HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Cikin takun nutsuwa ta k’arasa har gaban table d’insa zata duk’a kenan yace”haba My Wife to be d’ina ya zaki zauna a k’asa ga kujera bayan kinsan bazanji dad’in hakanba”.
yadda ya fad’ane yasa taji yabata kunya tayi k’asa da kanta tana murmushi zama tayi a kan kujerar daya jamata yakoma ya zauna ba tare da ta d’agoba tace”nagode Malam”.
“nidai gaskiya a canzamun suna banason wani Malam”.
yak’arasa maganarsa cikeda shagwab’a Kamar wani k’aramin yaro ware dara-daran idonta tayi tare da cewa”to wanne kakeso toh”.
“irin wanda na fad’amiki man nakeso”.
nanma yafad’a cikin shagwab’a a zuciyarta tace”ni Hafsat na shigesu dama haka Malam yake dama dan dai inajin kunya danasa masa Pure one”.
tana tsaka da zancen zuci taji yace”wow amma wannan sunan yayi my ???? sure d’ina thank you”.
jin abinda yace ba k’aramin kunya yabataba tayi k’asa da kanta ajemata leda yayi a kusa da ita yace”gashinan ba yawa”.
d’aga ido tayi da niyyar cewa a’ah suka had’a ido cikin shagwab’a yace”nidai Allah sekin amsa wlh”.
ganin ya rantse yasa ta amsa tare da cewa”nagode Allah yak’ara bud’i da d’aukaka”.
“Amin sauranki abu d’aya?”.
kallonshi tayi alamar mefa ganin kallon datayimasa ne yasashi cewa”bakice Allah yabani keba”.
saurin k’asa da kanta cikin kunya da k’asa da murya ta fad’a nan tayimasa sallama ta fita cikin nutsuwa inda ko wanne cikinsu keta shauk’i k’auna da begen d’an uwansa.

Tana fita ta taddasu Billy amsar ledar Zully tayi Billy tace”ammafa ba soyayyar datakai ta Uztazai dad’i wlh sun iya soyayya dana ga suna caccafkewar nan sena hasaso ni nida F2 a guarding Muna Shan love”.
“nima haka wlh Zully Allah ya tabbatarmana da wannan abu dai kedai kawai akwai Shan kallo”.
wata dariya Billy ta saki tare da cewa”Zully gafa su mutuniyar tamu nan an lab’e “.
kallon su Habibah da Jamila Zully tayi tare da cewa”Iska dai na wahalar dame kayan kara anji kunya dai mutum wataran seya jiyowa kansa abinda zuciyarsa zatai bunduga muga tame hassada”.

A harzik’e tayi kansu dak’yar Jamilah ta rik’eta tare da cewa”ya hak’uri Habibah karkuyi fad’a da wa’innan ‘yan tayin su rainaki su zubdarmiki da mutunci ana ganinki da mutunci yanzu zamu aiwatar da abinnnan na jiya kibar jahilan marasa tarbiyyar”.
maganganun Jamilah ne suka sakata jin dad’i ta tsaya tana wani shu’umin murmushi suko ganin an rik’eta yasa sukaita rashin kunyarsu har zak’ewa sukeyi.

Dafe k’irji Billy tayi tare da sauke numfashi tace”kai ammafa mun auna arzik’i wlh data dank’emu da munshiga uku domin wannan hannun nata me kama dana jaririn samudawa da k’ila sede a kwashemu wlh”.
“Wlh kuwa nima abinda naita tinani kenan da sede a tsincemu a gadon asibiti”.
dariya Hafsat tayi sosai tace “matsoratan banza kawai sarakan rashin kunya wai yau bazakuga mazajen naku bane”.
“meze hana yanzuma kuwa Allah yayimiki Albarka Ina system d’in taki muga”.
“Innalillahi wlh na mantata a gida”.
“amma baki ko kyautaba kinsan dai inason ganin my Habib d’ina dai”.
Hafsat data fad’i maganar jitayi kawai ta fito nanta shiga zancen zuci tace”ni Hafsat meke damuna niko da har nake maganar wa’innan arnan banzan wata zuciyar ce tace kika sani ko wani abun sukewa ‘yammata dansu mak’alemusu batasan sanda tace a’uzubillahi mina shad’anurrajim ba nafi k’arfinku insha Allahu”.
jitayi sun tab’ata kallonsu tayi tare da cewa”kazace a ciki dasu Irish da juices kuzo mu koma class yau kud’in break d’inmu ya huta”.
“wlh kuwa dama da system d’innan da Ina ganin F2 ina cin kazata abun zefi sweet”.
tsintar kanta tayi cikin jin wata fad’uwar gaba kama hanunta da sukaine hakan yasata sauke numfashi gaba sukai suka barta a baya tana tafiya Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki tana tinanin itako meyasa take jin fad’uwar gaba akan wannan mara tarbiyyar tana zuwa gurin dakalin shiga class d’insu ta tafi zuuuu ta fad’i da sauri su Billy suka juya me zasu gani Hafsat kwance kamar bata numfashi wata uwar k’ara suka kwalla Wanda hakan yajawo hankalin Malamai na fitowa daga meeting da sauri sukayi kanta M. Jalaludeen na k’arasawa idonsa ya rife besan sanda ya d’auketa Kamar wata baby ba ya nufi gurin motar makaranta cikin tashin hankali Malamai suka shiga suka nufi Genaral Hospital .

Billy na kuka juyawar nan da zatayi sukai Ido hud’uda!!!!!

Warning a gaskiya banajin dad’in rashin comments and votes d’inku in baya dad’i ku fad’amun sena dena typing d’insa domin baze yiwu in b’ata lokacina da lokacin karatuna kukuma kuk’iyin comments ba Dan Allah ku gyara inba hakaba daga wannan page din na dena wlh.

Masoyana a nunamun k’auna ta hanyar suburbudomin comments

Votes and Comments
Plz share

Daga Alk’alamin’yar mutanen Gwarzo ✍️nen Gwarzo*_ ✍️???? *HASKEN RAYUWATA*

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION

DUNIYAR LITTATAFAN HAUSA TV
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Subscribe and share

PAGE 1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣

     Habibah tana murmushin k'eta kallon Zully Billy tayi cikeda takaici tace"Habibah da Jamila ne Ina tinanin sukayiwa Sweetheart  wannan abunfa".

“Inko sune wlh dukda sunfi k’arfinmu semun fad’awa M. Jalaludeen “.
“wlh kuwa”.
duk jikinsu yayi mugun sanyi sunata hawaye.

Suna isa hospital aka d’aurata a gadon marasa lafiya aka nufi emergency room da ita M. Jalaludeen se kaiwa da komowa yakeyi cikeda tashin hankali sauran Malamai ma hakan take a b’angarensu ko cikin tashin hankali yake musamman ma shugaban makaranta sun dad’e suna bata temakon gaggawa kafin su fito gumi doctor yake sharcewa kafin yak’arasa inda suke sun k’arasa inda yake M. Jalaludeen cikin sanyin murya me nuna yana cikin tashin hankali yace”doctor meya sameta”.
dafa kafad’arsa doctor Abubakar yayi tare da cewa”abokina ku kwantar da hankalinku muje office”.
“Toh”.
nan suka rankaya suka nufi office d’insa.

Zama yayi tare da zare glass d’insa ya sauke numfashi tare da cewa”ku kwantar da hankalinku ba wani abu bane ya sameta sanadiyyar fad’uwar datayi yasa tasamu karaya a hannu muma yimata d’ori yanzu haka zaku iya ganinta inkunason ganinta”.
sauke numfashi kowa yayi a cikinsu M. Jalaludeen yace”munaso muganta”.
“toh zama ku iya tafiya da ita Amma a kula da ita gurin shan magunguna akai akai insha Allahu befi tayi sati biyuba “.
“toh mungode “.
nansuka biya kud’in magani suka biya d’akin suka tafi da ita seda suka biya ta makaranta aka d’aukarmata jakarta sannan suka nufi Rumada.

Suna isa suka sauka a motar suka k’arasa har rugarsu suna zuwa k’ofar gidansu suka sami su Furera da Haladu me shayi suna zance da sauran ‘ya’yan gidansu Hafsat ko dukda tana cikin zafin ciwon dake hannunta hakan be hanata jin kunyar M. Jalaludeen ba saboda ganin ko mitsi tayi se yace meyafaru sunzo wucewa tagabansu M. Jalaludeen yayimusu sallama ba Wanda ya amsa sema tsaki da Furera tayi tare da cewa”kace yau duk iskancin da ake zuwa anayi abun yak’ara girmama har anfara kawomana kwarata gida andaiyi asarar haihuwa wlh”.
saurin d’agowa M Jalaludeen yayi da niyyar magana suka had’a ido da Hafsat tace”bara nayiwa Bappana magana gasu can”.
“zaki iya kuwa”.
“eh”.
nan ta nufi gurin wata bishiya dake d’an nesa dasu tana k’arasawa tayi sallama tace”Bappa sannunku da hutawa Bappa kazo ga Malaman makarantarmu can sunzo”.
kallonta Bappa yayi tare da cewa”lafiya dai d’iyar Bappanta meyasameki naga idonki yayi ja”.
“bakomai Bappa”.
“toh muje ‘yar lelena”.
nansuka tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button