HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Suna zuwa Ummita ta share gidan Furera na hakimce Ummita ta ƙintsa komai ta shigarmusu da kayansu sega Aminu ya dawo da katifu irin na ƴan boarding school kowa da tasa nan Ummita ta kintsa komai tsaf inda Furera se harare-harare taketayi.

Da asubar fari Fulani ta tashi ta nufi ɓangarenta tana shiga ko sallah batayiba tayi dialing no Ruƙayya seda ta kira sau uku sannan ta ɗaga cikin muryar bacci tace”nashiga uku ni Ruƙayya ina cikin baccina me daɗi kin wanizo kin ɓatawa mutane lafiya?”.
“haba Ruƙayya ya zakiyimun haka bayan kinsan maganar da mukayi dake”.
tashi Ruƙayya tayi zaune tare da cewa”au wlh namanta to bara naje yanzu kuwa”.
“yauwa ngd”.
nanta kashe wayar ta koma ta kwanta ba tare da tayi sallah ba.

Zaune take a gaban boka Matsatsatsako ta warwaremasa komai dariya yayi lokaci ɗaya ya haɗe rai lokaci ɗaya yace”aiko gwara da kikazo da wuri da tini ina ƙona wannan abun na hannuna mutuwa zatayi”.
dafe ƙirji Ruƙayya tayi tare da cewa”to yanzu boka meye abunyi kenan”.
“abunyi ɗayane shine makarin abun karta ƙara bari mijinta ya saduda ita na tsawon sati guda sannan a ranar sati gudan tazo nafara saduwa da ita zansaka mata maganine a gabanta wanda ba wani ɗan iska da ya isa ya jefeta domin gidannan nasu akwai maƙiya sosai sannan karta bari asamu wani akasi akan wannan inko tabari to ba makawa seta samu matsala domin ni daka wannan bani da maganin temakonta”.
“toh boka hakanma mungode sosai ga wannan”.
ta ajemasa kuɗi ɗauka yayi tare da cewa”mushiga daga ciki to”.
“toh kamar kasan nima abinda zance kenan”.
nan suka shige sun daɗe sannan suka fito ta gyara ɗaurin zaninta ta tafi bata zame ko inaba se gidan Fulani ta warwaremata komai dafe ƙirji Fulani tayi tace”aiko Allah ya temakeni aiko wancan tsinanne ko yana tsafi da bahaguwar jaɓa be isa nabarshi yayiba wlh”.
“yadaifimiki infa kinason rayuwarki”.
“kemadai kinsanfa waceceni ai wlh yayi kaɗan daka yauma zan nunamasa nafara Al’ada”.
“nagode haka nakesonki”.
nan sukaita hirarsu suna tafawa.

SAUDI ARABIA
Fitowa sukayi cikin ado ko wacce se baza ƙamshi take Aunty Fido dake zaune tana hangosu tace”wow ƴammatan Ammi kunyi kyau sosai irin wannan baƙaƙen dogayen riguna haka karfa ku saje da larabawa a gurin shopping ɗinfa”.
“kinji Aunty wai karmu saje da larabawa sede Aunty aini tafini haske”.
“hakane amma bakuga yadda kukayi kyauba wlh ɗiyar Ammi kinyi kyau amma ina niƙabin da Ammi tace zaki riƙa sakawa”.
“nagode Aunty au wlh namanta bara na ɗakko nasaka”.
“toh “.
nanta ta koma itakuma Fatimah ta isa gurin Aunty bata jimaba ta fito sanye da niƙab Aunty Fido da Fatimah ne suka haɗa baki gurin cewa”wow masha Allah kinga yadda kikayi kyau kuwa dukda niƙab ne a jikinki”.
“nagode “.
“kuzo kuyikhtafi karku daɗe kunga yanzu aiki zanfara yau su Anun zasu dawo da Abbansu daga Malaysia”.
“toh insha Allahu”.
nanta basu Atm ɗinta ta rakasu har gaban mota suka shiga driver yajasu.

Basu zame ko inaba se wani katafaren mall haɗaɗe parking sukayi gurin adana motoci sannan drivern ya zagaya ya buɗemusu fitowa kowacce cikinsu tayi cikeda jan class suka fita suka shiga mall ɗin inka gansu zaka ɗauka twins ne saboda abinda ya banbantasu kawai niƙab se haske nan suka shiga sayayyarsu hankali kwance sun ɗauki wata doguwar riga Fatimah tace”wow gaskiya mu ɗauki wannanma zata yimana kyau sosai”.
“toh mu ɗauka amma ni a ganina muƙara da riga da wando seyafimana”.
“hakane to muƙara dasu ɗin”.
nan suka zuba a kwando suka cigaba ji sukayi jiniyata kauraye garin kallon Fatimah Hafsat tayi tace”sis wannan jiniyarfa waye wannan ya cikama mutane gari haka”.
“oho Aunty amma baya wuce wannan yaron na babban sarki hatsabibi domin shine yake hakan”.
zatayi magana sukaji wasu ƴammata nacewa”wow yau ashe munada rabon ganin F2 shida Abdul’aziz”.
“nifa na ƙagu nagansu domin banida wani masoyi da nake ƙauna kamar F2 yau kota halin ƙaƙa sena faɗamasa shiyasama na shiryo da wuri”.

Hafsat ce taji zuciyarta tayimata zafi jitake kamar ta caka musu wuƙa saboda jin maganganun wa’innan ƴammatan tace”Fatimah aimun gama siyayyarmu aiko?”.
“a’ah Aunty saura turaruka amma mu fara kai wa’innan afara yin balance semu zaɓo turarukan”.
“toh “.
nansuka tafi suka bayar suka juya yayinda Hafsat a zuciyarta tace”to waini meye yasa nakejin haushin wa’incan bayan niba sonshi nakeba”.
wata zuciyar ce tace”to ke inbanda abinki ina ruwanki ko kema sonshi kikeyi?”.
saurin girgiza kai tayi ba tare da tasan maganar a fili take yintaba tace”Allah ya tsari gatari da saran shuka”.
jitayi Fatimah tace”lafiya Aunty shukar me kike cewa”.
se lokacin Hafsat tasan a fili ta faɗa sauri wagarar da zancen tayi tace”sis muyi mu ƙarasa kije can ki zaɓowa Aunty nikuma bara naje can na zaɓomana”.
“toh kinga kuma hakan yayi musamman ma tunda akwai hanyar da zamu haɗe ma haɗu kawai a tsakiyar gurin”.
“toh muyi-muyi saboda kinga anfara iska “.
“toh”.
nan Hafsat tabi ta hanyar dama Fatimah tayi ta hagu.

Duba wani turare tayi ta saka a ɗan ƙaramin basket ɗin dake hannunta tacigaba da zaɓa ta ɗauki wani turare hadari yafara tasowa yayinda iska ke kaɗamata rigarta sakawa tayi ta juya ta ɗauki wani desingner ɗin turare me turare biyu tsakiyarsu kuma tedy bear ne fari tas dashi tsakiyarsa kuma zanen heart red baƙaramin kyau yayiba tajuya zata saka kenan taji haɗaɗen ƙamshi wanda bata taɓa jin irinsa a jikin wani mutumba jitayi tayi karu turarukan dake basket ɗinta suka zube ba tare data ɗaga ido taga wayeba ta tafi da niyyar kwashe turarukan taji rigarta ta harɗe ta tafi luuuu rife idonta tayi dan tarigada ta sadaƙar ba zato tajita a jikin mutum yayinda niƙab ɗin dake fuskarta ya yaye ɗankwalin kanta ya zame a hankali tashiga buɗe ido inda tasaukesu a haɗaɗiyar fuskar F2 shima ɗin sauke sexy eyes ɗinsa yayi akan haɗaɗiyar fuskarta kallon juna suka shigayi Hafsat damm zuciyarta tabada a zuciyarta tace”tabɗi gaskiya mutuminnan a hoto ana ragemasa kyau ni banga kamarsu da Abdallah ba sede in ta jini amma wama ze haɗa gaskiya ya haɗu ƙarshe ne”.
tana wannan zancen taji dogon gashinta ya rifemata fuska sanadiyyar iskar da akeyi ba zato taji lallausan hannunsa akan fuskarta ya gyaramata gashin haɗe da ƙuramata ido ya saki wani murmushin gefan baki itama anata ɓangaren jitayi ta mayarmasa da martanin murmushin da yayimata yayinda beauty point ɗinta suka lotsa ba zato taji yaƙara haɗeta da faffaɗan ƙirjinsa yayinda ƙirjunsu ya haɗe guri guda sukashiga kallon juna ko ƙiftawa basayi ko wannensu ya lula duniyar tinani.

Fatimah tazo tsakiyar gurin inda sukayi zasu haɗu ɗaga idon da zatayi tayi arangama dasu Hafsat da suka lula wata duniyar murmushi ta saki tare da cewa”bara nayimuku video da hotuna”.
ta fito da wayarta ta raɓe gefe inda bazasu lura da itaba tashiga ɗaukarsu gani tayi gashin Hafsat yaƙara rifemata fuska yakai hannunsa ya gyaramata murmushin jindaɗi tayi tace”yayi romeo da juliet kuna shagalinku yau su Aunty da shan kallo kenan”.!!!!!

Tallah! Tallah!! Tallah!!!
Ina kuke masoyana na haƙiƙa kufito kunu namin ƙauna ta hanyar siyen book ɗina me suna BAR RAINA ALLURA(Itama ƙarfe ce) ta wannan account no 2411022356 Aisha Ibrahim Zenith Bank aiko da shedar biyanka ta wannan no 08108362334 ko katin Mtn or Airtel ta wannan no 08108362334 sena jiku.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button