HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Haɗa ido Aunty Fido sukayi da Fatimah tayi ƴar dariya ba tare da tabari Hafsat ta ganiba ganin suna niyyar gane a jikinta yake yasa Hafsat cewa”Aunty bara naje sama yanzu zan sakko”.
“toh sekin dawo daughter”.
nanta tafara tafiya suka bita da ido tana hawa step ɗin farko Aunty Fido tace”daughter ina kika baro niƙab ɗinki bayan kinsan abinda Amminki tace”.
rasa inda yake tayi domin ita ta manta da duniyar wani niƙabma ita wata ƙarya ce ta faɗomata tace”gashi nan a jakata Aunty”.
“ok kiriƙkulawa kinji dai abinda Ammi tace sabodake matar aure ce”.
“toh”.
nan ta haye sama jiki na rawa dan kar a ƙara jehomata wata tambayar.

Tana shiga Aunty Fido ta kalli Fatimah tace”yau ko meke damun daughter oho ko duk missing ɗin Ammin ne haka”.
dariya Fatimah ƙara kyalkyalewa da ita tace”yanzu dai ba missing ɗin Ammi bane wannan ya Abdallah kunga wannan video ɗin amsarku tana ciki”.
taƙarasa tare da kunna wayarta ta nuno video ɗinsu Hafsat ta kunnawa su Aunty Fido sosai sukasha dariya seda suka gama Abdallah yace”dama akwai ranar da zamuga Hammah na murmushi irin haka mu seya dauremana fuska kodai yasantane”.
“eyi gashi yayiwa masoyiyarsama befasan ko waceceba domin nima kaina da danaga yadda sukayi naɗauka ma ya ganeta amma ita dai da alama ta ganeshi to Aunty kinji inda kikaji ƙanshin turaren ɗanki”.
“naji kace watan cin uban ɗana yafara kamawa domin da alama ba ƙaramin so yakemataba batare daya saniba nima dole na rife ido naci ubansa yanzunnan turawa su Ammi su gani suma”.
“toh Aunty muma munshirya tsaf dan tayaku ko Yah Abdallah shiyasama ban bari ya ganniba”.
“wlh kuwa my kwaɗayyar ƙanwata”.
dariya sukayi gabaki ɗayansu nan Fatimah tatutturawa su Ammi da Hajjo .

Tana shiga bedroom ɗinsu ta zame rigar jikinta ta ɗaura towel a ƙirjinta ta wuce toilet ba abinda tafarayi se brush seda tayi sau uku ta kalli mirrior ɗin bango ta tofar da miyau tace”Allah ya isa ɗan iska mara tarbiyya ka wani tsotsarmun bakina da wani ƙazamun bakinka dakasha sakashi ana ƴan bariki”.
ta fashe da kuka tare da ƙara tofar da miyau share hawayenta tayi tare da ƙara cewa”sakarai me kallon ƙirjin mutane kawai danasan zan haɗu dakai da banjeba kajamun tambaya gurin Aunty nijima nake kamar kallon da Fatimah takemun nata ganene”.
wata zuciyarce tace”bata ganeba saboda daga ke seshine a gurin”.
“yauwa gwara da bata ganeba danaji kunya matuƙa”.
seda tayita maganganunta sannan ta shiga yin wanka.

Tana fitowa ta shirya cikin wani haɗaɗen material dack blue riga da skirt ƴar powder kaɗan tasaka sannan ta bar gaban madubin da niyyar fita tare da shinshina jikinta jitayi ƙanshin turaren F2 kamarma lokacin tasaka tsaki tayi takoma ta zabga burmemen hijabj ta fice zama tayi a falo kusa da Fatimah murmishi Aunty Fido tayi tare da tayi wadda ta daɗe dashan gayu na tarbar AbbansuAfnan tace!!!!

kuyi manage har yau zazzaɓi ne ke damuna naso yin typing me yawa

Tallah! Tallah!! Tallah!!!
Ina kuke masoyana na haƙiƙa kufito ku nunamun ƙauna ta hanyar siyan book ɗina mesuna BAR RAINA ALLURA(Itama ƙarfe ce) cikin farashi mafi sauƙi #200 kacal ta asusun 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank aiko da shedarka ta wannan no 08108362334 ko katin vtu ta wannan no 08108362334 sena jiku.

Votes and Comments
Plz share

Daga Alƙalamun ƴar mutanen Gwarzo.✍️arzo.*_✍️???? *HASKEN RAYUWATA*

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION

SUBSCRIBE
DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

PAGE 3️⃣5️⃣➡️3️⃣6️⃣

     "daughter wanka kikayine naga an canza kaya".

“eh Aunty kayan jikina ne naji suna warin wani abu”.
Aunty Fido takusa sakin dariyar da take ɓoyewa dakyar ta maida ita tace”toh ai shikenan”.
Fatimah ko kasa jurewa tayi ta tattake da dariya harda riƙe ciki sosai Hafsat ta tsargu seta wani dake tace”kekuma dawa irin wannan dariya haka kidai dena domin dariya rage imani takeyi”.
tsagaitawa tayi da dariyarta tace”toh Aunty nagode “.
“yauwa tashi muje kitchen mu taya Ashwariy ayi a ƙarasa karya dawo”.
“toh”.
nan suka tafi kitchen suka bar Aunty Fido da Abdallah daketa ƙunshe dariyarsu sukayitayi ƙarasa aikin sukayi suka zuba awarmers suka jere a dining area suka dawo falo suka zauna suka cigaba da hira.

Suna tsaka da hira sukaji shigowar motocinsu Abban Afnun murmushi Aunty Fido tayi tare da gyara ɗaurin ɗan kwalinta tace”gasunan “.
buɗe ƙofa akai wani farin balarabe ne yashigo gefensa kuma wasu yara guda biyu da sauri Aunty Fido taje ta rungume mijinta bakunya yaranma rungumeta sukayi nan tace”sannu da zuwa My “.
“yauwa Dear”.
duƙawa su Hafsat sukayi haɗe da cewa”Abbah ina yini”.
“lafiya ƙlau daughters an iso lafiya inceko My bata takuramuku”.
yayi maganar ne cikin alamar tsokana murmushi Aunty Fido tayi haɗe da cewa”sarkin tsokana kafa dawo su Afnun bakuga Aunties ɗinku bane bakuyimusu oyoyoba”.
kyawawan yaran ne suka ruga ɗaya ta rungume Hafsat ɗaya kuma Fatimah murmushi Hafsat tayi tare da cewa”sweetheart kinada kyau”.
kowa na gurin ne yakalli Anun ana dariya murmushi Hafsat tayi tare da cewa”sweetheart a ina kikasan kyau “.
“a school ɗinmu Auntynmu ke faɗamana yadda zamu gane mutum mekyau infaɗamiki”.
murmushi Hafsat taƙarayi wanda har seda beauty point ɗinta suka lotsa tace”sweetheart base kin faɗa “.

Murmushi Aunty Fido tayi tare da cewa”My muje dining abincinka yana jiranka inafata dai bakaci a wani gurinba ko”.
waro ido waje yayi tare da kama haɓa yace “nina isa inci wani abincin bayan nasan yanzu kinan kinyimun girkinnan naki me ɗan karen daɗi muje naci nayi wanka kinsan gobene birthday ɗin My twins ɗina ina Salman ne banganshiba”.
“toh muje angama ma komai su Hafsat basu daɗe da dawowaba daga siyayyar komai me twins yaudai na rigaka Salman ƙila yana part ɗinshi”.
nan suka wuce dining shida twins da Aunty Fido tayi serving ɗinsa yanata santi tunkafin yakai bakinsa saboda ƙanshin dake tashi nanya shiga ci .

Su Hafsat na falo ko wacce cikinsu tana danna wayarta da alama dai chart suke wata iska ce ta taso yayinda lokaci ɗaya aka fara ruwa me ƙarfi kallon Fatimah Hafsat tayi haɗe da cewa”tashi mu tafi ɗaki sanyi nikeji “.
“toh muje nima dama abinda zance miki kenan”.
nansuka tashi suka haye sama kan gado suka hau haɗe da hawa kan bed ɗinsu sukaja blanket saboda sanyin da gari ya ɗauka bata daɗe da kwanciyaba wayarta dake gefenta tayi ƙara dubawa tayi tare da ganin baƙuwar number har bazata ɗaukaba kuma seta ɗaga tare da cewa”salamu Alaikum”.
jin muryar Yayah Amin tayi yace”wa’alaiki salam sister kinmanta daniko?”.
murmushi Hafsat tayi me sauti tace”Yah Amin kace kaine wlh banmanta dakaiba bani da numberka shiyasa amma ina ni ina mantawa da babban Yayana sukutum da guda to yasu Ummita da mutan gidan namu”.
“duk lafiyarsu ƙlau mun dawo Gwarzo fa “.
Fatimah dake kusa da Hafsat tunda taji Hafsat da wanda take hakanan taji ta kafeta da ido ba tare data saniba Hafsat ko na lura da ita murnushi tayi tare da cewa”masha Allah hadda su Iyah kuka dawo amma”.
“a’ah dagani se Bappah da Furera dasu Isah Bappama gobe yace ze kaisu makarantarku anfara kuma saida provision ɗin ba laifi gaskiya ana siya sosai “.
“masha Allah harnaji daɗi to ya akaiko Iyah tabari kuka dawo kukuwa”.
“wlh bansaniba ina Fatimah”.
yafaɗane cikin alamun nishaɗi kallon Fatimah Hafsat tayi data kafeta da ido murmushi tayi tare da cewa”gata Yayah ku gaisa”.
“toh”.
nan Hafsat ta miƙawa Fatimah cikin girmamawa suka gaisa sukayi sallama yayinda ko wanne cikinsu yana cike da son ɗan uwansa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button