HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Kaciɓus tayi da Fatimah na shirin futowa dukda ta ɗan razana amma seta dake tare da cewa”ƴammata dama yanzu gurinki nake shirin komawa saboda inason infara yimiki ƙarin karatu”.
“aiko Aunty kamar kinsan abinda yake raina dama jiya mantawa nayi naimiki magana nagode sosai”.
“aiba godiya a tsakaninmu”.
“eh dai dukda haka anjuma zansa a kawomana Zadul-Zaujain mufara “.
“toh Allah yakaimu”.
“Ameen”.
nan suka ɗunguma sukai falo suka zauna suka shiga hira inda Ammi tace”bara inje nima inshirya su Hajjo ana hanya”.
“kai amma naji daɗi Aunty sukazo gani kenan”.
“eh ku dubo kuka sunkusa kammala aikin abincin”.
“toh”.
nan suka tashi suka dubo sannan suka dawo suka zauna suka cigaba da hirarsu.

Suna cikin hira aka buɗe ƙofa Maryam ceta shigo tare da sakin murmushi taƙarasa har falon tazo gabda zata wuce wata Kuyanga tazo wucewa da glass cup da lemo a ciki yafaɗi inda lemon yaɗan taɓa gefen doguwar rigar jikin Maryam tasss kakeji ta ɗauketa da mari ta nunata da yatsa tace”ke wacce irin dabbace mara tinani bana hana bance in nataho naga ƙafar wata a cikinku sena karya ƙafar ba shine saboda tsabar raini shine zaki watsamun lemo zan koya miki hankali tinkiya mara daraja”.
dafe gurin baiwar tayi ganin wadda ta watsawane yasa ko zafin batajiba saboda tsoro murya na rawa tace”dan Allah kiyi haƙuri ranki shidaɗe tubanake bansan ze zubeba”.
“au ina magana kina magana ke wacece”.
tass taƙaramata wani marin tare da cewa”zaki gane kurenki kisameni a part ɗina anjuma”.
tausayin kuyangar ne yakama Hafsat tace”Maryam kiyi haƙuri bara na wankemiki gurin “.
murmushi Maryam tayi tare da cewa”Aunty ki kyaleni da ita basuda mutunci “.
“ya haƙuri dai ayimata afuwa”.
“to taci darajarki wuce sakarai kawai”.
Maryam tafaɗa tana mai gallawa kuyangar daketa kuka harara Fatimah da tayi shiru tayi kamar bata ga abinda yafaru ba Hafsat ce tace”to nagode”.
cikin kissa da kwarkwasa Maryam tace”ai bakomai Aunty kin wuce haka agurina kecefa babbar Yayarmu”.
“nagode”.
Hafsat tafaɗa tare da komawa kan kujera ta zauna kallon wannan kuyangar Maryam tayi tare da cewa”kin ɓacemun anan gurin ko senasa an saɓamiki kamanninki”.
jiki na rawa ta tafi itakuma ta nufi kujerar da Hafsat take.

Hafsat na lura da ita taɗan haɗe rai zama tayi tare da niyyar kamo hannun Hafsat matsar da hannun Hafsat tayi tare da cewa”washh nafama ciwonnan”.
Maryam da bata gane metake nufi bace tace”sannu Aunty”.
“yauwa nagode”.
“dama Aunty zuwa nayi idan kin iya kitso kiyimun”.
“toh bara nayimiki amma sede bame yawaba danse hannuna yayimun zafi”.
shu’umin murmushi Maryam tayi tare da cewa”nagode aini daman bansan manyan kitso”.
“toh”.
Fatimah dake gurin yitayi kamar batasan Maryam tazoba tanata chart ɗinta abunta kallonta Hafsat tayi tare da cewa”Fatimah asamomana kibiya”.
jin wani haushi Fatimah tayi rai ɓace tace”toh Aunty bara na ɗakko”.
nanta miƙe fuuu ta haye sama bata jimaba ta dawo murya a cunkushe tace”gashi”.
murmushi Hafsat tayi tare da amsa nan Maryam tabuɗe kwakuidon gashinta nan Hafsat tafara tsagawa jitayi Maryam tayi miƙa hammm tare da taɓamata ƙirji yi tayi kamar batajiba a haka suka cigaba da kitson da Hafsat tayi niyyar yimata kamar guda talatin jin miƙar da takeyi yasa Hafsa cewa a zuciyarta”amma wannan ko anyi sheɗaniyar yarinya bara kiga yadda zan muki guda goma zan miki maga ta iskanci”.
tana cikin wannan zancen zucin taji zata kuma miƙa tayi maza ta goce tayi kamar kibiyace ta ɓace Fatimah dake kallonsu dariya takusa suɓucemata zuciyarta tace”maganinki kenan Aunty”.
tana wannan maganar taji Hafsat tace”keko Maryam meke damunki kiketa miƙa haka”.
Maryam da idanunta suka ƙanƙance sukayi ja ce tace”hmmm Aunty kawai jikina ke ciwo”.
“toh gaskiya ki nemi magani”.
“toh Aunty”.
tayi maganar tare da yin nishi Hafsat ko jikinta har rawa yake tanata sauri tagama mata a daddafe taƙarasa mata ta tashi tare da cewa”bara naje nayi karatu namanta inada wata muraji’ah da banyiba”.
“toh Aunty se anjuma na dawo nima yanzu fita zanyi”.
“toh”.
nanta miƙe tare da kallon Fatimah ta wurgamata harara ta wuce Hafsat da harta haye upstairs tana ganin Maryam ta fita ta koma tare da sauke numfashi tace”wayyo Allah na kajini da sakaran yarinya zata ɓatamun tarbiyya”.
dariya sosai Fatimah tashiga yi harda riƙe ciki seda tayi me isarta har seda taga Hafsat tafara jin haushi sannan ta dena tace”bakeba nafaɗamiki halinta kin nuna bakomai ai gashi nan tafara nunamiki halinta to wannan da kike gani kaɗan ne daga cikin halinta wlh bakiga komaiba bake me ƙanwar mijiba kina sakarmata fuskaba”.
“to ai yanzu takau kajini da sheɗaniyar yarinya Allah ya shiryeta yasata gane gaskiya”.
“ameen”.
Hafsat na niyyar magana sukaji sallamar Hajjo tace”salamu Alaikum”.
da gudu Fatimah ta ruga ta rungumeta tare da cewa”oyoyo Hajjo sannu da zuwa “.
“ja’ira zaki kadani yauwa muje”.
nan suka ƙarasa gurin Hafsat zama Hajjo tayi itakuma Fatimah da gudu ta haye stairs dan faɗowa Ammi .

Hafsat ce ta duƙa har ƙasa tace”Ina yini “.
Hajjo faɗaɗa murmushinta tayi tare da cewa”lafiya ƙlau kishiyata da kika kwacemun mijina”.
murmushi Hafsat tayi tare da yin ƙasa dakai tace”ya hanya”.
“Alhamdulillah tashimana ɗiyata kizauna”.
“a’ah Hajjo nanma ya isa”.
“to ai shikenan”.
Ammi ce suka fito tare da Fatimah nan Ammi suka shiga gaisawa nansu Fatimah suka basu guri Ammi cetasa aka cikawa Hajjo gabanta da kayan mitsa baki irin nasu na masarauta kaɗan taci sannan aka kwashe Hajjo ce ta kalli Ammi tace”Aminiyata naji kince da matsala Allah dai yasa lafiya”.
“wlh kuwa Hajjo ba lafiyaba dazunnan nakira me sunan Malam na sanarmasa da aurennan buɗar bakinsa se cewa yayi wlh baze dawoba kancinme za’ah rasa wanda za’ayiwa aure seshi aurenma kuma ƴar Nigeria baƙauya marasa ilimi da wayewa a dubeshi duk class ɗinsa shi za’ayiwa wannan cin mutunci daga ƙarshema ya kashemun waya”.
taƙarasa maganarta cikeda tsananin damuwa sauke numfashi Hajjo tayi tare da cewa”Innalillahi wa’innah ilaihirraju’un gaskiya dole kice akwai matsala nima kina faɗamun seda nayi tinanin ƙila shine bazeyiwu mu zama ƙananan mutaneba kirabu dashi yanzu inbanda abinshi wlh kafinyasu mace me kyawun Hafsat da iliminta da aiki wlh kinsan wani abu aminiyata meze hana mu maidata makaranta tacigaba da karatunta a koyamata girki da ayyukan gida ta goge zesha mamaki”.
murmushib Ammi tayi tare da cewa”gaskiya Aminiyata naji daɗin shawarar nan taki haka ko za’ayi zesha mamakin baƙauya kuwa tare zasu tafi higher insitution da Fatimah ze gane kuransa”.
“toh kingani karki ƙara tayarmasa da zancenma”.
“aiko dai haka za’ayi”.
Hafsat da Fatimah dasuke sakkowane sukaji abinda Hajjo tacene Hafsat tayi kamar bata ganeba a zuciyarta tace”hmm baƙauya mara ilimi mara wayewa dukni kaɗai”.
tana wannan zancen suka ƙarasa main falo suka zauna.

RUGAR RUMADA

Tunda aka tafi da Hafsat Iyah keta tsiya dakyar tabari aka kakkai amare gidajensu zaune Ummita take tana tsintar wake Aminu na tayata Bappah yashigo bakinsa ɗaukeda sallama amsa masa tayi tare da miƙawa Aminu farantin duka tace”kacigaba ina zuwa inka gama ka wanke ka zuba”.
“toh Ummita sena tino da Hafsat da yanzu itace ke yin wannan aiki”.
murmushi Ummita tayi tare da cewa”eyi Allah sarki ɗiyar Albarka kome takeyi oho Allah ya tsaremunke daga sharrin masharranta”.
“Ameen”.
nanta bi bayan Bappah samunshi tayi yayi tagumi harta zauna besan ta zaunaba seda ta taɓashi firgigit ya kalleta cikin damuwa Ummita tace”meyake damunka mijina banason ganinka cikin damuwa komai yayi zafi maganinsa Allah kakoje ka gaida Iyah kuwa”.
“wlh so nake nakoma amma ƴan kuɗin hannuna bazasu isheni nakoma ba shine narasa yadda zanyi banjeba kinsan dai konaje bazata kulaniba gwarama na tafi na huta da wannan baƙar rayuwar”.
cikin kwantar da murya haɗida sace zuciya Ummita tace”todon wannan kake damun kanka kwantar da hankalinka ɗazu Aminu daya dawo daga aikin rifin ɗaki da aka basa sallamarsa shine yabani dubu uku gata nasan zata isheka”.
murmushi yayi tare da cewa”Allah nagodemaka daka bani mace tagari me kwantarmun da hankali idan nashiga damuwa Allah yayimiki Albarka nagode sosai”.
“ninafi kowa sa’ah da Allah ya mallakamun miji nagari mesona dan Allah kajeka gaidata kasan iyaye ba abin wasa bane”.
taƙarasa maganarta cikeda shagwaɓa murmushi yayi tare da cewa”toh bara naje”.
“seka dawo”.
“toh”.
nanya tafi abinsa yayinda sonta yake ƙara ƙaruwa a zuciyarsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button