HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Tana isa gurin Haladu me shayi ta haɗe ranta tace”abani breadi na hamsin”.
taƙarasa tana mai miƙamasa kuɗin caraf taji ya kamata hannu saurin warɓar da hannunshi tayi kamar ta taɓa wani abinƙin cikin masifa tace”inkai ɗan iskane niba irinki bace kaje can ka nemi irinka wadda batasan mekemata ciwoba”.
fuu ta wuce da niyyar tafiya Haladu yasha gabanta tare da cewa”wato ke dandin naki da ƴan birni kike kenan masu kuɗi ki kwantar da hankalinki zanbaki jaka biyu kuma kullum kizo ki anshi brodi da soyayyen kwai kyauta”.
tsaki tayi tare da nunasa da yatsa tace”aini ko abinda nakeyi kenan bazanyi dakaiba dubeka duguja dakai shasha”.
nuna kansa yayi tare da cewa”aradun Allah zakisan kincimun mutunci ne karuwa kawai”.
fuu ta wuce ta shiga dannin dake jikin ƴar rumfar shayin nasa tana shiga tayi sallama aɗan daƙile suka amsa gaidasu tayi tace”abani kwaki na ashirin sugar na ashirin gyaɗar goma”.
“toh”.
wata mata ta faɗa tare da amsar kuɗin tashiga ɗaki bata jimaba segata tafito ta bata ta tafi.
Tana isa gida ta jiƙa kwakinta tafarasha tana gamawa tashiga koyawa Yayanta karatu suna cikin karatu sukaji yaran gidansu suna murnar Bappi yadawo tashi sukai cikin sauri suma sukai waje har Ummita itama dake koya itama suna fita suka ganshi a tsugunne bakin ƙofar Iyayenshi tsaitsaiye ƙarasawa sukai Hafsat ta rungume mahaifin nata cikeda shagwaɓa tace”sannu da zuwa Bappana”.
wata uwar harara Iyah ta bankamata uwar harara yitayi kamar bata ganiba murmushi Bappa yayi tare da cewa”yauwa ƴar albarkar Bappanta Aminu jeka waje ka shigo da keke”.
“toh Bappa”.
nanya tafi matan ƙannen yayyen Bappi ne sukaita zuwa suna gaidashi itako Lantana tanajin Bappa yace a shigoda keke tashi washe baki nan kowa na babban gidan yafito anata murna da dawowar Bappa shigowa Aminu yayi da keke sabo blue babbah mekyau yakaishi bakin bishiya yajingine ya ƙarasa gurinsu Bappa ya duƙa yace”Bappa gashinan”.
“toh ƴar Bappanta ga tsarabarki nan na siyomiki danya sauƙaƙamiki gurin zuwa makaranta”.
rungume Bappa taƙarayi cikin murna tace”amma Bappa nagode sosai kamar kasan in natafi da safe ina daɗewa yanzu bansamu abin hawaba wanibinma har makara nake Allah yaƙara buɗi”.
“bangane ita ka siyowaba baze yiwuba naɗaukama Habu ka siyowa”.
“wlh kuwa Iyah”.
“ke dena duba kekennan dan ba nakibane bare aji daɗin zuwa karuwanci na Iro ne”.
washe baki Lantana tayi tare da kallon Ummita datayi kamar batamasan abinda ke faruwaba jin Bappa sukai yace”haba Iyah nasiyomata ne danya sauƙaƙamata tafiya gurin karatunta bawai dan wani abun ba”.
“kai da’Allah can rifemun baki sakarai wanda aka shanye to aradu bari kaji infaɗama inkai anshanyeka toni ba’ah shanyeniba cakake tuntini bamusan karuwanci yarinyar takeyiba da zaka wani rainawa mutane hankali wai wani karatu take zuwa karatomato shasha”.
zeyi magana Ummita ta girgizamasa kai shiru yayi nanya rarraba tsaraba yabama kowa yakoma wajansa sannan ya kwashi na Iyalinsa sukai ɓangarensu koda sukaje yaraba yaba kowa nasa rai ɓace yashiga ɗakin Ummita ya zauna tare da cewa”wash ɗiyar kirki zo”.
murmushi Ummita tayi tare da cewa”mijina kadena damuwa inda sabo yaci ace ka saba kadena ɓacin rai domin Iyah uwace a garemu ta isa damu bare kuma kayanmu”.
“eh nasan ta isa amma ai nayimata bayanin saboda insauƙaƙawa yarinya tafiya na siyo dama ƴan kuɗin dana samo suna ƙundige na siyo ya za’ai ayimun haka fisabilillahi”.
Lantana dake raɓe jikin ƙofa ce ta wuce da sauri ta nufi ɓangaren Iyah da gudu tana haki Iyah dake zage zogala ce tace”lafiya Lantana kike haki haka”.
tana nishi tace”yanzu ina raɓe naji tana cemishi wai shiya kyaleki kikemasa duk abinda kikaga dama ai kuɗinshine yadena daka ta taki”.
aje zogalan Iyah tayi tace”kujini da tsinanniyar yarinya muje dan ubanta”.
nansuka nufi ɓangaren Bappa suna shiga sukaji Ummita na cewa”ka kwantar da hankalinka ta isa damu ne wata rana se labari muyita haƙuri har a rabu lafiya”.
bankaɗa labule Iyah tayi tare da cewa”karya kwantar da hankalinshi ya mutu inyana iyawa kajini da ƴar iskar yarinya mara mutunci ni zaki riƙa cewa shiya kyaleni nakemasa duk abinda naga dama wai ya dena daka ta tawa aini bazaki birgeniba tunda baki isa kinzo gabana kinmunba duk rashin kunyarki sede kiyi ta bayan ido kaikuma dake bakasan ciwonaba shine hartake faɗamaka haka baka ɗau matakiba”.
“wlh Iyah bance hakaba kiyi haƙuri”.
“rifemun baki munafuka nidai nafi ƙarfin a shanyeni wuce mutafi Lantana”.
harar Lantana Bappa yayi danyasan ita taje ta haɗa wannan gulmar suka fita Hafsat dake duba littafinta ce taji iyayen nata sunbata tausayi a zuciyarta tace”kai wannan gida namu ko yaushe zegyaru su Iyah su gane gaskiya oho Allah ya shiryesu”.
kama hanun Ummita Bappa yayi tare da cewa”kiyi haƙuri kinji matata”.
murmushi Ummita tayi tare da cewa”bakomai ai mahaifiyarmu ce Hafsa ɗakkowa Bappanki abincin dana haɗamasa “.
“toh”.
“zo Hafsat”.
cewar Bappa ƙarasawa tayi gurinsu ta duƙa tace”gani”.
“kiyi haƙuri kinji in Allah yakaimu natashi dawowa zansiyomiki wani keken”.
“bakomai Bappa Allah yabuɗamaka”.
“amin ɗiyar Bappa”.
nanta tashi tashiga uwar ɗaki dan kawomasa abinci ganin yadda bata wani damuba ne yasa yaƙarajin tausayinsu yakamashi dan baƙaramin haƙuri sukeda Iyah da mutanen gidanba yana wannan tinanin yaji motsi gani yayi harta aje abincin ta juya Ummita na zubamasa nanya bata tsarabarsu Billy yafara cin abinci suna hirar yaushe gamo.
Washegari Hafsat na idar da Sallar asuba tayi azkhar ta nufi ɓangaren Iyah tana zuwa tagaida ita ko amsata batayiba ta fita waje ganin haka yaba Hafsat dama ta gyara ɗakin Iyah tsaf kallon gado me rumfar Iyah tayi taga ta gyarashi tsaf wani tunani ne yazomata tace”tab Iyah tazo ta sameni akan gadon nan na kaɗe dadaisu Furerane har kwanama insunga dama sayi”.
tana wannan zancen taji muryar Iyah nacewa”inma wani abun kikasamun Allah yafiku”.
da sauri ta ɗauki tulun ruwa ta nufi rafi seda tayi sawu biyar tacikawa Iyah komai nata sannan tayimata abubuwan data saba sanna ta nufi ɓangarensu nanma tayi shara ta share ɗakinta ta ɗauke shimfiɗarta tashiga wanka tasaka kaya cikin sauri ta shirya ta nufi ɗakin Ummita zaune ta sameta kan tabarmar kaba tana lazumi ƙarasawa tayi gurinta ta gaida ita faɗaɗa murmushinta tayi ta amsa tare da cewa”ga koko nan na ɗuramiki a laba kitafi dashi kin ebo kayan Islamiyyar daiko”.
“eh na aje a waje ina Bappa”.
“yaje gaida Iyah ga ɗari yace abaki”.
“toh angode nina tafi”.
nanta amsa ta tafi ta ɗauki uniform ɗinta ta tafi kamar jiya seda tasha uwar tafiya sosai sannan ta fita titi a titinma seda ta daɗe batasamu abin hawaba dakyar tasamu maleji tashiga suka nufi Gwarzo.
Tana sauka cikin sauri ta nufi Islamiyyarsu dake quartaz domin ta makara tana isa ta tadda M. Jalaludeene a ajinsu yana koya musu Basic science a sanyaye tayi sallama dantasan bayan bari inya shiga wani yashiga abin mamaki setaji ya amsa sallamarta tare da cewa”Moniter karki ƙara makara jeki zauna”.
“toh nagode Malam”.
haɗa ido sukaida su Billy suka sakarma juna murmushi taƙarasa seat ɗinsu ta zauna.
Tana zama ta zaro littafinta suka cigaba da note ɗinda yakemusu yana ajewa suka aje yashiga yimusu bayani akan Metabolism yafita domin ankaɗamusu break kallon juna sukai tace”ammafa nayi mamaki da Malam ya kyaleni”.
“muma haka wlh ai dandai yasan daga nesa kikezuwa kuma baƙaramin mutuncinki yake ganiba shiyasa”.
“kunsanko yadda naji danaga shine a class ɗinmu kuwa ga tsarabarku inji Bappi”.
ta miƙamusu choculate a leda baƙa cikeda murna suka amsa suka buɗe suka hausha Zully cetace”ke Billy bakince idan Hafat taƙaraso zaki nunamana wani abuba to ai gata tazo”.
“au to bara in nunamuku amma kibari mugama shan koko ga yam ball ɗinmu mufaraci “.
“toh”.
nan suna shan koko da Yam ball suna hirarsu har suka gama sannan Billy tace”ku rife idonku harsena ce kubuɗe”.
“toh”.
nansuka rife ta zuge wata jaka ta fito da wata system me kyau tashiga operating ɗinta sega wasu haɗaɗun gients guys sun bayyana masuji da kansu murmushi tayi tare da cewa”kubuɗe idonku”.
a hankali suka buɗe idonsu kan sabuwar system ba tare da sun lura da abinda ta nunomusu ba suka haɗa baki gurin cewa”wow wannanfa”.
farr Billy tayimusu da ido tare da cewa”eyi jiya ina komawa na tarar Yayanmu ya siyomun”.
“kai gaskiya mun taya murna sosai”.
“ameen ƙawaye na gari bakuga menake nunamuku bane a cikinta”.
taƙarasa zancenta tare da nunamusu wa’innan guys ɗin cikin sauri Zully tace”wow a ina kikasamo wa’innan haɗaɗun mazajen haka musamman ma wannan”.
dariya Billy tayi tare da cewa”watarana ina cikin duba wayar Yayanmu naga hotunansu a Istagram suna yawo aiko shine nikuma da Yah Munir ya siyomun system senayi download ɗinsu dan na nunamuku kunsanni da son abu mekyau”.
“kai amma sunyi kyau bara na daɗa ganinsu ammafa wa’innan duniya ne “.
“wlh kuwa kewai Hafsat yanaji kinyi shirune wani abun ne yafaru”.
“bakomai gani nayi kunata hauka kan wa’innan arnan banzan ina wani abinso ga wa’innan”.
sakin baki sukai suna kallonta ɗagamusu gira tayi tace”Allah ni banga abinso a wa’innan marasa ajinba”.
“lallai Hafsat anyako ba idanunki sunfara samun matsalaba kuwa kiga wa’innan haɗaɗun guys ɗin kice wani abu musulmaine fa”.
ware ido Hafsat tayi tare da cewa”da gaske tab a hakan jikinsu duk zane barama nina duba sunayensu”.
nansuka fara da wani haɗaɗen guy fari tas dashi Hafsat dake ƙoƙarin aje pencil ɗinta ce tayi arba da!!!