HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Tana shiga Ummita tasata tayi wanka da wasu turaruka da wannan dattijuwar tasa kuyangi suka zuba a cikin ruwan wanka tafito jitayi jikinta yanamata santsi taita taɓawa ƙarasawa tayi ɗakinta tafara neman ɗan vaseline ɗinta taji ana buga ƙofa ƙarasawa tayi gurin tare da cewa”waye”.
jitayi an haɗa baki gurin cewa”mune ranki shidaɗe”.
wani banbarakwai taji tare da cewa”Maman tana can ɗakin”.
“eh ai ita ta turomu ranki shidaɗe mu shiryaki”.
shiru tayi setaji anshigo ɗakin ganin dattijuwar matar nan tayi tare da cewa”daughter shiryamunke za’ayi”.
kasa yimata musu tayi ta ɗaga kai alamar to nan dattijuwar matar tabada umarni aka shiga shiryata cikin wani dakaken lace white me adon flowers pink se wasu stone masu ɗaukar hankali daketa walwali bata akai tasaka rigada skirt ɗin sun amshi jikinta kamar angwadata aka kashemata ɗaurin ɗankwali tayi wani mugun kyau aka sakamata fashion pink aka ɗauremata dogon gashinta da pink ɗin ribom ga kwalliya datasha lokaci ɗaya kamanninta suka canza inka ganta bazaka taɓa cewa Hafsat ɗinda kasani bace ƴar ƙauye wadda Iyah ta tsana bace sannan suka ɗakko wata farar alkyabba aka ɗauramata baƙaramin kyau tayiba dattijuwar matar nance ta kalleta tare da cewa”kai masha Allah kinyi kyau daughter mujeko sauri nakeyi”.
taƙarasa tare da kama mata hannu kanta a ƙasa tace”toh”.
nansuka fita.
Kowa na gurin ba abinda yake se aikin kallonta har suka ƙarasa gurin Ummita dattijuwar tsohuwar nance tace”gata muna jira domin inada baƙi sosai a gida”.
“toh bara nakaita gurin Bappanta”.
nan Ummita takamata hannu suka shiga ɗakin Bappah sosai yaji daɗin yadda yaga ɗiyar tasa ta canza wanda har yasashi kasa ɓoyewa yace”amma gaskiya ɗiyar Albarka kinyi kyau sosai wannan tin yanzu kin canza inaga kinje cikin hutu aisemu kasa ganeki”.
“wlh kuwa nima haka zance ka rigani”.
cikin shagwaɓa tare da turo baki tace”kaji Bappah taya zaku kasa ganeni sekace wadda aka canzawa fata”.
“toh ɗiyar Bappanta meze hanamu gane autar Ummitanta”.
“yauwa Bappanah”.
nan yayimata faɗa sannan Ummita tafito da ita tabawa dattijuwar matar nan amanar Hafsat nan suka nufi ɓangaren Iyah data fita tin ɗazu suna zuwa suka isketa ta tattara yayyen Bappah tanata zazzaga masifa.
Shiga sukayi me babban ɗaki tace”gatanan Iyah ayimata nasiha asamata albarka”.
“ni waceni dayin faɗa aini ban isaba ban kai nanba”.
“yazakice baki kai nanba keko kika isa”.
“dana isa da anyi abinda nace domin banga dalilin barin aurennanba tunda dai ansan yarinyar nan ta rugada ta gama zubarda mutuncinta a titi ga ƴar mutunci nabaku kunƙi to dole ya sakarmun jikata ehe”.
Lantana daɗi yakamat ba zato ba tsammani sukaji muryarta tsulum tace”aradu Allah saboda kowa yasan tagama barbaɗar da mutuncinta ne yasa batada ko saurayi a kaf rugar nan”.
murmushi me babban ɗaki tayi tare da cewa”hmm ai Iyah ki kwantar da hankalinki indai akan zubar da mutuncine mun yadda yanzu dai kiyimata faɗa mutafi sauri muke”.
“bazanyiba ya sakarmun jika nidai”.
murmushi me babban ɗaki tayi tare da kama hannun Hafsat suka fita suka shiga mota ɗaya samun yarinyar nan sukayi a ciki inda Iyah tabiyosu tanata ruwan masifa ita ala dole se ansaki Hafsat suka lula Hafsat nata kuka Ummita nayi Yayah Aminu nayi.
Suna isa cikin masarautar kano aka saki algaita wadda ake kaɗawa duk wata ɗiya data auri jinin sarauta Hafsat ko ganin abin take kamar a mafarki ba abinda takeyi se aikin kalle-kalle abinda bata taɓa ganiba murmushi yarinyar nan tayi tare da cewa”Aunty Hafsat anbugamiki tambarin shigowa gidan sarauta”.
“banganeba”.
“wannan abinda kikaji shine shedar shigowarki familynmu amma gaskiya matar Yayah kinada kyau sosai wlh domin yaya inya ganki seya gigice kingako dana ganki da farko yadda naji wani daɗi koda yake shimafa yayah ƙarshene gurin kyau”.
murmushi Hafsat tayi tare cewa”kai Fatimah harda tsokana ke zance ai kinada kyau”.
“wlh ba tsokana bace ai gaskiyace”.
“to nagode”.
suna wannan zancen me babban ɗaki tace”to sarkin surutu ki kyaleta haka ku sakko mutafi”.
“toh”.
nan suka fita suka fara tafiya inda tunda suka fara tafiya kowacce kuyanga data ɗago duk sun duƙar da kansu suna kai gaisuwa har suka isa ƙofar ɗakin me babban ɗaki nantasata tayi addu’ah sannan tayi tashiga tabarsu itada Fatimah suna magana dafata Fatimah tayi tare da cewa”kyace wannan yarinyar akwaita da surutu kinga muna magana har Ammi tashige tabarmu mujeko Aunty”.
“wlh ko ɗaya toh muje”.
nan suka shiga ɗaga kan da Hafsat zatayi taci karo da!!!!!
Votes and comments
plz share
_*Daga Alƙalamin ƴar Mutane???? *HASKEN RAYUWATA*
MALLAKIN
REAL EESHOW
HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION
DUNIYAR LITTATAFAN HAUSA TV
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQv
Subscribe and share
PAGE 1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣
Da tafkeken hoton F2 yasha kayan sarauta black masu adon golden ga sumar kansa nan tana nan a yadda take ganinta a hotunansa da suke gani ga wani ɗan kunne a kunnensa kamar wani mace gangarowa tayi gurin small pink lips ɗinsa yayi daidai da fuskar ga dogon hancinsa har baka yana kallon wani gurin da alama bemasan anayin hotonba an rubutu a ƙasan hoton ansa *Umar Muhammad Umar (Farouk)* damm gabanta yabayar inda duk taji takasa koda kwakwaran motsin a zuciyarta tace"nashiga uku ni Hafsat meke shirin faruwa danine wacce rayuwa aka jefani ciki haka wannan ai saurayin da Billy take mutuwar sone idan nayimata haka ai banyimata adalciba ballekuma nibema kwantamunba mezanyi da wannan mara tarbiyar nidai a rayuwata inashiga banu daga wannan se wannan nabaro wata a can yanzu zan shiga wata kuma Allah ka kawomun ɗauki ka shigemun gaba a duk lamurana".
tana cikin wannan zancan zucin taji Fatima tace”la Aunty kallon mijin naki kikeyi”.
saurin dawowa tayi daga duniyar tinanin datashiga tafara wuni-wuni tace”aini bammasan shineba Fatima”.
murmushi Fatima tayi tare da cewa”aiko dai shine Aunty muje kar Ammi tace na tsareki da surutu”.
“toh”.
nansuka shiga wani tanƙamemen falo yasha kwalliyar gidan sarauta samun Ammi sukayi ta kashingiɗa akan kilisarta Hafsat daketa faman kalle-kallece taɗan kintsa kanta har suka ƙarasa inda take fuskarta ɗaukeda murmushi Ammi tace”ɗiyata matso nan ki zauna nasan duk kin gaji gakuma sarkin surutu ta dameki”.
ƙasa tayi da kanta alamar kunya tace”a’ah Hajiya ba wata gajiya”.
turo baki Fatima tayi cikeda sakarcin shagwaɓa tace”Ammi nicema me surutun aidama kinfison Yayah yanzu kuma kin koma kan matarsa nima ana gama bikinnan zan tafi gurin Momyna Adamawa kuma in natafi bazan dawoba atom”.
murmushi Ammi tayi tare da cewa”waya faɗamiki nafisonki Fatima na shiyasama nayomiki sister dankifi jindaɗin zama kuyi komai tare”.
“toh nafasa tafiya zan zauna ganiga Auntyna”.
“yauwa good girl yanzu kuje ki nunamata bedroom ɗinki tayi wanka kema kiyi kafin kufito nasa anshiryamuku abinci “.
“tom Ammi Aunty tawo mu wuce”.
“toh”.
nan suka tafi inda duk inda takalla a ɗakin hotunansu F2 ne dasu Fatimah da wani wanda suke tsananin kama da F2 sosai bin wani corridor sukayi nan take ya sadasu da wata upstairs nan suka haye sama suna zuwa suka ƙofofi guda huɗu nan suka nufi ɗaya daga ciki ta gefen hagu itada Hafsat ba abinda takeyi se aikin kallo domin faɗin haɗuwar gurin ɓata lokacine nan Fatimah buɗe ƙofar nan take wani tamfatsetsen bedroom purple ya bayyana yayinda komai na ɗakin yake purple sosai gurin ya ƙayatar da Hafsat shiga sukayi Fatimah ta zauna gefen gado tare da cewa”wash gaskiya nagaji sosai Aunty yanaga kin zauna kan sofa kamar wata baƙuwa karfa kimanta nanfa kamar gidanki yake kafin ayimuku taron biki akaiki haɗaɗen gidanki”.
“bakomai Fatimah nanma ya isa muyi muyi wanka kinga lokacin magriba yana gabatowa “.
“toh ki tuɓe kishiga ga towels can ki ɗauki ɗaya kishiga”.
“toh”.
nan Hafsat tamiƙe ta jikin gado ta cire alkyabbar da dama dukta dameta sannan ta cire ɗan kwalinta jitayi Fatimah tace”masha Allah Aunty gaskiya kinada gashi sosai muda ake ganin munada gashi yauga wadda tafini ammafa gaskiya yayah Farouk yayi dace”.
hararta Hafsat tayi tare da cewa”nidai tashi ki miƙon towel ɗin ki nunamun toilet ɗin inshiga inyo”.
“toh”.
nanta miƙe ta ɗakkomata ta miƙamata amsa Hafsat tayi ta tuɓe kaya ta ɗaura ganinshi tayi ko rabin cinyarta be rifemataba tace”nidai Fatimah aramun hijab danni jina nake kamar tsirara wlh”.