HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Suna fita Marwan ya aje wayar hannunsa tare da cewa”gaskiya wannan zan kwashi ganima tab wai wai ni dama ni aka aurawa ita aida nadena neman mata har abada amma dukda haka senasan yadda nayi na rabasu bazan taɓa bari ya wuceni a komaiba itama wannan yarinyar ko zan rasa komai nawa sena mallaketa Ummah kitemakamun”.
“kwantar da hankalinka indai akan wannan yarinyar ne itadai kakeso”.
“eh Ummah na kitemakeni ban taɓajin son wata baby ba kamar nata”.
“toh kwantar da hankalinka me akai akayi mahaifiyarsu bare wani farouk da Ammi ko zan rasa zanin ɗaurawa seka aureta kamar yadda nayiwa mahaifiyarsu haka zanyiwa Farouk ɗin shima kuma shida mahaifinshi yayi gabas shikuma yayi yamma sarauta kuma kaine sarkin gobe”.
“yauwa Ummah na”.
shigowa Maryam tayi tare da cewa”gaskiya yarinyar nan duniyace hmm”.
“ke da Allah can gafara baki isa kin lalatamun My Queen ba kinyi kaɗan”.
“nifa ba wani abun naceba aina dena”.
“inma baki denaba sede ki nemi wata dan wannan idan nasameta nadena komai da nakeyi har shaye-shaye dukda Abbu besan inayiba amma zan dena komai”.
tashi tayi ta tafi tana ƙunƙunai kallonshi Fulani tayi tare da cewa”tin yaushe ta dena neman mata ai zancen da kasani seda na tashi tsaye kaima ka rage wasu abubuwan naka”.
“toh Ummah indai nasamu wannan bab ɗin zance yaƙare”.
nan sukaita birarsu wadda kusan duk yadda zasu raba Hafsat da F2 ne.
Suna shiga sukayiwa Ammi sallama sukai mata seda safe har sun juya sunfara tafiya Ammi tace”au Hafsat anmanto miki maganinki gobe insha Allah za’ah zo a dubaki”.
“toh Ammi”.
“yauwa ƴammatana ayi addu’ah kafin a kwanta”.
“toh”.
nansuka haye upstairs wucewa bedroom ɗinsu sukayi suna shiga suka wuce gefan bed suka zauna tashi Fatimah tayi ta ɗakko musu sleeping dress dogayen riguna tazo har inda Hafsat take tace”Aunty ga kaya nan mu canza inaso muyi magana”.
“toh”.
nan Hafsat ta ɗauka tashiga bathroom ta canza sannan tafito ta hau gado kamar yadda tasamu Fatima tahau zama tayi yayinda Fatimah ta ɗauki wayarta tayi dialing ɗin wata number bugu ɗaya aka ɗauka daga ɗaya ɓangaren akace”hello Fatimah tin ɗazu nake jiran inji kun dawo ki kirani amma najiki shiru”.
“wlh Aisha mun dawo dama jira nayi muzo kwanciya dama tambaya zanyimiki”.
“ok inajinki”.
“har yau Maryam tana nan da halinta a makarantarku?”.
“eh mana me hali yana fasawa ne tana nan”.
“toh nagode”.
“meyasaki tambaya”.
“gani nayi tanata shishigewa Aunty ne”.
“kaikai to tun wuri ki faɗama Aunty ta riƙa ɗauremata fuska”.
“toh se anjuma”.
“toh ki gaida Auntyn zanzo naganta”.
nanta kashe sauke numfashi Fatimah tayi tare da cewa”Aunty dan Allah kiriƙa ɗaurema Maryam da Yah Marwan fuska sabobada basu da hali domin Maryam wata ɗaya daya wuce seda akayi suspending ɗinta saboda neman mata da takeyi ba tare da kowa yasaniba da Ummah da Babah waziri suka maidata shikuma Yah Marwan ba abinda bayayi da kuyangin gidannan ba tare da Abbu yasani ba shikuma Abbu ya ɗauki son duniya ya ɗoramasa ya zare hannunsa kan Yayah Farouk yama koreshi banda Ammi da tini bama ze barshi ya riƙa zuwa gidannanba”.
ji tayi duk tausayin F2 yakamata inda a zuciyarta tace”zanso in temaki rayuwarka amma kuma ya zanyi da Billy masoyiyarsa”.
taɓata Fatimah tayi tare da cewa”kinyi shiru shigemikin nan da kikaga tanayi danta lalatakine”.
“insha Allahu zanyi Fatimah nagode”.
“bakomai Aunty sannan bakomai za’ah baki ki ansa kiciba a gidannan indai ba Ammi ba ko Yayah Abdallah koni karkici domin gidannan namu se a hankali”.
“toh nagode”.
nansuka shiga hira yayinda gefe guda kuma tana tinanin Ummita da Bappi matsalar da zasu shiga a gurin Iyah agefe guda kuma tana tanason jin labarin F2 a haka har bacci yayi gaba da ita.
AFTER ONE DAY
Ammi ce zaune akan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kira a wayarta seda tayi bugu uku sannan aka ɗauka murmushi tayi tare da cewa”me sunan Malam har yanzu kana nan da barcin nan naka na ƙaddara”.
cikin muryar zaratan maza masuji da class yace”Ammi ina kwana”.
“lafiya ƙlau”.
murmushi Ammi tayi tare da cewa”miskili kafi kurma ban haushi to yaushe zakazo”.
murmushin gefan baki yayi tare da cewa”Ammi wai har yau bazaki dena faɗamun wannan sunan ba”.
“bazan denaba har se randa kakoma kamar yadda kake da kana murmushinka”.
“hmm gaskiya banida lokacin dawowa saboda aiki yamun yawa lafiya Ammi”.
“lafiya ƙlau da wani albishir zammaka”.
“inajinki”.
yadda yake maganar kamar ammasa dolene yasa Ammi gane dandai itace shiyasa yake tsayawa yake doguwar magana da ita murmushi tayi tare dacewa”nayi maka mata har an ɗaura aurenma”.
a razane yace”what wacce irin mata Ammi toni gaskiya ban shirya yin aure yanzuba kuma ma ko auren zanyi zan nemi wata ƴar nigeria ne baƙauya marasa waye wa da ilimi to da nayi niyyar dawowa inganku gaskiya bazan iya dawowaba natsaneta kamarni F2 za’ah aurawa wata baƙauya to bazan taɓa dawowaba “.
seji tayi ƙittttt yakashe wayar jiki a sanyaye ta aje wayar tashiga duniyar tinani taji muryar Hafsat nace”sannu Ammi”.
ƙaƙalo murmushi Ammi tayi tare da cewa!!!!!!!
Dan Allah idan kinsan baki iya comments da votes ba kifita salin alin domin a wannan comnents da votes ɗin nakeson na fitar da wa’inda basa comments dan yanzu zamh tsunduma cikin labarin kai tsaye.
Tallah! Tallah!! Tallah!!!
Ina masoyana na haƙiƙa kufito ku nunamun ƙauna ta hanyar siyen paid book ɗina BAR RAINA ALLURA (ITAMA ƘARFE CE) ta wannan account number 2411022356 Aisha Ibrahim Zenith Bank aiko da shedar biyanka wato screen short ta wannan number 08108362334 ko kuma tranfer katin Mtn ko Airtel ta wannan number 08108362334 sena jiku.
Vote and comments
Plz share
Daga Alƙalamin ƴar mutanen Gwarzo. ✍️n Gwarzo.*_???? *HASKEN RAYUWATA*
MALLAKIN
REAL EESHOW
HOME OF QUALITIES WRITER’S ASSOCIATION
SUBSCRIBE
DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV
PAGE 2️⃣1️⃣➡️2️⃣2️⃣
"Hafsat kiyimun alƙawari komai wuya bazaki juyawa Farouk bayaba ko kowa zeƙishi saboda Farouk yana tsakiyar maƙiya wanda suka rabashi da mahaifinsa basuson ganinshi kusa dashi na nema masa aurenki ne badon komaiba saboda nutsuwarki da hankalinki a jikina inajin kece zaki zamo *HASKEN RAYUWARSHI* ki haskaka masa futular da zata dawo dashi daga cikin duhun daya shiga".
shiru Hafsat yayinda tausayin F2 ke ƙara ƙaruwa a zuciyarta gefe guda kuma a zuciyarta tana cewa”ni Hafsat ya zanyi da babbar aminiyata Billy zata kalleni a maciya amana amma kuma idan nacema Ammi bazan iyaba banyimata adalciba ta zaɓeni domin tasan zan iya Billy kiyi haƙuri “.
jitayi Ammi tace”Hafsat ko bazaki iyabane “.
saurin dawowa tayi daga duniya tinanin data tafi ta sauke ajiyar zuciya tace”Ammi zan iya insha Allahu kome ze zama bazan taɓa gudunsaba zanyi iya bakin ƙoƙarina”.
“nagode sosai daughter badon komai na faɗamiki haka sedan nasan zaki iya inaso kiyi ƙoƙari ki zama silar dawowar murmushi a fuskarshi”.
“insha Allahu Ammi zanyi duk yadda kikace”.
“nagode Allah yayimuku Albarka yabaki juriyar zama dashi domin mutum ne me wuyar sha’ani sannan inaso itama Fatimah a riƙa ƙara mata karatu”.
“Ameen Ammi toh”.
“ina Fatimah ta shigane?”.
“tana ɗaki tana shiryawa “.
“ok”.
nan Hafsat tace”nima bara naje nayi wanka”.
“toh”.
nanta tafi binta da kallo Ammi tayi cikeda tausayi tace”toni yazanyi da wancan hutsun shikuma daya kashemun waya bara na kira Hajjon Adamawa naji yadda za’ayi”.
Ɗaukar wayar ta tayi tare da dialing number Hajjo bugu ɗaya ta ɗauka tare da cewa”salamu Alaikum Ammin Fatimah muna hanya zamuzo muga amarya”.
“wa’alaiki salam amma shine baku sanar daniba ya gida”.
“lafiya ƙlau Maimartaba ne nima bansan da tafiyar nanba da safennan yake sanarmun mumma kusa ƙarasowa”.
“toh Allah yakawoku lafiya dan wlh da matsala”.
“ameen tofa muna isowa zan ƙaraso”.
“toh sekun zo ɗin”.
nanta kashe tare da sauke numfashi jitayi sarkin ƙofa na sanar da isowar Maimartaba part ɗin gyara zama tayi tare da bada izni nan ya shigo cikin takunsa na ƙasaita har ya isa gefan kujerar da take ya zauna ƙasa yace”Ammi ina kwana”.
haɗe rai Ammi tayi tare da cewa”lafiya ƙlau”.
“masha Allah dama su Papi ne zasuzo”.
a taƙaice tace”toh”.
“zan wuce fada”.
“toh Allah ya tsare”.
“ameen”.
nanya miƙe tare da yimata sallama ya tafi bayan fitarshi wasu hawaye suka silalowa Ammi tace”ya Allah duk wanda ya rabani da ɗana kayi gaggawar mayarwa da wanda yayimasa aniyarsa”.
ta faɗa tare da fashewa da matsanancin kuka Hafsat da duktaji abinda yafaru taji tausayin Ammi yakamata ta share hawayenta takoma bedroom ba tare da Ammi ta luraba goge hawayenta tayi tare da kiran kuyangi tabasu umarnin tsara abincin taryar baƙin nasu.