HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Juyawa sukayi suka koma part ɗin Ammi suka wuce bedroom ɗinsu suka fara karatun Al-qur’ani megirma seda sukayi sosai sannan Hafsat tace”Fatimah shafamun mannan yanzu kinga gobe da wuri zamu fita”.
“toh”.
nanta ɗakko man tabuɗe kanta tashiga shafamata.

Zaune take itada Maimartaba cikin kissa tace”sarkina intambayeka man”.
“inajinki sarauniyata faɗi zancenki kanki tsaye”.
murmushin riƙaƙun mata ƴan duniya tayi me ma’anoni kala-kala tace”dama zancen yarinyar nan ne da Ammi ta aurawa Farouk ne naga Son har yau shiru bezoba kuma kaga yarinyar nan bazataji daɗi ba wlh”.
“hakane ai seda na faɗawa Ammi karta aurawa wannan sakaran yaron yanzu gashi yana niyyar watsamata ƙasa a ido har cemata nayi a mayar da auren kan Marwan amma tace ita ga wanda ta aurawa amma kibari zanyi wani abu akai”.
“haba sarkina kabari kawai nidai gani nayi kamar yarinyar bazataji daɗiba ne anzo an ajeta ba ango ba labarinsa”.
“hakane aida Ammin taji shawarata da haka bata faruba dan ninasan ba wanda ze iya riƙe yarinyar nan tsakani da Allah kamar Marwan ba wanda yakaishi hankali da tinani ga kamilin mutum mezesa ta haɗa yarinya da ɗan iska mara hankali”.
murmushin jindaɗi Fulani tayi tace”a’ah kabari zanyiwa magana da Son ɗin”.
tafaɗa cikin ƙissa tare da miƙewa tace”Sarkina bara naje na gaida Ammi”.
“toh”.
nanta tafi shikuma yakoma yana tinanin ta inda ze ɓullowa Ammi harta yarda ta raba auren.

Tana fita bata zame ko inaba se part ɗin Ammi ana yimata iso tashiga Ammi na ganinta ta faɗaɗa murmushinta tace”sannunki da zuwa ƴata”.
“yauwa Ammi”.
tafaɗa tare da ƙarasawa ta duƙa ta gaidasu sannan ta zauna akan carpet cikin ladabi Ammi ce tace”dama Fulani yanzu nake shirin sakawa a kiramun ke muyi shawar-warin gobe taron karrama Hafsat da za’ah gudanar kan harkar tafiyar”.
“masha Allah to aikece me yanke hukunci Ammi duk a ƙar-ƙashinki muke”.
murmushi Ammi tayi tace”hakane tona baki wuƙa da nama kan mutanen daya kamata a tafi misalin goma za’ah gabatar da taron”.
“toh Ammi Allah yakaimu”.
nan sukaita hira baki kal-kal kamar me ƙaunar Ammi ba ita ta tafiba se tara da rabi na dare.

Tana fita ta nufi part ɗin Marwan dan bashi labarin abinda yake faruwa ba tare da knocking ba tashige bedroom ɗinsa samunsa tayi yanata shagalinsa da wata kafurar mata da alama ma ba musulma bace yana ɗaga ido sukayi ido huɗu da Fulani wata uwar tsuka ta saki ta juya saurin ɗaga ƴar mutane yayi yabi bayan Fulani shangabanta yayi tare da cewa”haba Ummah yazaki tafi kiyi haƙuri “.
tasss ta saukemasa wani lafiyayyen mari tace”kaiwai Marwan yaushe zaka dena bin matane kamar bunsuru yanzu duk ƙoƙarin da nakeyi dan kasamu cikar muradinka ashe baka gani meya ƙara kawo Cicilia cikin gidannan koko so kake mahaifinka da yake nuna kaina Allah ne wani yakaimasa tsegumunka “.
“sorry Ummah jinayi inbanyiba bazan iya komaiba shiyasa data kirani na bata izinin zuwa amma kiyi haƙuri”.
“to ka sallameta yanzu saboda kasan kaine dai Sarkin gobe banaso ka kasa cikamun burina “.
“toh Ummah bara na sallameta”.
“yauwa yimaza toh”.
“nina tafi ɗakin Maimartaba seda safe zamuyi magana”.
“toh”.
nan ta tafi tabarshi yanata zabga smiling .

Cicilia dake tsaye jikin ƙofa duktaji abinda yafaru ce tace”tab ai abunda baze taɓa faruwaba inga sweetheart da mata baniba “.
ƙarasawa tayi inda yake tsaye yanata zabga murmushi tayi ta dafashi tace”duk naji abinda yake faruwa wato ni ka maidani mara tinani kamun alƙawarin aure zakaje ka auri wata banza can baniba kamanta da abunda na taɓa faɗamaka ko to ka aureta nagani domin sena kasheta wlh ko wacece dan wlh bazan bari ka ɓatamun rayuwata ba ka tafi ka barni ba bayan kasan munyi alƙawarin aure dakai “.
“to ana dolene nafasa auren naki banza karuwa”.
“hmm dole kacemun karuwa tunda kaga makwaƙuleni kana hangen wata wlh sena kasheta maga yadda zaka auretan ingani nidakai mutu ka raba inkuma ni karuwa ce kaikuma kwarto ne”.
tass ya mareta tare da nunata da yatsa yace”kada ki ƙara kirana da wannan sunan inba hakaba zakiga meze faru dake aure kuma baki isa kin hananiba “.
dafe gurin tayi tare da ɗaukar jakarta ta shiga tafiya fuuu har takai bakin ƙofa zata buɗe ta waiga tace”badai ina rayeba maga yadda zaka aureta wlh sena kasheta”.
ta rife ƙofar bammm ɗaga ƙafaɗa yayi alamar ita tashafa ya nufi guarding .

Bayan fitar Fulani ta wuce ɗakinta tayi shirin tafiya ɗakin Maimartaba wayarta tafara ringing ɗagawa tayi tare da cewa”hello ƙawata”.
daga ɗaya ɓangaren akace”na’am ya yarinyar nan taci abincin ko zuwa yanzu komai ya daidaita ko”.
“inafa komai ya daidaita yanzu zuwama nayi naga kotaci wlh ko haɗuwa bamuyiba anya aikin boka Matsatsaku ko yanayi yanzu kuwa”.
“kema dai wlh kinada abin haushi wlh yazakice anyako aikinsa yanayi ai a tinanina keme bada shedace tunda bashi ya wuce miki gaba ba da harkika samu kikakai mutuniyarki ƙasa sannan kika raba tsakanin ɗan da uban ba”.
“hakane Saratu kuma anyako ba wanine yaga lokacin dana zuba ba ya hanata ci kuwa”.
“ƙila dan kinsan gidannan naku akwai munafukai kala-kala kibari gobe zanje miki gurinsa da sassafe”.
“toh shikenan domin banaso Marwan ya rasa yarinyar nan kodon alƙawarin da yayimun”.
“hakane”.
nansuka ɗan taɓa hira daga ƙarshe sukayi sallama ta tafi part ɗin Maimartaba.

MONDAY

Guri yayi guri baƙi duk sun halarci taron karamawar a ƙurarren lokaci suka isa a cikin wasu haɗaɗun Land cruser baƙaƙe masu baƙin glass ƙarasawa sukayi parking space ɗin mall ɗin sukayi parking sannan suka fito yayinda duk sunsha Alkyabba baƙaraminkyau sukayiba nan suka nufi inda aka tanaza
dominsu suka zauna ganin yadda gurin ya cika ne yasa Hafsat ƙara yiwa Allah godiya nan aka fara gudanar da ansar kyaututuka yayinda Bappah ya amsar mata kyautar kujerun makkah Ammi kuma ta amshi kuɗaɗen anata kabbara sannan aka sanar da tafiyarta wakiltar ƙasa gurin Musabaƙar da za’ah gudanar ta ƙasashe.

Kakakin majalissa ne ya tashi ya amshi loudspeaker yace”nima zanƙara da tawa kyautar ga wannan haziƙar ɗaliba kyautar dubu ɗari biyar sannan na ɗauki nauyin ginawa makarantar da suke block biyar upstairs”.
tafi aka shigayi principal ɗinsu ne ya tashi yace”ba abunda zamuce se godiya ranka shidaɗe Allah yaƙara arziƙi”.
“Ameen sannan zamu saurari jawabin godiya daga bakin haziƙar dalibarmu Hafsat Ibrahim da karatun al-qur’ani megirma”.
cewar m.c Hafsat ko ƙasa tayi da kanta tana tinanin yadda zata tsaya a gaban dubban jama’ar nan tayi magana tana cikin tinani taji Fatimah tace”Aunty ki tashi seki saki hular alkyabbar jikinki ga glass ki saka”.
“toh Fatimah”.
nanta ansa ta saka ta rife kanta da hular alkyabba ta tafi .

Habibah dake kusa da M. Jalaludeen ce tace”toh Malam yazanyi nabata haƙuri ba lallai abarni naje gurinta saboda dogarawan da suke tare”.
murmushi yayi yace”ki kwantar da hankalinki koda baki nemi yafiyartaba ninasan Hafsat bazata riƙekiba wlh”.
“hakane kam amma dai dukda haka yakamata na nema”.
“toh ai kinsan dole zatazo tagaidamu ko”.
“hakane”.
ba abinda Habibah take se santin alkyabbar dake jikin Hafsat a zuciyarta har Hafsat ta isa gurin da m.c yake ta duƙa cikin girmamawa ta ansa tare da gaidashi amsamata yayi nanta waiga tana kallon mutane tafara zazzaga jawabin godiyarta da larabci tamkar balarabiya tanayi tana hawaye domin abinda bata taɓa zata zefaru da ita bane a rayuwarta harta gama sannan cikin zazzaƙar muryarta tashiga karatun al-qur’ani megirma suratul A’araf .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button