HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Dariya Fatimah tayi tare da cewa”toh Aunty amma ni banga aibun towel ɗinnanba zakima saba domin idan nafara karantomiki irin dokokin mijinki zakisha mamaki”.
“nidai naji ɗakkomin”.
nanta ɗakkomata zabgegen hijab tasa ta nunamata toilet da yadda ake amfani da komai abinka dame kwakwalwa nanda nan ta ɗauke ta fito tabarta tayi wanka bata wani jimaba tafito samun wata haɗaɗiyar doguwar riga tayi baƙa da adon stone golden tayi me shegen kyau da adon stone golden a aje akan bed gefe guda kuma breziya ce golden da pant golden suma a aje ƙarasawa tayi gurin kujerar data zauna ɗazu tayi tana tinanin ina Fatimah tashigane tana wannan tinanin taji an turo ƙofa kallon ƙofar tayi ganin me babban ɗaki tayi cikin shiga ta alfarma ba irin shigar ɗazu da suka dawo da itaba tana ganinta ta miƙe tare da cewa”sannu da zuwa Hajiya”.
ƙarasawa gurinta me babban ɗaki tayi tare da cewa”yauwa Hafsat ya kika zauna anan taso maza kishirya kinji daughter”.
“toh”.
nanta kama hannunta suka isa gaban tanƙamemen mirrior ɗin ɗakin tace”ga mayuka nan kishafa kinji sannan kuma wannan kunyar tawa da kikeji banasonta inaso ki ɗaukeni tamkar Ummita duk abinda kikeso ki tambayeni kanki tsaye kinji ɗiyata koriƙa kirana da Ammi kamar yadda Fatimah take faɗa kinji “.
“toh Ammi insha Allahu nagode”.
“bakomai yimaza ki shirya ga kayanki nan akan gado ina jiranki a falo bayan magriba zamuje dake fada kikai gaisuwa”.
“toh angode”.
“ba godiya a tsakaninmu”.
nan Ammi ta fita tabar Hafsat wasu hawaye taji sun zubomata tace”Allah sarki Ummitana da Bappana ko suna wanne hali oho”.
jitayi ance”lafiya Aunty kike hawaye”.
saurin share hawayenta tayi tare da cewa”bakomai Fatimah ina kikajene na fito bangankiba”.
“Yayah Abdullah ne ya kirani indubamasa takarda a ɗakinsa na duba banganiba yace gobe yana hanya in gaishemishi dake”.
“toh ina amsawa kiyi shafarki mana Aunty”.
“toh”.
nanta ɗauki wani lotion tafara shafawa ƙarasawa Fatimah tayi nunamata sauran lotion ɗin nanta shafa tashafama gashin kanta ta tajesa nan ya kwanta yayi luf kamar wata ba indiya nanta shafa powder kaɗan tasaka lips stick ta gyara girarta lokaci ɗaya taga tayi wani sihirtaccen kyau Fatimah ce tace”kinyi kyau Aunty nima bari inyi wankana”.
nanta shige toilet ƙarasawa gurin kayan Hafsat tayi ta ɗauki pant tasaka ta ɗauki bra tasaka jinta tayi duk a matse amma haka ta daure ta zura doguwar rigar ta ɗaure gashinta da baƙin ribom ta yafama mayafin rigar ta ƙarasa gaban mirrior ganinta tayi kamar wata balarabiya nanta fesa perfumes kalakala ta koma gefan gado ta zauna tana wasa da hannunta.

Fatimah ce tafito itamah shafar tayi ta gyara fashinta ta ɗaure da ribom tasaka abaya red sosai tayi kyau tace”Aunty mutafi”.
“toh gaskiya kinyi kyau sosai”.
“nagode”.
nan suka fita a kashingiɗe suka samu Ammi anamata tausa kuyangin dake kusa da itane suka duƙa suka kai gaisuwa sosai abin yakebama Hafsat mamaki Ammi na ganinsu ta faɗaɗa murmuahin tare da cewa”gaskiya ƴammatana kunyi kyau sosai ku wuce dining kuci abinci”.
“toh Ammi”.
suka haɗa baki gurin wucewa dining sukayi inda Hafsat taga wani zungureren dining table an maƙareshi da kayan alatu kalakala kamar baza’ah mutuba jamata kujera Fatimah tayi zama Hafsat tayi itama taja ta zauna ta zubamusu abinci a plate ɗaya nansuka shiga ci.

8:30pm
Suna zaune a falo Fatimah na danna waya Hafsat na gefe tayi shiru Ummita ta fito cikin tsadadiyar shiga yayinda suma suna cikin alkyabba kallonsu tayi tare da cewa”ku tashi muje Hafsat takai gaisuwa fada”.
“toh”.
nan suka miƙe sega jakadiya ta shigo kallon Hafsat tayi tare da cewa”gaisheki uwar magajin gobe sannunki da zuwa Allah yasa alkhairi”.
“ameen jakadiya muje”.
cewar Ammi nan Ammi tayi gaba suka bi bayanta da jakadiya yayinda tunda suka fara tafiya kowa na cikin bayin gidan ya dena aikin da yake ya tsaya yana kwasae gaisuwa har suka shiga wani part dayafi kowanne guri kyau a cikin masarautar a bakin ƙofa suka tsaya sarkin ƙofa ya sanar sannan jakadiya tayo musu iso suka shiga kan Hafsat a ƙasa.

Ba abinda kakeji se ƙarar a.c daketa faman aiki a ƙayataccen falon inda wani dadaɗan ƙamshi keta tashi gefe guda kuma zaune wani farin mutumi yake akan kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana ganinsu ya miƙe fuskarsa a sake yace”sannu da zuwa Ammi “.
“yauwa”.
tafaɗa tana neman kujera ta zauna zama yayi a ƙasa suma su Hafsat suka zauna tare da cewa”ina yini “.
murmushi yayi tare da cewa”lafiya ƙlau Hafsat ya baƙunta”.
“Alhamdulillah”.
Hafsat tafaɗa tare da yin ƙasa dakai murmushi yayi tare da cewa”Allah yabada zaman lafiya”.
“Ameen”.
nan Ammi ta kalli Fatimah tace”kuje tagaida su Fulani”.
“toh Ammi”.
nansuka yimusu sallama suka tafi.

Binsu da kallo maimartaba sarkin kano yayi tare da cewa”Ammi kinko sanar da mara mutuncin yaronnan ina jiyemiki ya watsamiki ƙasa a idone domin gaskiya danasan wannan natsatsiyar yarinyar za’ah haɗa da wannan sakaran yaron daban bariba wlh tausayi tabani saboda Farouk ba ganin mutunci kowa yakeba yaronda ko tarbiyya bata isheshiba da kinyi shawara dani da Marwan kika aurawa ita tunda nake ban taɓa ganin inda wuta da ruwa suka haɗuba yarinya me tarbiyya a sakata cikin masifa”.
“waikai meyasa ka tsilgawa yaronnan ne toban haɗata dashi ban kasani ko silarta ya nutsu ya dena duk abinda yakeyi”.
“gaskiya ba lallai Ammi yanzufa case ɗin wata yarinya akeyi da sukayiwa fyaɗe nifa koson ace ɗanane banayi shiyasama da aka kirani nace suyimishi duk abinda zasuyimai nace kuma kar a ƙara kirana akan harkarshi “.
cikin takaici Ammi tace”toh kaidai tunda ka zare hannunka akanshi meye damuwarka da tsaramun yadda ya kamata inyi “.
ta miƙe rai ɓace ta fara tafiya a zuciyarta tana cewa”duk wanda yashiga tsakaninku insha Allahu seyaji kunya”.
tanata zancen zucinta ta fita rai ɓace.

Koda su Hafsat suka isa ɓangaren Fulani samun wani chocolate guy sukayi yana chart haɗa baki sukayi gurin cewa”salamu alaikum “.
ba tare daya ɗagoba yace”la….”.
maganar maƙalewa tayi sakamakon arba da yayi da fuskar Hafsat jitayi a jikinta ana kallonta ɗago idon da zatayi taga Marwan nabinta da wani mayen kallo lura da hakane yasa Fatimah cewa” Yah Marwan sannu”.
wani shu’umin murmushi yayi tare da kallon Hafsat yace”yauwa Teemah wannance amaryar tamu”.
“eh Yayah Ummah tana nan”.
“eh tana nan bara inyomuku magana da ita”.
“toh”.
nanya tafi harya kusa yin tintiɓe garin kallon Hafsat .

Be jima da shigaba suka fito su uku da Fulani da wata yarinya wadda zata iya kaiwa shekaru ashirin dashida kuma Fulani na ganinsu tayi murmushi cikin ƙissa tace”a’ah kace amaryar Son ce a darennan baki gajiba na ɗaukama seda safe za’ah kawomunke”.
“a’ah Ummah ina yini”.
taƙarasa zancenta tare da duƙawa har ƙasa saurin ɗagota Fulani tayi cikin muryar ƴan duniya haɗe da kissa tace”tashi ɗiyata zauna lafiya ƙlau Fatimah ya Ammin”.
“lafiyarta ƙlau tana ɓangaren Abbu”.
“okay to sannunku Larai kawomusu abin motsa baki ko bakuga surukatabane”.
“toh ranki shidaɗe”.
ɗayar yarinyar ce taƙarasa inda Hafsat take murya ƙasa-ƙasa cikin kashe murya takama hannun Hafsat tace”Aunty sannu da zuwa”.
“yauwa sannu ya sunanki”.
“Maryam”.
“sannunki Maryam”.
nanko Maryam se wani shashafa hannun Hafsat take tayi yayinda Fatimah tayi kicin-kicin da ranta ta miƙe tare da cewa”Aunty ki taso mutafi kinsan Ammi tace muyi sauri mukoma”.
“toh”.
nan Hafsat ta miƙe Fulani ce tace”haba daughter da kun zauna kun ɗansha abinsha nakumasaka a kawomuku”.
“wlh kuwa Ummah dasena rakasu”.
“yanzufa muka gama cin abinci Ummah”.
“to shikenan ku gaida Ammin”.
“toh zataji”.
“bara na rakasu Ummah”.
“toh”.
“amaryarmu senazo”.
“toh Allah yakawoka”.
nansuka fita yayinda yaketa binta da wani mayen kallo seda ta rakasu har ƙofar Ammi sannan ta juya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button