariya a zuciyata itakuma Fulani taje duk ta yayyafa musu sannan ta dawo tana dariyar jindaɗi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button