HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Haɗuwa sukayi da Aunty Fido tana magana da Ammi a zaune a falo ganin Fatimah cikin tashin hankali yasata cewa”lafiya Fatimah meyake faruwa”.
“Aunty Fido gaskiya ba lafiyaba Aunty Hafsat keta kuka wai gida zata koma”.
“innalillahi ko wani abu kikayimata”.
“wlh a’ah hasalima lokacin dana tashi na tarat bata ɗakin har nayi wanka na shirya nashiga toilet nayo fitsari ina fitowa naganta tana haɗa kaya tana kuka”.
“toh tafi gani nan zuwa”.
“toh”.
nanta tafi Aunty Fido tace”Ammi bara naje gurin ƴar shagwaɓarki na lallasheta “.
“toh idan kinje ki haɗani da ita”.
“toh”.
nanta tafi samunta sukayi harta gama haɗa kayanta tanata kuka ƙarasawa gurinta Aunty Fido tayi ta rungumeta tace”daughter ko wanine yayimiki wani abun ki faɗamun naci ubansa kinji”.
“ba wanda yayimun komai Aunty nidai gida nakeson naje naga Ammina”.
murmushi Aunty Fido tayi tare da cewa”kiyi haƙuri ai nanma gidane”.
nandai ta kafe tanata kuka kiran Ammi Aunty Fido tayi tare da cewa”Ammi fa yau ɗiyarki rigima takeji tunɗazu take aikin kuka nace me akaimata tace bakomai itadai gurinki zata”.
murmushin jindaɗi Ammi tayi tace”sani a hansfree nayimata magana”.
“toh”.
nanta saka Ammice tace”Hafsat ɗina ki kwantar da hankalinki kinji zanzo naganki nima ina kewarki kinji ɗiyata”.
“toh Ammi yaushe to zakizo”.
murmushi tayi tace”indai kika kwantar da hankalinki zan iya zuwa a kowanne lokaci sannanma ai kun kusa tafiya U.K jarabawarku takusa fitowa”.
“toh zan kwantar da hankalina Ammi”.
“hmm yauwa Hafsat ɗina good girl kingafa banason ƙanwarki ta rainaki intaga kina kuka ki share hawayenki”.
“toh Ammi”.
nanta share sannan ta cire Ammi daga hansfree suka ɗanyi hira har seda taɗan saki ranta sannan sukayi sallama nan Fatimah tayita yimata dariya sannan ta shiryamata kayanta Aunty Fido tace”toh ku taso mutafi muci abinci”.
“toh Aunty “.
nan tayi gaba suka bita a baya sukaje suka zauna akan dining samun Abdallah sukayi yanaci Aunty Fido ranar da kanta tayi serving ɗinsu amma duk hankalin Hafsat a tashe yake haka ta daure tashiga tura doyar tanacinta kamar magani.

Sakkowa yayi cikin shigar nan tashi ta ƴan iska goshinsa yasha plaster yana kallonta dake itace a saitin stairs ɗin da yake sakkowa harya ƙarasa gurin dining ɗin kallonsa Aunty Fido tayi taga plaster cikin firgici tace”Salman meyasami goshinka naga plaster”.
haɗa ido sukayi da Hafsat ta ɗauke kanta shafa gurin yayi tare da yin murmushi yace”karki damu Aunty ɗazune ina wanka santsi ya kwasheni na biye da tiles ɗin toilet shine naɗan wanke gurin”.
“ok to kariƙa kula Son kaji”.
“toh Aunty”.
nan Abdallah yayimasa sannu sannan yayimusu sallama ya tafi school yanada class 8-10 bayan ya tafi Aunty tayi serving ɗin Salman shima nan yashiga cin abinci yana kallon Hafsat itako a zuciyarta tace”gaskiya wannan ba ƙaramin ɗan iska bane wato bigewa ma yayi hmm dole na tashi tsaye inba hakaba wannan seya kaini ya baroni”.
tana cikin maganar zuci taji yace”Hafsat bako gaisuwa”.
murmushi ta ƙirƙiro tace”au Yah Salman antashi lfy”.
“lafiya ƙlau ya gajiyar aiki “.
“lafiya ƙalau”.
nan suka gama aka kwashe kayan suka tafi falo harda Aunty sunata hira yayinda Hafsat kuma duk a cikin damuwa take saboda yanzu ita Salman tsoroma yake bata.

IYAS POV

Indo saboda tsabar jindaɗin harka bama susan ana asuba seda kowanne cikinsu yayi releasing wajan uku sannan sukaji sanyin asuba na shigarsu dakyar Indo tace”gaskiya aradu jinake kamar karka dena abun akwaishi da daɗi”.
“aikuwa ni aradu banma ƙoshiba saboda keɗin akwaiki da daɗi yanzu dai yimaza ki lallaɓa ki ɗakko kayanki mutafi kafin wannan tsohuwar ta tashi nasan yanzu gab take da tashi kartazo tacimun mutunci”.
“aradu kuwa dan kasan tana tashi zata fara yayyafamana ruwan bala’i”.
Iyah dake jikin murfin ƙofa taji duk abinda sukace ta girgiza kai tayi sauri ta kwanta akan gadonta nan Indo ta wuce saɗaf-saɗaf tashiga ɗakin Iyah ta ɗauki ƴar bakkonta ta juya ta wuce har gadon Iyah ta buɗe abun luluɓar Iyah tace”sede kitashi kiga bani aradu haka kurum fitinanniyar tsohuwa ki hanani rawar gaban hantsi nida mijina ki hanamu jin daɗi da cin duniya da tsinke kinyi kaɗan”.
ta mayar da abun rufar ta rifeta tayi tsaki ta juya harta fara tafiya Iyah taja hannunta tare da cewa”ke ina zaki mara zuciya”.
“gidan mijina mana”.
“saboda rashin zuciya”.
“aiba rashin zuciya bane idan na zauna anan dawa zanyi rayuwar auren Iyah”.
“innalillahi Indo wato ni kike faɗawa haka aradu kije gaki ga namiji nan ya gama kwaƙuleki tass muna nan zamujiku a rana”.
“eh najiɗin kema dakece kikejin irin daɗin da akeji da tini kinkoma amma saboda bakyasona daidai da rana ɗaya bakicemun na komaba shine yanzu zaki wanice na zauna tab Allah ya kyauta”.
“wuce kitafi zakizo hannune badai ni kikayiwa rashin mutunciba anamiki gata kinamun rashin kunya kitafi”.
“aikuwa dai ko bakiceba”.
nanta wuce fuuu sosai ran Iyah ya ɓaci dakyar ta haɗiye ƙullutun daya tsayamata ta wuce ta ɗaura alwala ta tada sallah.

10:30am
Bappa da Amin ke duduba wani ɗan madaidaicin gida me haɗeda shago a ƙofar gida wani mutumine ya sauka napep ya ƙarasa gurinsu nan suka gaisa bayan sun gama gaisawa mutumin yace”toh ya kuka gani yayimuku koko yaya”.
“yayi Malam bamu takardar gida mubaka kuɗinka”.
“toh”.
nan Bappah yabashi kuɗin gidan shikuma yabasu takardu da mukullin gida suka shiga suka duduba nan Amin yace”Bappah bara naje kantinsu wani abokina na siyo fenti komu semuyiwa gidan”.
“toh shikenan ni bara nashiga daga ciki kayi sauri dan a yau daddare nakeson mutare kaga se asa su Isah islamiyyarsu Hafsat”.
“toh aiko hakan yayi”.
nan Bappah ya shige gidan shikuma ya tafi siyo fentin.

Be wani jimaba ya dawo nan suka haɗuda Bappah suka fente gidan tsaf sannan suka tafi gida Bappah be zarce ko inaba se ɗakin Iyah samunta yayi tana ɓarar gyaɗa zama yayi kusa da ita shima yasa hannu ya ɗauki gyaɗa yashiga tayata haɗe da cewa”Iyah ta sannu da aiki “.
“yauwa Iro lafiya naganka cikin farinciki haka”.
murmushi Bappah yayi a zuciyarsa yace”gaskiya in nafaɗama Iyah gaskiyar al’amari zata kwaɓemun to yanzu ni ya zance wata zuciyarce tace to kacemata me gidan da kake gadine ya siyamaka gida a Gwarzo yakuma baka jari”.
jin wannan shawar da zuciyarsa tabasa yasashi cewa”Iyah dama wani abun farincikine ya samemu”.
washe baki Iyah tayi tare da cewa”yika faɗamun inajinka”.
“toh Iyah ina fitar nan da kikaga nayi ɗazu to me gidan da nikeyiwa gadine ya kirani Gwarzo wai yazo danaje muka gaisa seya bani wannan mukullin na gida wai ya siyamun gida”.
“wayyo gaskiya naji daɗi sosai na tayaka murna”.
“nagode Iyah seki shirya kayanki mukoma dan yau nikeson mu koma”.
waro ido waje Iyah tayi tare da cewa”aradu ba inda zanje tin iyaye da kakannina ba inda sukaje nima kuma ba inda zan tafi wata uwa duniya can kaidai ka tafi”.
wani sanyine ya luluɓe Bappah amma seya nuna kamar beji daɗiba yace”haba Iyah da kinzo mun koma tare na riƙa ganinki”.
“a’ah nifa ba inda zanje abinda dai zancemaka ka kula sosai da wannan tsinanniyar matar taka dan karta riƙa yimaka ƴan sace-sace kuma ka sanar da maƙota su kula da agwaginsu dan karsuji wuff ka kula dasu Furera sosai suma”.
abinda Iyah tafaɗa Bappah dakyar ya maida dariyar data tahomasa yace”to Iyah zanyi insha Allahu”.
“yauwa Allah yayimaka Albarka jeka ku shirya kar dare yayimuku”.
“ameen Iyah”.
nanya tafi yasanar da Ummita shiryamusu ƴan kayansu suka tafi har Furera.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button