HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Suna tsaka da aiki sega Furera da Indo sun shigo suna wak’e-wak’ensu har zasu wuce suka hangi hannun Hafsat da k’ullin bandage kallon juna sukayi inda suka matsa sunata habaice-habaicensu ganin basu kulasubane yasa Furera tura Indo daidai saitin hannun Hafsat aiko nan ta fad’a kan hannun wata uwar k’ara Hafsat tasaki wadda taja hankalin mutanen dake gidan da gudu Yayah Aminu yashigo ganin hannun Hafsat na jinine yasashi k’arasawa gurin ya rungumeta Bappah ne yak’araso gurin tare da kallonsu Furera daketa zare Ido alamar rashin gaskiya yace”mekukayimata”.
fara sosa kai sukai alamar rashin gaskiya sukai hakan yasashi harzuk’a yayi kansu da nufin dukansu yaji muryar Iyah ta fasa kururuwa tana cewa”ze kashemun jikokina saboda wannan ‘yar iskar yarinyar da uwarta ta gama dashi “.
nan ‘yan gida suka zagayesu kowa ya harzuk’omasa ba Wanda abinda suka aikata kallon Zully Bappah yayi tare da cewa”Zulaihat meyafaru”.
nanta bashi labarin komai shiko Aminu kama Hafsat yayi sukayi b’angarensu Bappah ya kalli Iyah tare da cewa”to kinji abinda sukayimata metayimusu karayacefa a gurin Iyah”.
Iyah da daketa b’ararrako cetace”to Ina ruwana da wata karayarta ai garin yawon iskancinta ta sameta yaudai zamu huta in rabuda k’aya inhuta Kuma karka sake ka b’atamun farincikina domin banga abinda sukaimataba da har taketa wani kuka danta ganka kukuma ku wuce amare kusha shagalinku”.
su Furera najin haka suka wuce suna dariya sosai abin yabawa su Zully mamaki suma suka tafi Ummita ta cigaba da aikin.
Suna shiga ya dad’a shafamata magani yace takwanta yafita bayan yafita su Billy suka shiga taddata sukai tanata zabga ajiyar zuciya zama sukayi kusa da ita yayinda sukejin wani irin tausayinta na kamasu Billy cetace”Sweetheart anyako Iyah kakarkuce kuwa ya tana ganin gaskiya ta taketa”.
“hmm kakarmuce kidena fad’in haka Ummita bazataji dad’iba komai kikaga tayi daidaine watarana se labari”.
“toh amma meyasa da aka kawomiki mijinnan bakice da M. Jalaludeen ba kodon kifita daga wannan jarabar k’angin rugar nanba sweetheart “.
“hmm Billy kenan ai auren zumuncine Kuma aishi M. Jalaludeen Koda na fad’eshi ba yanzu zamuyi aureba senanda shekaru biyu Kuma Iyayena bazasu yaddaba shiyasama ban fad’eshiba amma anjuma inyazo zanje inmushi sallama”.
“hakane Amma dakin fad’a Kuma k’ila yafito saboda bazeso ki kufb’ucemasa ba”.
“hakane Kuma banyi Kuma wannan tinaninba dama Allah yasa ba mijina bane”.
tak’arasa maganarta murya na rawa Kamar zatayi kuka yishiru kinji sweetheart Billy kunno mana su Nusful-Hayat d’inmu itakuma sweetheart tayiwa Ahmad kallon k’arshe sede a bikinmu Kuma a had’u a gaisa”.
dariya tayi nan suka bud’e sunayin searching sukayi sukaga wani had’ad’en update dasu F2 sukayi da manyan kaya amma na sarauta sunsha kyau wata mummunar fad’uwa gaban Hafsat yayi saurin dafewa tayi ba tare sun luraba ta koma gefe ta kwanta tare da sauke wani numfashi me k’arfi Wanda hakan yasa su Zully kallonta sukace”lafiya sweetheart”.
“lafiya k’lau kawai hannuna nad’an bige nad’anji zafi”.
“toh kitashi kije kiyi wanka”.
“Tom.
nanta nufi d’akin Ummita ta tub’e ta shiga wanka.
Jama’ah sosai sun taru a rigar Rumada sanadiyyar d’aurin auren mutum biyar da za’ah gudanar guri yayi guri iyayen kowanne ango sunzo amma Banda na Hafsat sosai hankalin Iyah ya tashi domin har anfara d’aura aurukan sega wasu mutane nan ‘yan tsirari tsofafi su biyar ana fad’ama Iyah zancennan taji sanyi nan aka d’ad’d’aura auren sauran Bappah da ganin wa’innan mutanen yasa hankalinshi kwanciya nan liman yace”ku mik’o kud’in sadakin ku”.
Wani dattijone yace”to gashi”.
ya mik’a bandir d’in ‘yan dubu-dubu guda d’aya amsa liman yayi nan aka d’aura auren Hafsat Ibrahim da angonta Umar Muhammad akan sadaki dubu d’ari kowa na gurin ne ya kalli d’an uwansa Iyah dake mik’owa wani Bappanta goro taji wani marok’i yace”and’aura auren Hafsatu da angonta Umaru akan sadaki dubu d’ari aradu a kaf fad’in rugar nan ba’ah tab’a samun d’iyar datayi kasuwa irintaba”.
damm gaban Iyah yabayar tace”Bappah naji Kamar ance dubu d’ari”.
“eh hakane nima naji menene”.
“bakomai gashi”.
nanya tafi kama baki Iyah tayi tare da cewa”lallai Hansai kinci amanata bara inzuba Ido ingani nanda d’an anjuma in mutane sunyi sauk’i na b’ulla gidan naki”.
nanta juya ta tafi cikeda bak’in ciki.
Zaune suke suna hirarsu sukaji abinda marok’innan yace”a yau ranar Asabar an d’aura auren Hafsat da angonta Umaru akan sadaki dubu d’ari lakadan ba ajalanba”.
kallon juna sukayi Zully tace”kice k’awata gidan arzik’ine kenan ashe sunan angon namu Umar”.
murmushi Hafsat tayi nan sukaita tsokanarta .
5:00pm
ba abinda kakeji se k’arar motoci nashiga rugarsu Hafsat gabaki d’aya Range Rover ne bak’ak’e wuluk masu bak’in glass basu zame ko inaba se k’ofar gidansu Hafsat motocinnan sunfi guda talatin duk iri d’aya mutanen rugako kowa lek’e yake yaga wa’inda sukazo kuma gurin wa sukazo seda suka d’an juma sannan aka bud’ema wata dattijuwar mata k’ofa tafito cikin shiga ta alfarma motar bayanta nanma wasu mata suka fito suma cikin shigarsu ta alfarma su biyu se wani yamutsa sukeyi kamar sunga kashi d’ayar motar kuma wata kyakyawar yarinyace tafito meji da class wadda bazata wuce 17yrs sauran Kuma motocin kuyangine suka fito gefe guda sega Hansai duk’awa Hansai tayi tare da cewa”Allah yajada ran uwar soro ma iya tafiya”.
murmushi farar tsohuwar tayi na k’asaita Wanda ke dad’a nuna ita jinin sarautace tace”muje Hansa’u”.
“godiya muke”.
nan Hansai tayi gaba sukabi bayanta basu zame ko inaba se k’ofar d’akin Iyah.
Iyah daketa sallamar bak’intace tana ganinsu ta wangale baki tare da cewa”sannunku da zuwa marhabun lalai Hansai bak’i mukayine ?”.
“eh nan tasa a shimfid’amusu tabarmi zama sukayi amma wa’innan matan se wani yayyatsina sukeyi kallon Lantana datazo kallon mutanen Iyah tayi jiki na rawa tace”akawowa bak’in Hansai fura da nono susha da dambu”.
murmushi k’asaita wannan tsohuwar tayi tare da cewa”a’ah munk’oshi ina Amaryar tamu takene zuwa mukayi d’aukar Amarya”.
Iyah dake yin hamma ce tayi saurin gintsile hammar tare da cewa”bangane amaryarkuba wacece”.
“hmm Hajiya mufara gaisawa tukun”.
“au namanta anyini lafiya”.
murmushi dattijuwar nan tayi tare da cewa”lafiya k’lau”.
“madallah”.
Hansai dake gefece tace”Hafsatu mana wai baki gane wacece wannanbane Iyah”.
damm gaban Iyah yabayar hade rai tayi tare cewa”Hafsat Kuma wacece wannan matar d’in”.
“eh Hafsat mana wannan da kike gani babar sarki Muhammad Umar ce jikanta ta aurawa Hafsat”.
dammm k’irjin Iyah ya buga inda nan take gumi yashiga tsatstsafomata ta ko Ina tace”yanzu cin amanar da zakiyimun kenan Hansai wato dama kinsan gidan kud’ine gidan mutuncine kika bari akai wannan abun to baze yiwuba dole a canza ya saketa ga ‘yar uwarta nan Fatimah me tarbiyya ya aura ba’ah bashi jabuba ya saketa dan wannan batada tarbiyya ta rigada ta gama zubar da k’imarta a waje”.
murmushi dattijuwar matar nan tayi tare da cewa”aini ita nayimasa sha’awa ba Fatimah ba a kiramun surikar tawa”.
tashi tsaye Iyah tayi cikin masifa tace”wlh ba’ah isaba dole wannan yaro ya sakarmun jikatab inbayason Fatimah a kyale duka”.
mutanen gida dake ba gaskiya kowa ya nuna haka kallon Hansai me babban d’aki tayi tare da cewa”rakamu muga surukar tawa inada abinyi sosai a gida”.
tak’arasa fad’a tana gyara alkyabbarta kallon Hansai Iyah tayi tare da cewa”kinyi kad’an kiyimun haka ina kallonki dole ya sakarmun jikata aiba dole bane munafuka maga inda zaku tafi da ita inbkwason Fatimah kubari duka Banda ma rainin hankali a ina yaga waccan fankan fayau d’in aradun Allah dole ya saketa”.
murmushi Hansai tayi tare da cewa”ai aure ya rigada ya d’auru sekuma fatan zaman lafiya keko bak’in cikine ze kasheki da ‘yan gidannan ga kud’inki nan kya maida tinkiyarki”.
Hansai tak’arasa zancenta tana murmushi nan suka nufi b’angaren su Hafsat Iyah na biye dasu tanata sababi.