HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Ummita na fita tak’arasa suka gaisa dasu shugaban makarantarsu Hafsat nanya sanarmusu da abin Alkhairin da suka samu Ummita harda kukan farinciki murmushi shugaban principal yayi tare da cewa”ai Allah yayima ‘yarku baiwa ku godewa Allah domin Hafsat akwai kwakwalwa sede fatan Allah yak’aramata hazak’a Kuma Dan Allah son samu kubarta ta k’arasa karatunta sannan Kuma nanda sati biyu za’ai taron bada kyaututuka ga daliban da sukazo na farko dana biyu dana uku kyaututukansu “.
kallon junasu Bappah sukayi Ummita tayi k’arfin halin cewa”insha Allahu mungode sosai Allah yakaimu lfy”.
nansukai musu bayani sannan suka saka aka kira Hafsat suka yimata Allah sa alkhairi sannan suka tafi kowa cikin jindad’i.
Kwance take tana tinani murmushi tayi tare da cewa”niko meyasa nake missing d’in ganinka F2 koma dai me kukeyi ninafi k’arfinka”.
jin mutsi tayi Ummita ta gani tashi tayi zaune tarec da cewa”sannu Ummita”.
“yauwa d’iyar kirkina zauna muyi magana”.
gyara zamanta tayi tare da maida attention d’inta kanta jiki a sanyaye Ummita tace”Hafsat kinsan komai mutum yagani ya faru dashi muk’addarine daga ubangiji Kuma rubutacce ne dan haka ina mai sanar dake Iyah tayimiki miji ki kwantar da hankalinki bazata tab’a zab’armiki abinda ze cutar dakeba ki amshi wannan auren hannu biyu insha Allahu ze zama Alkhairi insha Allahu kinji d’iyata”.
murmushi Hafsat tayi Wanda yayi matuk’ar saka zuciyar Ummita tayi dad’i tace”bakomai Allah ya tabbatarmana da Alkhairi “.
“Ameen d’iyata abar alfaharina Allah yayimuku albarka ya k’ara shiryamunku kije ki siyomun mai Zan d’aura sanwa yamma na kwacewa”.
“Ameen Ummita na toh “.
nanta amshi kud’in ta tafi.
Bayan ta siyo ta tawo a hanyarta ta dawowa ta hangi kamar hijabin Furarea d’iyar Lantana a jikin wata tsamiya wucewa tayi tafara tafiyarta hartazo wucewa taga k’afa hud’u da hijabin ya d’an bud’e wa zata gani Haladu me shayi da Furera anata iskanci jikinta ne yafara b’ari tafara tafiya taji an lek’o dakai ta wuyan hijabin ance “wanne d’an iskanne yake kallonmu ne kaikuma ka cigaba da yimun aradun Allah akwai dad’i”.
Ido hud’u sukayi da Hafsat damm gabanta yabayar amma dake sunsaba se cewa tayi”to meye ake kallonmu ke sanda kike shan naki dad’i a barikin da kike zuwa wakika fad’awa koko saboda munafunci mu za’ah sawa ido inko hakane yanzu muka fara”.
Hafsat ko k’ara sauri tayi jikinta nata rawa ta nufi gida.
9:00pm
“Salamu alaikum”.
“Wa’alaiki Salam sannu da zuwa Iyah ce”.
“eh nice Hansai”.
“sannu da zuwa”.
“yauwa dama nazone kan batun aurennan danni banason asamu tangard’a azo a jawomin abun kunyarda harna mutu baze gogeba a iyalinaba”.
“hmm banda abinki ai magana tana nan d’azunma seda naje na fad’amasa yace shi yanzu baida kud’in sadaki amma abari seya samu se ayi”.
waro ido waje Iyah tayi tare da cewa”banganeba yaza’ai kibari ya kub’uce Hansai bayan kinsan saboda bak’in jinin yarinyar nan dabin maza ba wanda ze aureta a rugar nan ya zakiyimun haka niko ba ko sisinsa na yafe sadaki nabashi ita sadaka Allah yabasu zaman lafiya”.
“Ameen toko tunda hakane anjuma in na amso wayata sena kirashi na sanarmasa ranar Asabar suzo d’aurin aure kawai ammafa kinyi tinani domin idan ya kucce shikenan k’ilama wanine yafara kai tsegumi bara nayimaza na gyara abun”.
“yauwa Hansai nagode sosai kicemasa na yafe komai suzo kawai danni tsbarma kawai zan saimata “.
murmushi Hansai tayi Wanda ni kaina Real eeshow bansan me take nufiba tace”Ina laifi ai hakanma yayi su birni ina ruwansu da kayan d’aki Allah dai yasa Alkhairi”.
“Ameen ngd sosai Hansai Allah yabar zumunci”.
“Ameen”.
nanta rakata waje ta dawo gida.
Koda Hafsat tagama taya mahaifiyarta abinci hakan yayi daidai da shigowar Furera ganin Hafsat na magana da Ummita se hankalinta ya tashi matuk’a dakyar ta iya tafiya tashige d’akin Lantana tanata b’ace-bacen rai .
BAYAN KWANA 4
Yau takama Asabar inda kowa yanata shirye-shirye!!!!!
Questions
ko ince
Quiz
1- Anyako auren Hafsat za’ah yishikuwa?
2-Inkuma ya yiwu wazata aura?
3- Ya sunan mijin Kuma mutumin arzik’ine?
5- Wazata bama kujerun Makkan data samu?
6-Meye ma’anar murmushin Hansai?.
A cikin comments seki fad’i abinda kike tinani ze faru dan inji inyayi daidai da yadda labarin yake
Yanzu zamu fara wasan don da shimfid’a mukai
More Votes
And
Comments
More typing
Plz share
Daga Alk’alamin’yar mutanen Gwarzo._tanen Gwarzo.* ✍️???? *HASKEN RAYUWATA*
MALLAKIN
REAL EESHOW
HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION
DUNIYAR LITTATAFAN HAUSA TV
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQvSubscribe and share
PAGE 1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣
"Iyah dan Allah kiyi hak'uri Hafsat duka nawa take da za'amata haka kuma ma ni yanzu banida ko biyar d'inda zammata kayan d'aki Iyah kiduba ki gani wlh Hafsat yarinyace".
cikin masifa Iyah tace”kaga Iro ka fita a idona in rife dama waya fad’amaka ko kana dasu Zan bari kayimata wani abun ai daka ita se halinta da ‘yar tabarma za’ah kaita idan canma taje tanamusu karuwancin da uwarta take sata tasan ba kyaleta zasuyiba dan haka kama fitar da rai inkaga ba’ayi aurennanba to banida rai Kuma ko banida rai kabari akak’i ban yafemakaba ina laifi ma da aka samu wanda yake sonta domin ni namayi mamakin da yace yanasonta k”ila kyalkyal banza yagani dan haka fara shirin biki daka yau”.
idon Bappah sun kad’a sunyi ja ya bud’e baki ze magana Yayansa Shafi’u ya d’agamasa hannu tare da cewa”karka sake sakamana baki domin wannan shawara da Iyah ta yanke tayi bazamu bari azo har gida a b’atamana zuri’ah ba ka shirya Asabar za’ah d’aura bandama an shanyeka yaza’ai ka zuba ido kana kallon yarinya me shekaru irin wannan a gida tana yawon sakarci to baze yiwu ba”.
shiru Bappah yayi Iya tace”ka tashi kaban guri sokon namiji wanda baida katab’us a gidansa”.
jiki a sanyaye ya tashi ya fita bayan ya tafi Badamasi yace”aiko Iyah gwara da kikai haka inba hakaba se anje an kwasomana abun gori har mu mutu baze dena bummuba”.
“eyi ai shiyasa nayi haka nima anje anko dudubawa amare katakwaye gurin Nasiru kuwa yacemun ya gama”.
“A’ah yaushe ya gamane”.
“eh d’azu ya aiko”.
“toh bamuje”.
nansuka tafi.
A daddafe ya k’arasa b’angarensu yana zuwa ya zauna sharaf Ummita dake jan carbice tana lazumice a tsorace ta kalleshi tare da cewa”lafiya Bappan Hafsat naga kashigo a irin wannan yanayin meyafaru “.
cikin damuwa murya a sanyaye yace”Iyah ta zab’ama Hafsat miji kuma tace muddum in nahana aurennan seta tsinemun”.
“toh seme dan kakarta ta zab’a mata miji ai abun alfarinmunema kuma Iyah bazata tab’a zab’amata wanda ze cutar da rayuwartaba ni banga abin b’acin rai ananba a ganina inbanda abunka”.
“ya zakice haka memakon kinemomin mafita sekice haka bafa asan yaronba ta cemun d’an ciranine k’ilama iyayensa zasu aura mai ita Allah dai yasa ba gagararre bane danni bazan b’ata kud’ina insai wasu kayan d’akiba ita Iyar data jajiboshi tayimata”.
“hmm kana bani mamaki Bappan Hafsat ai komai ka gani muk’addarine daga Allah kadena tashin hankalinka Allah yasa Albarka yabasu zaman lafiya da zuri’ah ta gari”.
sauke numfashi Bappah yayi cikeda tausayin matar tasa da ‘yayansa yace”bakomai Allah ya tabbatar mana da Alkhairi amma ni Hafsat nakeji koya zata amshi abun”.
“Ameen mijina haka nakeson naji kana cewa ka kwantar da hankalinka ba wani abunda ze faru Hafsat yarinyace me biyayya ba abinda ze gagara da izinin Allah”.
murmushi Bappah yayi yana k’arajin k’aunar matartasa nabi tako ina na jikinsa.