HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Tarar da Iyah yayi tana yafa ilajonta zata fita tana ganinshi ta haɗe girar sama data ƙasa murmushi yayi tare da cewa”Iyah unguwa zakine”.
cikin masifa tace”eh lafiya”.
“eh lafiya ƙlau zuwa nayi nagaidake”.
“nina faɗamaka muddum bakaje kasa an raba aurennan anmaidashi kan Fatimah ba karka ƙara gaidani “.
murmushi yayi tare da cewa”toh Iyah zanje gobe insha Allahu ki kwantar da hankalinki””.
“yauwa yaron arziƙi aradu inko kayimun haka shine zansan nahaifi ɗanda Jamilah bata shanyemunba ya kuɓuta daga sharrinta aidama nasan za’ai haka domin tunda naje gidan Malam nakan tudu yafaɗamun hakan”.
“hakane kam Iyah bara nabarki kitafi”.
“toh bara nayi sauri gidan waccan maciyyar amana itama zanje nacimata mutunci kamar yadda ta kwancemun zani a kasuwa nima na kwancemata”.
murmushi Bappah yayi tare da cewa”toh sskin dawo “.
nanta tafi baki buɗe tanata shimasa albarka koda taje gidan Hansai tasamu bata nan se juyowa tayi tana cewa”ai komun daren daɗewa zaki dawo zakisanine aradu”.
HAFSAT POV
8:30pm
Zaune suke a wata ƴar rela tashan iska kowanne riƙeda Alqu’ani yayinda Hafsat ke rero karatun Alqur’ani megirma cikeda kwarewa suratul Muhammad yayinda itakuma Fatimah tana kallon Alqur’anin da alama dai ƙari takeyimata wani haɗaɗen ƙanshine yakaiwa hancinsu ziyara ɗaga kan da Hafsat zatayi tayi kaciɓus da!!!!!!
Dan Allah duk wanda yakaranta yayima mahaifiyata addu’ar samun lafiya da musulmi baki ɗaya nagode.
Tallah! Tallah!! Tallah!!!
Ina masoyana na haƙiƙa kufito ku nunamun ƙauna ta hanyar siyan paid book ɗina wato BAR RAINA ALLURA (Itama ƙarfe ce) cikin farashi me sauƙi #200 ta wannan account number 2411022356 Aisha Ibrahim Zenith Bank aiko da shedar biyanka ta wannan number 08108362334 ko kuma transfer vtu ta wannan number 08108362334 .
Votes and Comments
Plz share
_*Daga Alƙalamin ƴar Mutane???? *HASKEN RAYUWATA*
MALLAKIN
REAL EESHOW
HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION
PAGE 2️⃣3️⃣➡️2️⃣4️⃣
Wani haɗaɗen handsome guy lokaci ɗaya taji wani irin faɗuwar gaba domin kamarsu ɗaya da F2 ƙasa tayi da kanta tacigaba da biyawa Fatimah tana amsawa cikin takun ƙasaita wanda ke nuna cewa shiɗin jinin sarautane yaƙarasa inda suke inda Fatimah ɗaga kan da zatayi sukayi ido huɗu dashi buɗemata hannu yayi inda itakuma da gudu ta ruga ta rungumesa wani mamakine yakama Hafsat dake zaune a zuciyar ta tace"anyako wannan Farouk ɗinda ake faɗane me zafin kannan kuwa wannan naga yana murmushi anya".
tana wannan zancen ta ɗaga ido aiko idanunsu yafaɗa cikin na juna saurin ɗauke idanunta tayi tare da yin ƙasa da kanta shiko anashi ɓangaren jiyayi wani irin yarrr tsigar jikinsa ta tashi a zuciyarsa yace”masha Allah ashe a duniya akwai kyawawan mata kamar wannan tsarki ya tabbata ga Allah aiko in hakane nasamu matar aure bara naƙarasa nayimata magana kai amma Babyn nan ta iya ƙira’ah nifa kakata ta yanke saƙa dama 9ja akwai irin wa’innan amma ni bantaɓa ganiba ko a ina Fatimah tasamota oho aini nasamu matar aure dan wannan bazan taɓa gajiya da kallontaba to idan kuma ansamata ranafa wata zuciyar tace ko ansamata rana dole a warwareta koda uban waye dan inka tsaya garin kallon ruwa kwaɗo zema ƙafa”.
duk wannan zancen da yake idanunsa nakan Hafsat da tayi ƙasa da kanta shiko yakasa ɗauke kansa daga kallonta seda yaji Fatimah data rungumesa tace”Yayah tinanin me kakeyine haka ne”.
firgigit ya kauda kansa daga kanta yahau sosa ƙeya alamun yaji kunya yace”bakomai sweetheart mekika gani”.
murmushi Fatimah tayi tare da cewa”ok to bara na ɗakko maka kaima chair”.
“toh kamar kinsan dama a gajiye nake nashiga ciki akace kina nan”.
“wlh kuwa ƙari akemun”.
wani ƙasaitaccen murmushi yayi tare da satar kallon Hafsat yace”ok bara na ƙarasa na zauna a kujerarki nima ayimun”.
“toh”.
nanta tafi abunta shikuma yafara tafiya inda tinkan yaƙarasa gurinta kanshin turarensa yakaiwa hancinta ziyara lokaci ɗaya ta lumshe ido saboda wani yanayi data tsinci kanta me wuyar fassaruwa a zuciyarta tace”amma kuma ai F2 bayasa manyan kaya sena ƴan iska tsayadai muga ikon Allah”.
nan taita sake-sakenta .
Cikin takun zaratan maza masujida class yaƙarasa gurin Hafsat zama yayi akan kujera tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sauka Hafsat tayi daga kujera ta tsugunna cikin girmamawa tace”inayini”.
jiyayi lokaci ɗaya nefarsa ta ɗauke yayinda ya lumshe lulu eyes ɗinsa ya saukesu akanta a zuciyarsa yace”kai dolema na mallaki Babyn nan komai kin tara ga tarbiyya nasameta aina more komai nata yayi Allah kasa idan nasanar da ita ta amshi tayina cikin sauri”.
jin datayi yayi shirune yasa a zuciyarta tace”ke meya kaiki bayan kinsan ba lallai bane ya amsa inbandama bakida zuciya yacemiki baƙauya mara ilimi mara wayewa harkike wani gaidashi koda yake kinfishi koba komai gaba yake dake meye a ciki”.
tana kai nan ta saki wani murmushi wanda ita kaɗai tasan ma’anarsa taƙara cewa”Ina yini”.
murmushin nan datayi jiyayi taƙara kashe masa zuciya murmushin shima ya mayarmata tare da cewa”lafiya ƙlau My Queen”.
mamakine yakama Hafsat yayinda shikuma ya ɗagamata gira alamar yes komawa tayi ta zauna kan chair murmushi yayi a zuciyarsa yace”yanzu yakamata na faɗamata sirrin zuciyata tunkafin Fatimah ta dawo”.
sauke numfashi yayi tare da cewa”My Queen nima a biyamun”.
ta buɗe baki da niyyar magana sukaji sallamar Fatimah shiru tayi tare da cewa”kin wani tafi kin daɗe”.
murmishi Fatimah tayi tare da cewa”sorry my Aunt”.
“hmm”.
kallon Fatimah yayi tare da cewa”nifa sonayi kafin nafara ganin kowa nafara ganin Aunty tashi muje naganta”.
Murmushi Fatimah tayi tare da cewa”Yayah ga Auntyn nan ai Aunty ga Yayah Abdallah dayake Saudia gidan Aunty Fido aiki yakeyi a Jami’ar Madina”.
damm gaban Abdallah yabayar lokaci ɗaya gumi yafara tsatstsafomasa a zuciyarsa yace”innalillahi nakusa yin abun kunya ashe matar Hamma Farouk ce ni harda cewa Queen bazan taɓa son abinda ɗan uwana yakesoba hakanma nayi a cikin rashin sani wata zuciyar ce tace to yanzu kenan gwara ka rasata kenan kake nufi wata zuciyar ce tace to meye a ciki kome nayiwa Hamma Farouk ban faɗiba saboda duk abinda nakeso shiyakemunshi anyako za’ah samun ɗan uwan daya fifita rayuwar ƴan uwanshi akan tasa dolene nima na taya su Ammi wannan yaƙin”.
a fili kuma murmushi yayi tare da kallon Hafsat yace”Auntynmu ashe kece wlh naɗauka ƙawar Fatimah ce”.
Hafsat da tacika da mamaki ce tace”Allah sarki nima banyi zaton kaineba ya hanya anzo lafiya”.
“lafiya Alhamdulillah yazaman baƙunta “.
“Alhamdulillah”.
a zuciyarta tace”haba nifa ince shida akace ko dariya bayayi kullum rai a chuɗe”.
nan suka cigaba da karatu inda yayita yimata tambaya akan addini yaji itama ba dama itama gwanace.
Washe gari da safe Ummita na gyarawa Bappah jakar daze tafi da ita yashigo tare da kallonta fuskarsa ɗaukeda murmushi yace”ƴar Aljanna kenan wato kafin inje in dawo har kin haɗamun kaya”.
“eyi inban haɗamakaba waze haɗamaka masoyina kaje ɗakin Lantana ko”.
“a’ah bara naje”.
“toh”.
nan yafita ya nufi ɗakin Lanta tinkan yaƙarasa wari yafarayimasa sallama harya isa ɗakin cikin dauriya yashiga kallon kwanuka yayi batsa-batsa dukba wanki kaya can kaya nan ko ina ba kintsi gata zaune daga ita se bra da daurin zane a ƙugu kai buɗe kamar guiwa anata cin tako ana hura iska alamar yaji ko kallonsa batayiba sema sosa kanta datayi cikin takaici Bappah yace”Lantana bakiji sallamata bane?”.
“eh naji se akai yaya ko nono zanbaka da se lallai na amsa inace kunne kejidai ko to naji”,.
“Lantana ni kike faɗawa haka”.
“eyi indai bazaka dena nuna banbanci tsakanina da wannan karuwar matar takaba tonima bazan dena yimaka abunda nakemaka ba aradu koda yake ashefa shanyeka akayi “.
shiru Bappah yayimata saboda takaici seda yakai zuciyarsa nesa yace”tafiya zanyi”.
“toh asawowa Isah kekenshi da aka haɗa baki a barmasa tsura ehe”.
cikin takaici ya fita yashiga ɗakin Ummita bejimaba suka fito tare suna murmushi zata rakashi seda suka isa gaban ɗakin Iyah sannan Larai tace”aiko bata daɗe da fitaba tace kajira tazo”.
“toh “.
nan suka koma ɓangarensu gwanin sha’awa.