HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Suna shiga sukaga su Hafsat sunata hira da Ummita saurin tashi Hafsat tayi da hannu d’aya ta fara kiciniyar shimfid’amusu tarbama amsa Billy sukayi suka shimfid’a duk’awa sukai har k’asa suka had’a baki gurin cewa”Ina yininku”.
Murmushi dattijuwar nan tayi tace
“lafiya k’lau cikinku wacece Hafsat d’in “.
k’asa Hafsat tayi da kai tare da cewa”nice mama”.
murmushinta ta fad’ad’a tare da cewa”zonan surukata”.
ta fad’a tare da bud’emata hannu Hafsat wani irin farinciki taji ya saukarmata tana d’an d’ari-d’ari harta k’arasa nanta rungumeta se lokacin su Ummita suka gane surukan Hafsat ne nan ta zuzubamusu fura sallama akayi su Billy su fito nan ta kalli Me babban d’aki tace”Mama zanje na rakasu”.
“toh ‘yar Albarka sekin dawo”.
nanta mik’e ta kalli Ummita suka fita suka shiga d’aya d’akin inda suka tadda Bappah yana Shan furarsa cikin nishad’i k’arasawa sukayi inda yake suka zauna k’asa Hafsat tayi da kanta murmushi Bappah yayi tare da cewa”lafiya d’iyar Bappanta fad’i buk’atarki d’iyar Albarka”.
“Bappah dama”.
“dama me”.
“Inaso ne a!!!!!
Question
1- Waye Umar
2-Iyah zatabar aurennan kuwa
3-Angonnan ko ze anshi Amaryar nan
Tallah! Tallah!! Tallah!!!
Ina maso buk’atar siyen littafina me suna BAR RAINA ALLURA (Itama k’arfece) cikin farashi mafi sauk’i Naira #200 kacal ta Account Number ta 2411022356 Aisha Ibrahim Zenith Bank aiko da shedar biyanka ta wannan phone number 08108362334.
A nuna mun k’auna ta hanyar siyenshi
Votes and Comments
Plz share
Daga Alk’alamin’yar mutanen Gwarzo. ✍️ mutanen Gwarzo.*_???? *HASKEN RAYUWATA*
MALLAKIN
REAL EESHOW
HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION
DUNIYAR LITTATAFAN HAUSA TV
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQv
Subscribe and share
PAGE 1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣
Kasa magana tayi ƙasa da kanta murmushi Bappah yayi tare da cewa"to Ummita ƙila ke za'ah faɗawa ki faɗamun ".
“hakane kuma taso muje ki faɗamun”.
“toh”.
murmushi Bappah yayi nan suka tafi sukayi nesa dashi tafaɗamata a kunne murmushi Ummita tayi tare da cewa”aikon dai yayi bara in sanarwa da Bappah”.
“toh”.
nan Ummita ta ƙarasa tayiwa Bappah magana ƙasaƙasa murmushi yayi tare da cewa”aiko hakan yayi kinga yarinya tafimu dogon tinani Allah yayimiki Albarka kema yabaki masuyimiki biyayya yabaki zuri’ah tagari”.
“Ameen Bappah yimaza kije nabaro baƙi bara naje nima kibasu nonon nan sukaima iyayensu karki manta dashi”.
“toh”.
nanta tafi Ummita ma ta tafi.
Tundaga nesa yake kallonta saboda wani fresh datayi seda yaƙaremata kallo fuskarshi ɗaukeda murmushi yace”amincin Allah ya tabbata ga masoyiyata abar alfaharina”.
murmushi tayi tare da yin ƙasa da kanta tace”salamu alaikum Malam ina yini”.
“wa’alaiki salam sarauniyar birnin zuciyata lafiya ƙlau ya ƙarfin jikin naki”.
“naji sauƙi Malam”.
“masha Allah ,Allah yaƙara sauƙi”.
“ameen”.
shirune yabiyo baya tsakaninsu inda Hafsat tashiga duniyar tinanin ta inda zata fara da sanar dashi abinda yake faruwa tana wannan tinanin taji yace”sweetheart zamu tafifa yamma nayi”.
sauke numfashi tayi tare da cewa”dama Malam inada magana bansan yadda zanyi insanar dakaibane wlh”.
murmushi yayi tare da cewa”inajinki sweetheart faɗamun komenene”.
jinkinta taji yayimata sanyi ba abinda take se tinanin yadda ze karɓi zancen seda ta nisa murya na rawa tace”Malam kayi haƙuri da abinda ze fito daga bakina kasan komai kaga yafaru to dama muƙaddarine daga Allah Malam kayi haƙuri yau aka ɗauramun aure da wani ɗan uwana”.
damm gaban M.Jalaludeen yabada yayinda yaji komai ya tsayamasa cik yawun bakinsa ya ƙafe ƙaf ga wani jiɓi da yake ketomasa da jiri da yake neman ɗibarsa dakyar ya iya aro jarumta hawaye nabin fuskarsa yace”Hafsat meyasa kikayimun haka kinsan inasonki amma kikayimun haka ya kikeso nayi da rayuwata amma ki kasa sanarmun”.
itama hawayenne ya zubomata murya na rawa tace”Malam kayi haƙuri nima nan bansan da wannan aurenba se saura kwana biyar ɗan uwanmune dan Allah karkaga laifina inasonka ina ƙaunar dukda bansamu na aurekaba dan Allah karkayimun mummunar fahimta koba komai bazan taɓa mantawa da irin halarcin da kayimunba a rayuwata kaine mutum na farko daya fara faɗamun kalmar datafi kowacce kalma a duniya tsada wadda bakowa ake faɗawaba kalmar da wani mahaluki be taɓa faɗamun itaba bayan Bappah na da Ummitana se kai kalmar inasonki kayi haƙuri naso ace murayu da juna cikin aminci da ƙaunar juna”.
jiyayi dukda yana cikin damuwa jiyayi kalamanta sun basa tausayi jan numfashi yayi tare da cewa”to bakomai Hafsat naji daɗin kalamanki bazan taɓa ganinki a matsayin kin yaudareni ba kinji dama haka Allah yatsara bazamu rayu da junaba”.
ya ƙarasa zancensa murya a sanyaye tausayinsane yaƙara kama Hafsat tace”Malam ina neman wata alfarma dan Allah”.
“inajinki kifaɗi komenene insha Allahu indai befi ƙarfinaba zanyimiki”.
“hmm zaka iyama Malam”.
“toh inajinki zanyimiki”.
seda tayi shiru ta furzar da numfashi sannan tace”Malam dan Allah ka auri Habibah”.
“what Hafsat kinsanko mekike cewa kuwa yarinyar da bata ganin mutuncin kowa shine zakice na aureta bayan kowa yanason yaga ƴaƴansa sun tashi cikin tarbiyya a rayuwa kima canza zancenki”.
yadda yayi magana baƙaramin bata tsoro yayiba tace”dan Allah Malam ka aureta kaifa kace kome nace zakayimun amma seda na faɗamaka sannan kace bazaka iyaba”.
taƙarasa zancenta tana mai fashemasa da kuka jiyayi kukanta har cikin zuciyarsa jiyayi kamar ya rungumeta ya lallasheta jin kukan na taɓamasa zuciyane yasashi cewa”yi shiru Hafsat na yarda zan aureta amma darajarki zataci”.
saurin share hawayenta tayi tare da buga tsalle tama manta a gabansa take tace”nagode sosai Malam bansan da wanne baki zangodemaka ba duk wannan abin datake yi zata dena insha Allahu Malam nagode”.
sauke numfashi yayi tare da cewa”aini dama nayiwa zuciyata alƙawarin nemomiki fariciki aduk inda yake nagode sosai da halarcin da kikayimun”.
“nikeda godiya Malam sannan Malam nabaka ɗaya daga cikin kujerun makkan danaci karkayi tinanin komai dama tin randa kuka sanarmun nayi niyyar baka”.
wasu hawayen fatincikine suka zubomasa yace”Hafsat bansan da wanne irin baki zangodemikiba haƙiƙa keta dabance nayi takaicin rashin samunki a matsayin uwar ƴaƴana amma dukda haka nagode da zaɓin da kikayimun insha Allahu nanda shekara ɗaya zan aureta insha Allahu bazaki taɓa taɓewaba Allah yabaku zaman lafiya”.
“ameen Malam nikeda godiya tun ku kuka koyamun kome na zama nagode da har ka amshi tayina nagode sosai”
nan yayita yimata godiya suka koma gurinsu Billy M.Jalaludeen ya sanar dasu kujerar makkan data bashi sosai sukaji daɗin abinda tayi yaƙara da faɗamusu haɗashi aure datayi da Habiba sosai sukayi farinciki yayi gaba yaɗan basu guri Zully ceta makawa Hafsat harara tare da cewa”kedai wlh sweetheart bansan irin halinkiba wlh kayita haƙuri ana kwararka Billy kalli abinda Habibah tayiwa Sweetheart dan Allah amma shine harda haɗata aure da M.Jalaludeen wlh nidai da tare muke da Hafsat se zuciyata ta buga saboda haushi Allah yasa karkije gidan sarautar kiyita wannan sakarcin naki”.
“wlh kuwa dan rainaki zasuyi mufa yanzu munada gurin zuwa yanzu zakiganmu jibi ko gata”.
“toh ina ruwanku shifa alheri danƙone baya faɗuwa ƙasa banza sena ganku ga wannan inji Ummita”.
“toh mungode kedai kija mutuncinki karkiyita haƙuri a kashemanake”.
murmushi tayi tace”najiɗin nidai kuzo kar inji shiru”.
“toh Allah yakaimu seki saka a sanar da masu tsaron ƙofa dankar a hanamu shiga”.
“toh Allah yakaimu lafiya”.
“ameen”.
nansuka tafi zuciyar kowa ba daɗi kowa yanata matse kwalla ta rabuwa da juna dakyar ta iya jan kwafafunta da sukaimata nauyi ta nufi cikin gida.