HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Hafsat dake shirin shigowa d’akin taji duk abinda ya faru ta share d’an guntun hawayenta tausayin iyayenta nabi ta ko ina na jikinta juyawa tayi zata nufi d’aki sega Lantana Itada Hanne ‘yarta tana wak’a tana cewa”Hanne azo a fara shirye-shirye dan tunda ank’ak’aba me bak’in jini a cikin bikinnan dole mu tashi tsaye kar a shafamiki saboda tsabar bak’in jini da dandin da ake zuwa seda akayi gwanjanta sannan aka samu wani masaki ya taya shima dan besan ciki fanko bace dabe d’aukaba”.
murmushi Hafsat tayi ta shige d’aki sukuma suka wuce.
Sallama akayi Ummita ta lek’a ganinsu Billy ne yasata cewa”a’ah su Bilkisu ne sannunku da zuwa”.
“yauwa Ummita”.
nansuka gaidata tayimusu jagora har d’akin Hafsat samunta sukai tana sallah zama sukai Ummita na Shirin juyawa Zully tace”Ummita tare muke dasu shugaban makarantarmu suna waje da Bappah wai kije inji Bappah”.
“toh Zaliha “.
nanta fita abinta Hafsat nayin sallama suka rungumeta harsun kusa fama mata hannu suka had’a baki wurin cewa”albishirinki sweetheart ke kikazo ta d’aya kinga yadda gari ya d’auka kuwa ko ina kaje zancen da akeyi kenan jiya aka sanar da daddare”.
hararsu Hafsat tayi tare da cewa”kudai bakwa raboda tsokana kuga yadda ‘yan meduguri suka zubarda k’ira’ah kuce ni kwayi kwa gama k’aryarku”.
“sweetheart wlh dagaske muke kuma ‘yar nan kinci kujerun Makkah guda ukuma da kyauttutuna manya da million biyu da sauran abubuwa”.
“Dan Allah dagaske kuke ko wasa”.
“wlh dagaske mukeyi jiya da ana fad’a jinayi kamar nayi tsintsu nazo nan na fad’amiki”.
wasu hawayen farin cikine suka zubomata nantake tayi sujjudushshukur tayi godiya ga Allah sukaita murna.
Ummita na fita tak’arasa suka gaisa dasu shugaban makarantarsu Hafsat nanya sanarmusu da abin Alkhairin da suka samu Ummita harda kukan farinciki murmushi shugaban principal yayi tare da cewa”ai Allah yayima ‘yarku baiwa ku godewa Allah domin Hafsat akwai kwakwalwa sede fatan Allah yak’aramata hazak’a Kuma Dan Allah son samu kubarta ta k’arasa karatunta sannan Kuma nanda sati biyu za’ai taron bada kyaututuka ga daliban da sukazo na farko dana biyu dana uku kyaututukansu “.
kallon junasu Bappah sukayi Ummita tayi k’arfin halin cewa”insha Allahu mungode sosai Allah yakaimu lfy”.
nansukai musu bayani sannan suka saka aka kira Hafsat suka yimata Allah sa alkhairi sannan suka tafi kowa cikin jindad’i.
Kwance take tana tinani murmushi tayi tare da cewa”niko meyasa nake missing d’in ganinka F2 koma dai me kukeyi ninafi k’arfinka”.
jin mutsi tayi Ummita ta gani tashi tayi zaune tarec da cewa”sannu Ummita”.
“yauwa d’iyar kirkina zauna muyi magana”.
gyara zamanta tayi tare da maida attention d’inta kanta jiki a sanyaye Ummita tace”Hafsat kinsan komai mutum yagani ya faru dashi muk’addarine daga ubangiji Kuma rubutacce ne dan haka ina mai sanar dake Iyah tayimiki miji ki kwantar da hankalinki bazata tab’a zab’armiki abinda ze cutar dakeba ki amshi wannan auren hannu biyu insha Allahu ze zama Alkhairi insha Allahu kinji d’iyata”.
murmushi Hafsat tayi Wanda yayi matuk’ar saka zuciyar Ummita tayi dad’i tace”bakomai Allah ya tabbatarmana da Alkhairi “.
“Ameen d’iyata abar alfaharina Allah yayimuku albarka ya k’ara shiryamunku kije ki siyomun mai Zan d’aura sanwa yamma na kwacewa”.
“Ameen Ummita na toh “.
nanta amshi kud’in ta tafi.
Bayan ta siyo ta tawo a hanyarta ta dawowa ta hangi kamar hijabin Furarea d’iyar Lantana a jikin wata tsamiya wucewa tayi tafara tafiyarta hartazo wucewa taga k’afa hud’u da hijabin ya d’an bud’e wa zata gani Haladu me shayi da Furera anata iskanci jikinta ne yafara b’ari tafara tafiya taji an lek’o dakai ta wuyan hijabin ance “wanne d’an iskanne yake kallonmu ne kaikuma ka cigaba da yimun aradun Allah akwai dad’i”.
Ido hud’u sukayi da Hafsat damm gabanta yabayar amma dake sunsaba se cewa tayi”to meye ake kallonmu ke sanda kike shan naki dad’i a barikin da kike zuwa wakika fad’awa koko saboda munafunci mu za’ah sawa ido inko hakane yanzu muka fara”.
Hafsat ko k’ara sauri tayi jikinta nata rawa ta nufi gida.
9:00pm
“Salamu alaikum”.
“Wa’alaiki Salam sannu da zuwa Iyah ce”.
“eh nice Hansai”.
“sannu da zuwa”.
“yauwa dama nazone kan batun aurennan danni banason asamu tangard’a azo a jawomin abun kunyarda harna mutu baze gogeba a iyalinaba”.
“hmm banda abinki ai magana tana nan d’azunma seda naje na fad’amasa yace shi yanzu baida kud’in sadaki amma abari seya samu se ayi”.
waro ido waje Iyah tayi tare da cewa”banganeba yaza’ai kibari ya kub’uce Hansai bayan kinsan saboda bak’in jinin yarinyar nan dabin maza ba wanda ze aureta a rugar nan ya zakiyimun haka niko ba ko sisinsa na yafe sadaki nabashi ita sadaka Allah yabasu zaman lafiya”.
“Ameen toko tunda hakane anjuma in na amso wayata sena kirashi na sanarmasa ranar Asabar suzo d’aurin aure kawai ammafa kinyi tinani domin idan ya kucce shikenan k’ilama wanine yafara kai tsegumi bara nayimaza na gyara abun”.
“yauwa Hansai nagode sosai kicemasa na yafe komai suzo kawai danni tsbarma kawai zan saimata “.
murmushi Hansai tayi Wanda ni kaina Real eeshow bansan me take nufiba tace”Ina laifi ai hakanma yayi su birni ina ruwansu da kayan d’aki Allah dai yasa Alkhairi”.
“Ameen ngd sosai Hansai Allah yabar zumunci”.
“Ameen”.
nanta rakata waje ta dawo gida.
Koda Hafsat tagama taya mahaifiyarta abinci hakan yayi daidai da shigowar Furera ganin Hafsat na magana da Ummita se hankalinta ya tashi matuk’a dakyar ta iya tafiya tashige d’akin Lantana tanata b’ace-bacen rai .
BAYAN KWANA 4
Yau takama Asabar inda kowa yanata shirye-shirye!!!!!
Questions
ko ince
Quiz
1- Anyako auren Hafsat za’ah yishikuwa?
2-Inkuma ya yiwu wazata aura?
3- Ya sunan mijin Kuma mutumin arzik’ine?
5- Wazata bama kujerun Makkan data samu?
6-Meye ma’anar murmushin Hansai?.
A cikin comments seki fad’i abinda kike tinani ze faru dan inji inyayi daidai da yadda labarin yake
Yanzu zamu fara wasan don da shimfid’a mukai
More Votes
And
Comments
More typing
Plz share
_*Daga Alk’alamin’yar???? *HASKEN RAYUWATA*
MALLAKIN
REAL EESHOW
HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION
DUNIYAR LITTATAFAN HAUSA TV
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQv
Subscribe and share
PAGE 1️⃣5️⃣➡️1️⃣6️⃣
Biki domin kowa harkar gabansa take Iyah ce keta sauri bata zame ko inaba se gidan Hansai samun Hansai tayi zaune tana zage zogale k'arasawa tayi inda take tare da cewa"salamu alaikum ".
“Wa’alaiki Salam a’ah Iyah kece da sassafennan haka “.
“eyi ba dole ki ganniba nazone naji yadda kukai dana baki kud’in sadakin da kika kaimasa dan bazanje insaida tinkiyata a banzaba basuzoba”.
murmushi Hansai tayi tare da cewa”ai Iyah tunda kikaji shiru ai ya amsa yau zaki gansu sunzo a d’aura ya tafi da kayarsa a huta da jangwangwama”.
washe baki Iyah tayi tare da cewa”yanzu naji duka ato dan inbasuzoba aradun Allah se anbiyani dama kan wata mutuniyar arzik’ine da da sauk’i amma kan wannan banzar bazan b’ata kud’ina ba yanzuma da kika ganni zuwa zanyi ink’arasa biyan kud’in kayan katakwaye gurin Nasiru na biyo”.
“hmm ai Iyah kinsan bazanyi wasaba nima bazanso abinda ze tab’a darajarkiba”.
washe baki Iyah tayi tare da cewa”aidama nasan haka Hansai toni bara na wuce”.
“Toh”.
nanta tafi abinta seda tabiya gurinn Nasiru tak’arasa biyansa kud’insa sannan ta nufi gida cikeda farinciki .
Tin tashinta taketa jin fad’uwar gaba ga wata kasala da takeji wasu hawayene suka zubomata masu zafi jin sallama kawai tayi Kamar a mafarki taji muryar su Billy saurin share hawayenta tayi tare da k’ak’alo murmushi rungumeta sukai zama sukayi a gefan tabarmar datake kwance suka zauna kallon su tayi tare da cewa”sannunku da zuwa nayi missing dinku sosai”.
“muma haka sweetheart munso zuwa Amma ai yau wuni zamuyi ya hannun naki anjuma M. Jalaludeen yace zezo yak’ara gaidaki”.
hawayen datake b’oyewane suka zubo sharr cikin rikicewa suka had’a baki wurin cewa”sweetheart meyake faruwa haka kodai hannun ne ?”.
share hawayenta tayi cikin k’arfin hali tace”bakomai kawaidai ina tinanin rabuwa dakune”.
“kamarya ki rabu damu ina zaki “.
“yau ake d’aura aurena fa”.
had’a baki sukai gurin cewa”what amma dai wasa kike sweetheart dawa kenan amma dai bada M. Jalaludeen ba ko”.
cikin k’arfin hali da rifawa kakarta asiri tace”wani d’an uwanmune “.
“d’an uwanku Amma baki tab’a fad’amanaba saboda ba yadda muka d’aukeki haka kika d’aukemuba yanzu da bamuzoba da sede muzo muji anyi aurenki tashi mutafi Zully”.
yadda suka k’arasa maganar yasa Hafsat sanin bak’aramin haushi sukajiba suka mik’e da niyyar tafiya sukaji muryar Ummita na cewa”kuyi hak’uri Bilkisu itama kanta batayi kwana biyar da sanin da ita za’ayi aurenba bakuma waya bare tasanarmuku”.
“toh Ummita amma angon a ina yake”.
rasa tacewa Ummita tayi saboda ita kanta batasan waye angonba murmushi k’arfin hali tayi tare da cewa”meye na sauri d’iyoyina kubari zakuga angon naku nanda anjuma”.
“toh shikenan Ummita Allah yakaimu amma meye sunan angon namu ne sa’ah da yayimana wuf da k’awarmu “.
shiga tinanin amsar da zata basu Ummita tayi sejin Hafsat tayi tace”kuwai mekukeci nabaka na zubane anjuma ganinsama zakuyi k’arewar sunansa”.
hamdala Ummita tayi tare da cewa”bara in shafamiki maganinki.”
“toh”.
nanta shiga shafamata sunayi suna hira cikin nishad’i sukaji muryar Lantana akansu nace”ke waye zeyi wa’incan ayyukan kowa na aiki ke kina nan shafaffa damai ‘yar Iyah isau kinfi kowa to ai seki tashi”.
cikin sanyin murya Ummita tace”kiyi hak’uri magani nake shafamata yanzu zata fito”.
“lallai se an gama shafamata kenan za’ai aikin kenan ai gwarama da yau alak’ak’ai zatabar mana gidan ba tare ankwaso mana d’an gaba da fatihaba ajamana zagi”.
“ke Kuma wacece da har kike fad’awa Ummitarmu da sweetheart haka”.
“yishiru Zulaihat “.
harara Lantana ta watsawa Zully itama ta mayarmata tare da cewa”yarinya inma zagina kikayi da wani sweet me zanci ubanki”.
Zully zatayi magana Ummita tayi mata wani kallo hakan yasata yinshiru nan taita tsagale-tsagalenta basu kulataba harta tafi bayan ta tafi Ummita tasa Hafsat ta tafi nan suma suka bita suka shiga aiki inda suka tadda bakowa suka shiga aiki.