HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Iyah ko ba abinda take se sauri harta isa gidan Furera bakin ɗaukeda sallama tashiga surukar Furera ce dake zaune a tsakar gida tace”wa’alaiki salam hannunki da zuwa”.
“yauwa”.
iya tafaɗa tare da zama a tabarmar da surukar furera take tace”ina wuninmu Hajara”.
“lafiya ƙlau ya gajiyar biki”.
“lafiya ƙlau zuwa nayi naga amare”.
“amare ana zaune ƙalau kuwa”.
“ai haka ake…..”.
kasa ƙarasawa Iyah tayi sakamakon fitowa da Furera tayi daga ɗan zageyenta tanata kwara amai kamar zata amayar da ƴan hanjinta mamakine yakama su Iyah sesuka dake basu kawo komaiba nan mahaifiyar Haladu ta bata buta ta wanke bakinta tanata nishi taƙarasa tabarmar da Iyah take zaune dakyar ta zauna tanata nishi batakaiga ƙarasa zamaba wani aman yakuma tawowa nan tayitayi tsoro abun yabasu Iyah nanta wanke bakinta tazauna kusa dasu Iyah zuwa can se tsirtar da yawu seda tayi wajan sau uku Iyah ta ɗaura hannu aka tace”nashiga uku ni Sa’adatu mezan gani haka aradu ƙarya kikeyi Furera ki kwasomana abun kunya da tozarci a rugar nan ba ace ko sati ɗaya bakiyiba ciki yafito sekin faɗamana wanda yayimiki wannan abun bara inje in sanar da iyayenki domin baki isa kin tozartamun zuri’ah ba aradu”.
Iyah taƙarasa tare da fashewa da matsanancin kuka surukar Furera ce tayi tsalle ta dire tace”ai aradu baki isaba a gidan ɗan nawa tab dole yazo ya sakeki dan ba anan zaki haifomana ɗan shegeba da ba’asan wanne tambaɗaɗen bane yayimikiba”.
kuka Furera ta fashe dashi tare da cewa”waiku wayacemuku cikine aradu bashi bane”.
dakuwa Iyah tayimata tare da miƙewa tsaye tana hawayen takaici tace”inba ciki bane ubankine kajini da tambaɗaɗiyar yarinya “.
ta wuce ta tafi tana kuka yayinda surukar Furera tace”ai aradu dama kin tsaya kun tafi tare dan yana zuwa zata tawo taje can ta nemi uban cikinta tashi kibarmun nan kafin in kwaɗamiki mari”.
da sauri Furera ta tashi da niyyar tafi ɗan kewayen da aka yimata Innar Haladu tace”ina zaki dan ubanki aradu gidanku zaki tafi dan kinbar ƙara kwana a gidannan “.
nan takora Furera bako hijabi.

Iyah kona futa ba inda ta zame ko inaba se gidan Indo nanma sallama tayi mezata gani Indo mijinta na turota daga ɗaki yana cewa”aradu yau a gidanku zaki kwana bazan iya da ƙazantar nan taki da rashin iya abinciba jakar banza”.
yafaɗa tare da cankaɗata da sauri Iyah ta tare da cewa”lafiya Sa’eedu meyake faruwane haka”.
“ai Iyah aradu wannan yarinyar batada mutunci tunda aka kawota bata share ɗakintaba kayan jikintama bata cireba ɗaki duk tayi batsa-batsa dashi ko garken shanunmu yafishi nagarin gani ɗazu na yanka kaza nace ta gyaramun dana dawo sena tarar ta soyata bako wanki batare data dafaba ga ƙazanta ta tafi ko zata dawo seta iya aiki da tsafta”.
kama baki Iyah tayi tare da cewa”ke Indo meyasa bakya aiki kike ƙazanta”.
zumɓuro baki Indo tayi tare da cew”kajima Iyah nan bakece kike hanamu ko taɓa tsintsayaba Hafsatu keyi ai ban iya komai ba ni”.
cikeda rashin gaskiya da borin kunya ta fututuke tace”ni karkiyimun sharri sede in uwarki da bata gaji arziƙiba kayi haƙuri kaimun rai ta zauna a ɗakinta”.
waro ido waje yayi cikeda tsiwa yace”ki tafi da ita inta koya ta dawo aradu bazata ƙara kwananmu a gidaba keda kika koyamata sekije ku zauna”.
yaƙarasa kamar ze doki Iyah cikin masifa Iyah da daketa lalaɓashi ce tace”toh seme kajini da ɗan iskan yaro ko cemaka akayi muna neman kai da ɗiyar tamu kekuma wuce mutafi”.
“eh naji ɗin adai tafi”.
cikeda neman masifa irinta tsofaffi Iyah tana dungurinshi tace”kardai ka zageni ato dan aradu daseka gane kurenka”.
“eh dai naji adai tafin”.
cikin masifa Iyah tace”mutafi kaikuma zakazo bikone zakaga yadda zanyi dakaine aradu ke kuma wuce mutafi nasan wannan duk aikin wannan sheɗaniyar ne zanyi maganinta wlh sena cimata mutumci”.
nan suka tafi tanata masifa wai ita ala dole Ummita ce tayomusu jifa.

HAFSAT POV

Zaune Hafsat take itada Fatimah suna hira tace”au namanta yaufa su Billy zasuzo kizo muje mu sanarwa da sarkin ƙofa a buɗemusu insunzo”.
“kai amma Aunty kikasa sanarmana asan yadda za’ah tarbesu amma shine kikayi shiru da bakinki”.
hararta Hafsat tayi tare da cewa”ƴar rainin sense nafacemiki namanta”.
“sorry Aunty to bara naje nasanar da Ammi sannan nasa kuyanga tafaɗama sarkin ƙofa zuwansu”.
“a’ah kibari muje inaso naga yanayin gidan nan “.
“toh taso muje”.
“toh”.
nan Hafsat tayafa mayafin abayarta yayinda dogon gashinta ya zubo gadon bayanta suka fita falo samunsu Ammi sukayi da Hajjo da Jakadiya a duƙe da alama magana sukeyi shiru sukayi ƙarasawa sukayi Fatimah tace”Ammi ƙawayen Aunty zasuzo yau shine zamuje mu sanarwa da sarkin ƙofa”.
“toh Allah yakawosu lafiya memakon kusa kuyangi su sanar seku tafi dakanku”.
“itace tace tanaso muje tamaga gidannan”.
“wai haka daughter”.
“eh Ammi”.
“toh sekun dawo kuyi sauri dai karku daɗe”.
“toh”.
nansuka tafi suna ƴar hirarsu.

Sun dawo kenan Hafsat tace”muje mu gaida Ummah “.
“toh gaskiya Aunty kina bani mamaki wlh kinmanta da mutuniyarki ta jiya kenan”.
“kidena haka kinji ƴar ƙanwata insha Allahu itama zata shiryu “.
“Allah yasa”.
“Ameen”.
nan suka ƙarasa part ɗin gaidasu kuyangin dakeyiwa Fulani tausa sukayi suka fita murmushinta ta faɗaɗa tare da cewa”a’ah kace ɗiyata ce sannu da zuwa”.
“yauwa Ummah inayini”.
murmushi tayi tare da cewa”lafiya ƙlau daughter keeeh kirawomun Maryam”.
sosai mamakin yadda suke kyarar kuyanginsu yakeba Hafsat amma seta make kuyangar jiki na rawa tace”toh ranki shidaɗe”.
ta wuce cikin sauri kallon hanyar kicin Ummah tayi cikin muryar ƴan duniya tace”senace akawomusu abinsha sannan zaku kawo kenan”.
“haɗowa muke ranki shidaɗe”.
kallonsu Hafsat Ummah tayi tare da cewa”kuyi haƙuri daughter har yanzu ba’ah kawomuku abinshaba basuda mutunci kuyanginnan”.
“bakomai Ummah”.
nan aka kawomusu aka ajemusu Ummah tace “kuci daughter bara ina zuwa”.
“toh”.
nanta tafi har Hafsat sun ɗauki wani cake zasu ci wata kuyanga tayi gyaran murya kallonta sukayi gabaki ɗayansu girgizamusu kai tayi alamar karsuci mayarwa sukayi suka aje suka miƙe sega Ummah tafito tare da cewa”lafiya daughter Auta yanaga bakuciba kun miƙe ko kaɗan kuci”.
“Ammi ce takiramu wai ƙawayen Aunty sunzo”.
“toh kuɗanci ko kaɗan ne”.
“a’ah Ummah “.
“a’ah dole kuci bara a biku dashi ke zoki ɗaukarmusu”.
“toh Ummah angode bara muje”.
“bakomai daughter ai keɗin ɗiyatace Maryam ɗinma wanka take inta gama zatazo”.
“toh setazo”.
nantasaka aka tafi kaimusu sannan suma suka fara tafiya sunzo fita Hafsat tayi karo da Marwan saurin baya tayi zata faɗi yakai hannu da niyyar tareta tayi sauri ta matsa sanadin haka wayarsa tafaɗi da jiki na rawa Hafsat takai hannu da niyyar ɗakkomasa tare da cewa”kayi haƙuri ga wayar”.
shiko yashagala da kallonta yaji taƙara cewa”ga wayar Marwan”.
“toh”.
garin ansa yana sani yahaɗa da hannunta takaicine yakama Hafsat ta miƙamasa suka wuce suka tafi yanacan ya lumshe ido bemasan sun tafiba seji yayi Ummah tace”to sarkin soyayya yaudai angama domin yau yarinyar nan indai taci abincin can tazama taka ka kwantar da hankalinka”.
“wow Ummah dagaske kace nakusa kwasar gara domin bakiji taushin hannunta ba wayyo Allah na harna hasaso nafara harka”.
dariya Fulani tayi tare da cewa”ƙaniyarka mara kunya”.
ta wuce cikin jindaɗi shiko se murna yake.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button