HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Masoyana dan Allah ku temaka kuyiwa ƙwnwata voting a gasar data fito book ɗinta me suna MAHAƘURCI (Mawadaci) Haseenan Masoya da Real eesha book ɗinta me suna WANNAN RAYUWAR.

Daga Alƙalamin ƴar Mutanen Gwarzo.✍️Mutanen Gw???? HASKEN RAYUWATA

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION

PAGE 3️⃣3️⃣➡️3️⃣4️⃣

     Fatimah ta faɗa tana dariya ɓangaren Hafsat ko ƙiftawa batayi shima kuma haka can zuciyar Hafsat tashiga cewa"jahila baƙauya mara ilimi mara wayewa ni bazan taɓa dawoba".

lokaci ɗaya taji wata irin tsanarsa ta mamayemata zuciya yayinda wani ƙarfi yazomata ta hankaɗashi tare da buga tsaki tace”niba irin ƴammatan daka saba lalatawa bace mara tarbiyya kawai”.
wani takaicine yazowa F2 lokaci ɗaya ya buɗe idanunsa da sukayi ja ya saukesu akan ɗan ƙaramin pinky lips ɗinta wani shu’umin murmushi ya saki tare da juyar da ita wajan bango binta ya riƙayi tana baya harta ƙure da bango bugun zuciyarta ne yaƙaru yayinda iskar hadarin ta shiga kaɗa dogon gashinta dayasha gyara bako ɗan kwali jin ta ƙure da bango yasa lokaci ɗaya wani tsoro ya dirarmata lokaci ɗaya kallon wani madubi tayi taga ɗan madaidaicin ƙirjinta ya buɗe kallon F2 tayi taga me yake kallo gani tayi saman ƙirjinta yake kalla wani tuƙuƙin baƙincikine ya tasomata tayimaza ta gyara rigar wani shu’umin murmushin gefan baki yayi yaƙarasa inda take yasaka hannu ya saƙalo ɗan ƙaramin ƙugunta ya haɗeta da jikinsa cikin sauri ya haɗe bakinsa da nata yashiga tsotsa kamar wanda yasamu lolipop seda yayi me isarsa sannan ya cire bakinsa anata
ba tare data tsaya ɗaukar niƙabinta ba ta luluɓa ɗankwalin abayar kotakan wasu turaruka batabiba ta ruga da gudu tace”Allah ya isa ancemaka ɗan iska kawai”.
ta tofar da yawu haɗe da fashewa da kuka ta fice F2 ko kamar wani gunkin da aka dasa haka yatsaya yayi ƙiƙam ko ƙifta ido bayayi harta ɓacema ganinsa.

Saɗaf-saɗaf Fatimah ta koma ta baya ta ɗibar musu wasu turarukan tabi bayanta mota samun Hafsat tayi ta goge hawayenta amma lulu eyes ɗinta se maiƙo suke alamun tayi kuka Fatimah yi tayi kamar bataga meya faru da itaba a rikice tace”Aunty meya sameki a idonki haka naga kamar kinyi kuka”.
kai hannu Hafsat tayi fuskarta ta share wasu kwalla data tahomata ta ƙaƙali murmushin dole tace”kwarone yafaɗamun idona shinefa suketa ruwa driver mutafi”.
“ayya yafito kwaron”.
“eh yafito”.
Fatimah takusa dariya amma seta make tace”Aunty ina turarukan namu”.
damm gaban Hafsat yabayar jitayi lokaci ɗaya yawun bakinta ya ƙafe tashiga tinani a zuciyarta tace”innalillahi wannan mara tarbiyyar yasa namanta da turarukan”.
a fili kuma rasa mezatace tayi murmushi Fatimah tayi ba tare data lura da itaba Hafsat ce can tace”wash wlh namanta ban ɗakkoba kuma harda wani turare haɗaɗe tsakiyarsa tedy bear”.
“to shikenan aiga wasu na ɗebomana”.
“toh shikenan”.
nan Hafsat tashiga tinano abunda yafaru itada F2.

Wani numfashi me zafi ya furzar haɗe da sakin wani tsaki yace”niko meke damuna haka kan wannan ƴar shilar yarinyar na wani tsaya harna zubar da girmana da class ɗina haka”.
yafaɗa tare da gyara rigarsa datayi squeezing ya saki tsaki tare da ƙara haɗe rai yafara tafiya ya shinshina rigar jikinsa yaji ƙanshin turaren jikinta wani killer smile yasaki ba tare daya shiryaba yajuya ya cigaba da tafiya yaji ya daki kwali ɗaga idon da zeyi idonsa ya sauka kan wannan turaren data ɗauka me guda biyu tsakiya teddy duƙawa yayi ya ɗauka haɗeda niƙabinta yana murmushi ya cigaba da tafiyarsa harya isa gurin 5DBC Ahmad ne ya kalleshi ya kalli turaren hannunsa yace”wow gaskiya wannan turaren yayi kyau sosai bara nima na ɗaukeshi nima domin na masoyane ni wlh ban lura dashiba kuma danaje zaɓomana”.
“wlh kuwa kasa a ɗakkomana nima zanyiwa Sarah kyautarshi”.
“toh”.
F2 ne a zuciyarsa yace”to ita wannan yarinyar ƴar mitsitsiyarta da ita me zatayi da wannan teddy bearn na masoya”.
wata zuciyar ce tabashi amsa da cewa”saurayinta zata bawa itama”.
yana wannan zancen yaji Habib na shirin tafiya tsintar kansa yayi da yin gyaran murya a daƙile yace”irin wa’innan gabaki ɗaya na gurinnan nakeso akwasomunsu”.
wani agent ɗin gurin ne yace”toh ranka shidaɗe”.
nansuka tafi kallon mamaki 5DBC sukabi F2 dashi yayinda Habib yace”oga mezakayi da turaren masoya ai wannan harkar semu”.
shiru yayi kamar bejisaba hakan yasa suka gane yanaso shiru sukayi nan aka kawo aka haɗa da nasu akayi balance aka saka musu a mota dawowa Agent ɗin gurin yayi tare da cewa”angama ranka shidaɗe”.
seda ya jima har mutumin ya manta sannan yace”ok yimun jagora gurin Manager “.
“toh ranka shidaɗe”.
nan yayi gaba F2 yabi bayansa suka hau sama suna zuwa suka shiga agents ɗin ya buɗemasa ya shiga shikuma ya tsaya cikin takun ƙasaita yaƙarasa gurin manager zama yayi tare da cewa”anyini lfy”.
“lafiya ƙlau sir har angama siyayyar ne”.
“eh mungama dama zancen wani turare zan maka magana mesuna LOVERS HAPPINESS“.
“ok sir sonshi kakeyine?”.
“eh daka yau ko nawane zanbiya banaso aƙara siyar dashi a mall ɗinna saboda latata tarbiyyar yara yake”.
Managern ne a zuciyarsa yace”wato sekai dakafi kowa tarbiyya kenan “.
a fili kuma se cewa yayi “to ranka shidaɗe angama”.
“turon account no ka banaso asamu matsala domin lalata tarbiyyar yara yake”.
“toh gatanan bara na karantomaka”.
nanya karantamasa nan take ya sakamasa kuɗi yayimasa sallama ya tafi.

Bewa kowa maganaba yashiga motar da sukazo ya kwantar da kansa tare da lumshe ido yayinda daya rife ido ba abinda yake gani se kyakyawar fuskarta Ahmad ne yace”wai yau meyake damun mutumin ne naga duk ranshi a ɓace bayan ba haka mukazo ba”.
“nima dai abinda zance kenan domin naga lokaci ɗaya reaction ɗinsa ya sauya tunda ya tafi ɓangaren turarukannan shikenan yaƙara shan mur”.
ba tare daya buɗe ido ba cikin muryar me nuni da surutunsu yana damunsa yace”kuna damunafa kuyi maganarku iku,iku kudena sakani a ɓata lokacin da kukeyi domin bazan gushe gurin sanar daku kudena ɓata lokacinku kan wata aba wai ita soyayya ai ɓata time ne”.
“ok “.
wayar Habib ce tayi ƙara ganin Salman ne yasashi cewa”Man harfa mun juya yanzu haka munkusa jidda”.
“ok toh shikenan nima ƙila na shigo UK ɗinnan muje club”.
“toh sekazo”.
nanya kashe kallonsa Habib yayi tare da cewa”yaufa My Only zamu domin shine a time table ɗinmu”.
“ok Allah yakaimu domin ni duk Club ɗin da muke zuwa nafisonshi “.
“ba dole kace hakaba tunda Only ɗinka nacan”.
“sosaima kuwa kasan kwana nake ina caccakar ƴar nan amma ko a jikinta “.
“kaji daɗinka nima inaso na haɗuda babe ɗinda bata gajiya da sex ina aikina”.
suka cigaba da hirarsu ko na faɗin irin yadda yake shagalinsa .

Tunda ya lumshe ido ba abunda yake gani se kyakyawar fuskar Hafsat da pinky lips ɗinta a zuciyarsa yace”meyasa dana rife ido ba abinda nake gani se wannan ƴar shilar yarinyar ne meyasa nayi kissing ɗinta toh?”.
wata zuciyar ce tace”saboda kana sonta”.
wata zuciyar ce tace”never ever Allah ya kyauta naso wannan ƴar ficiciyar yarinyar kawai dai na temaketane dan karta faɗi”.
“hakane kam”.
nanya dinga tsaki su Ahmad sunata mamakin meke damun F2 har suka hau flight suka tafi bewa kowa maganaba.

Suna isa gida personal maid ɗin gidan suka gaidasu sannan suka kwashi kayan da suka siya suka shiga dasu bin bayansu sukayi itada Fatimah suna shiga Aunty Fido tace”sannunku da zuwa ƴammatan Ammi har kun dawo”.
“wash Aunty yauwa sannu ya aiki”.
“lafiya ƙlau harma munkusa gamawa da Ashwariy saura kaɗan Hafsat”.
“masha Allah Aunty muma bara muje musa Albarka”.
Hafsat ta faɗa tare da cire naɗin abayar jikinta ta ɗaura ɗankwalin ta matsa kusa da Aunty Fido murmushi Fatimah keta zabgawa Aunty ta kalleta tace”lafiya kekuma kiketa murmushi kamar wata gonar auduga”.
saurin ƙiftawa Aunty Fido ido tayi tare da nunamata tayi shiru kar Hafsat ta gane zasuyi magana gyaɗa kai Aunty Fido tayi tare da nunamata au Hafsat ceta waiga ta kalli Fatimah tace”kekuma dariyar me kikeyi haka kamar wadda aka gwaji ƴar kwata”.
dariya Fatimah tayi tare da cewa”bakomai Aunty tinowa nayi da wani abu a 9ja “.
“tom ai shikenan”.
Hafsat tafaɗa tana shirin gifta Aunty Fido shinshine -shinahine Aunty Fido tashiga yi tare da kallonsu tace”kamar ƙanshin turaren Farouk nakeji”.
tafaɗa tare da kallonsu damm ƙirjin Hafsat ya buga lokaci ɗaya wani gumi yashiga ketomata a zuciyarta cewa take Allah ya temakeni karsu gane ninake ƙanshin turarensa”.
jitayi Fatimah tayi ƴar dariya tare da cewa”nidai bani bace banji kuma ƙanshinba Aunty “.
murya na rawa Hafsat tace”nima dai banjiba Aunty ƙila dai a cikin turarukan da muka siyone wani yake irin wannan ƙamshin”.
Abdallah dake shigowane yace”gaskiya a’ah nima tunda kuka shigo gidannan nakejin ƙanshin turarennan kuma wlh duk inda turarennan yafito na Hamma Farouk ne”.
“tab gaskiya kanada kwakwa to wannan bashi bane a ina zamu haɗu dashi ko Fatimah bare harmu shafi turarensa”.
ta nuna kamar bata tsarguba nanko a zuciyarta ba ƙaramin tsarguwa tayiba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button