HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Tsalle Hafsat ta daka daga kan gadon da take saurin kallonta Fatimah tayi tare da cewa”lafiya Aunty”.
“lafiya ƙlau sis Iyatah yanzu tana sona tana ƙaunata”.
“bangane Iyarki ba aidama tana sonki ko kintaɓa ganin wanda kakanshi besonshi Aunty”.
“hmm bazaki ganeba Fatimah kawai yau kunyi waya da Yah Ameen ne?”.
“eh munyi yace lokacin ze shiga lecture”.
“ok bara inkirashi inyimasa albishir yau dole akwai party a gidannan”.
“hmmm yanzu dai Aunty kina shagalinki kalli kayan yanzu da kike sakawa”.
“eyi shan iska nikeyi wani abun kika gani kema waya hanaki sakewa kisaka abinda ranki yakeso ai ba waje kika fitaba”.
“hakane kam kinkira su Hajjo kuwa kin musu sannu da zuwa kuwa”.
“eh na musu hartama faɗamun a gidan Aunty Fido suka sauka”.
“eh hakane kam”.
nan Hafsat takira Ameen ta sanar dashi shima ba ƙaramin farinciki yayiba ranar Hafsat kamar ammata albishir haka ta wuni da farinciki.

Bayan an sallami Maryam sun koma gida Fulani Zainab tana bata abinci kenan wayarta tayi ƙara dubawa tayi taga sunan Ruƙayya na yawo akan screen ɗin wayar kallon Marwan tayi tare da cewa”kaga ƴar halak ɗaga kasamun a hansfree ƙila harta dawo”.
cikin zumuɗi yace”wlh kuwa kace nakusa zama ango bara insa”.
“eyi ai shiyasa nikeso ka kwantar da hankalinka”.
nanya ɗaga jin muryar wani namiji sukaji yace”Hajiya ke ƴar uwar Ruƙayya ce”.
“a’ah ƙawarta ce ya akayi”.
“taje unguwa ta dawo a hanyarta dawowa tasamu hatsarin mota yanzu haka tana asibitin F.M.F “.
“toh gamunan zuwa”.
nan ya kashe waya kallon Marwan Fulani tayi tare da cewa”kaji wata sabuwa kuma bara muje inji inta anso in ansa kawai saboda ai bani na ɗauramata cutar ba”.
“toh bara muje in rakaki”.
“toh taso kekuma Maryam kijiramu yanzu zamu dawo”.
nansuka tafi suna zuwa asibiti suka samu likita a Office suka zauna Doctor Fu’ad yace”sannunku da zuwa”.
“yauwa ina Ruƙayyan take”.
“muje ranki shidaɗe tana can ɗakin”.
“toh muje”.
nansuka tafi samun Ruƙayya sukayi tana jin jiki saboda yadda taji wawakeken rauni a ƙafarta ƙarasawa sukayi gurinta Fulani buɗar bakinta se cewa tayi”amma dai kin anso maganin daiko”.
wani baƙincikin Fulani ne ya turniƙe Ruƙayya a zuciyarta tace”wato matar nan ni zata nunawa rashin mutunci memakon taji yaya jikina a’ah ta maganin ɗanta takeyima ni kona mutu ko nayi rai ba damuwarta bane zan koyamata hankali wlh”.
a fili kuma tace”inafa naje bankaiga zuwaba wannan abun yafaru dani”.
“yanzu kenan ya kenan za’ayi ko so kike ɗana ya shiga duniya haba Ruƙayya”.
zuciya ce ta ciyo Ruƙayya suka shiga tsiya ba tare data faɗamata ta anshi maganinba harta kaisu ga gore-gore doctor Fu’ad ne yace”ranki shidaɗe kudena wannan maganar sansamu asha kan matsalar dake damun Ruƙayya za’ah yimata aiki na a ƙalla na 3million a ƙafa sannan ƙafarta zata dawo daidai inba hakaba ƙafar ruɓewa zatayi”.

Waro ido waje Fulani tayi tare da cewa”har million uku gaskiya abinda baze yiwuba dukiyata dan ƴaƴana nake tarata badan ƙadangarun barikiba bazan bayarba”.
Ruƙayya batayi mamakiba saboda tasan halin Fulani dasan kai tace”toh ko hakina da kikayimun alƙawari million ɗaya kibani dan Allah”.
wata uwar harara Fulani ta bankamata tace”an hanaki haƙƙin naki kiyi yadda zakiyi aini yanzu kingamun komai saboda bakida mamora kinzama gurguwa shikenan seki tsugunna guri ɗaya kafin lokacinki yayi”.
Fulani tafaɗa tana dariya nan ta wuce itada Marwan suka bar Ruƙayya na kuka sosai Ruƙayya tabama doctor Fu’ad tausayi yaƙarasa inda take yace”Hajiya ki dena kuka akwai wani abokina Farouk duk wata yana biyawa marasa lafiya ɗari a cikin asibitinnan zan mishi magana barama dai na kirasa na faɗamasa muji abinda zece”.
“toh nagode likita”.
nan doctor Fu’ad yayi dialing number F2 bugu ɗaya ya ɗauka hansfree yasaka dan Ruƙayya taji yace”F2 anyini lfy”.
“lafiya ƙlau akwai matsala ne a asibitin”.
“eh wlh dama wata mata za’ayiwa aiki a ƙalla za’ah kashe 3million shine nace bara in sanar dakai ayimata temakonnan da aka saba”.
“ok tom yanzu zan turamaka da 3million ayimata duk abinda ya dace Allah yabata lafiya”.
“ameen godiya take gata zata yimaka godiya”.
sosai hankalin Ruƙayya ya tashi a zuciyarta tace”Allahu sarki bawan Allah mu munmaku sharri ku kuna binmu da Alkhairi dolene nima na temakeka na fitar daku daga sharrin waccan tsinnaniyar matar mara imani da kanta kawai tasani da ƴaƴanta amma wannan karon zanyimata hankali duk sena lalata shirinta zatasan tayi da ƴar halak nicema ƙadangarun bariki”.
tana cikin zancen zucinnan taji doctor Fu’ad yace”gata”.
jitayi F2 yace”kyaleta kawai ni dan Allah nayi banason kowa yasani idan dame wata matsalar wani abun ka kirani se anjuma”.
nanya kashe godiya sosai Ruƙayya tayiwa doctor Fu’ad nanya tafi itakuma tashiga tinanin abinda zatayiwa Fulani.

6:00pm
Washe gari jirginsu Ummita ya sauka a ƙasa me tsarki motocin gidansu Aunty Fido ne suka kwashesu suka nufi Riyadh dasu inda Iyah ba abinda takeyi se aikin zuba ƙauyenci har suka isa gidan masu aikin gidan suka yimusu jagora gurin shiga main falon gidan ƙin ƙarasawa Iyah tayi ta kwarma ihu cewa take”aradu ku temako wannan abun ze faɗomun wayyo Allah”.
fifitowa masu aikin gidan sukayi sakamakon su Aunty Fido suna can cikin gidan ganin ƙaton kwan dake tsakiyar falon Iyah take kalla yasasu gane shi take tsoro babba cikin masu aikin ce tace”Hajiya ki wu ba abinda ze faɗomiki”.
“toh amma shi wannan abun tinjumeme meye amfaninshi ai wannan aradun Allah seya kashe mutum”.
tafaɗa tana mammatsawa “ba abinda zeyimiki Iyah”.
“toh amma wani yafara wucewa ingani inbe faɗomasa ba semu wuce”.
dariya duk sukayi babbar masu aikin ta wuce sannan Iyah tabari suka wuce suma amma tanata ɗari-ɗari har suka isa wani haɗaɗen falo wata me aiki tace”ku zauna anan bara in sanar dasu Hajiyar Babah ki kawo takalminki infitar dashi”.
daɗa maƙale takalmi Iyah tayi a hammata tace”keko baiwar Allah ina ruwanki da takalmina ne ko akanki yike haba tin ɗazu ina lura dake kiketa kallonshi in mayyace ke sede kici kanki kisha baƙin ruwa haka kurum”.
“ta haƙuri Babah”.
nanta wuce tana zuwa tasamu su Aunty Fido zaune suna hira da Hajjo tace”ranki shidaɗe sun iso suna falo na biyu”.
“ok gamuman zuwa akaimusu kayan motsa baki”.
“toh “.
nanta tafi aka cika gabansu Iyah da kaya abinka da ƙauyawa kaza kawai suka gane suka shiga ci bayan sun gama aka kwashe kwanukan sega su Aunty Fido sun shiga falon gaban Ummita ne ya yanke ya faɗi jin muryar Aunty fido da tayi.

Ƙarasawa sukayi suka zauna Ummita na ɗaga kai sukayi arba da Hajjo da Aunty Fido saurin miƙewa gabaki ɗaya sukayi su ukun yayinda Ummita tashiga nuna Hajjo yayinda takama kanta zatayi magana kenan ta yanke jiki ta faɗi!!!!!!

kar a gaji dani dan Allah inkin karanta ku tura zuwa wani group ɗin dukda kike ciki.

Votes and comments
Plz share to Others groups

_Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.✍️tanen Gwarz???? HASKEN RAYUWATA

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION

PAGE 4️⃣9️⃣➡️5️⃣0️⃣

        Saurin yin kanta sukayi gabaki ɗayansu Hajjo ce tayi ƙarfin halin cewa"Innalillahi wa'innah ilaihir raji'un Firddausi ɗakko faro a yayyafamata ɗiyatace Sa'adatu data ɓace ashe akwai ranar da idanuwana zasuganni gani ga Sa'adatu na yi sauri kar asamu matsala".

saurin kawo ruwan Aunty Fido tayi tare da cewa”Hajjo wacce Sa’adatu kike magana ne wai”.
“tamu man data ɓace ashe dama inada rabon sake haɗa ido da ɗiyata ban mutuba”.
Hajjo tana kuka tana magana firgigit Ummita ta tashi tare da cewa”Innalillahi wa’innah ilaihir raji’un”.
tana salati tana bin kowa na ɗakin da kallo rungume juna sukayi da Hajjo suka fashe da wani kuka me tsuma zuciyar me sauraro tausayi suka bama kowa na gurin Iyah ko cikinta dukya ɗuri ruwa ganin Ummita ta dawo cikin hayyacinta karta faɗama iyayenta cin mutuncin da tayimata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button