HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

IYAH POV
Suna shiga gida Iyah ta tarar da Furera na shirin shiga tana kuka ko mayafi babu kwaɗamata mari Iyah tayi tare da cewa”kekuma indo tafi ɗakin uwarki bara inje gurin Lantana inji in itace tasaka yarinyar nan ta ɓatamun suna”.
“toh”.
nanta tafi Iyah ko ta tangaza ƙeyar Furera sukayi ɓangarensu suna shiga suka samu Ummita na dama kunu a ɗan kitchen ɗinsu na langa-langa cikin takaici Iyahta kalleta tayi tsaki yau zanje a karyamun duk jifan da mutum yayowa jikokina saboda rashin tsoron Allah ace mutum ba tsoron Allah kamar kafiri zanyi maganin mutum dan sawa zanyi a mayarmasa da aniyarsa yaji yadda akeji”.
murmushi Ummita tayi ba tare data ɗagoba har Iyah ta gama habaicinta ta tafi suka nufi ɗakin Lantana.

Tundaga waje Iyah kejin wari har suka isa ɗakin ƙazanta kala-kala a ɗakin dukda irin kyamar da Iyah keji haka ta daure tace”sirri nazo muyi dake banason waccan tsinanniyar taji “.
Lantana dake ɗinkin hula ceta ture wasu kaya tace”zauna inajinki”.
tafaɗa a wani wulaƙance rakuɓewa Furera tayi tanata kuka cikin ɗari-ɗari Iyah ta zauna tare da cewa”Lantana ke kikasa waccan munafukar taje ta zubarmun da kima a idon jama’ah”.
saurin yadda hula Lantana tayi cikin rashin kunya tace”keeh Iyah nafiki iskanci wato abun naki ya wuce kan kowa kaina ya gangaro kenan to kinyi kaɗan ke har wani mutunci gareki dama a rugar nan”.
tass Iyah ta ɗauke Lantana da mari tare da saurin fita daga ɗakin tana kwarma ihu tana cewa”wayyo Allah na kufito yauga mahaukaciya zata illatani”.
itakuma Iyah tayi hakane dan ganin yadda Lantana ta zabura tayi kanta zata iyayimata wani abun kafin kace meye wannan kowa na gidan yafito harsu Ummita da Bappah nan Lantana tace”ni kika mara aradun Allah duk iskancinki nafiki kajini da munafukar tsohuwa nafiki bala’i “.
bata ƙarasaba Bappah ya ɗauketa da mari yace”mahaifiyatace fa wato abunma yabar kaina yakoma kan mahaifiyata”.
“eh ɗin ammatan ita bataji kunyar cewa ninasaka yarinya yin cikin shegeba seni zanji kunyarta aidama ance in tsoho beji kunyar hawa jakiba haka shima jaki bazeji kunyar kadashiba kumama ai in ɓata yarinyar ne tare muka ɓatata kajini da tsohuwar najadu”.
tass Bappah yaƙara ɗauketa da mari a zafafe yace”kije gidanku na sakeki saki uku kuma kitafi da ƴaƴanki banga wani mahaluki da zezo ya wulaƙantamun uwaba har gida ina kallonsa ba”.
“gwara da kayiwa tsinanniya da bata gaji arziƙi haka yarinya na ɗakkoki daga rana na kawoki inuwa ki watsamun ƙasa a ido”.
a ziciyarta ko cewa take”dama waccan tsinanniyar ce mara asali tayimun haka ya saketa”.
“eh najin kuma ba inda zani da yara domin badasu nazoba anan nasamesu”.
“doleko ki tafi dasu”.
cewar Bappah Ummita da bata tofa ko alifun bace tace”aiba dasu tazoba kabarsu baka kyautaba aiko darajar yaranta taci”.
“rifemana baki tsintattar mage”.
cewar Iyah data makawa Ummita harara nantaja bakinta ta tafi yayinda Bappah ya rife Furera da faɗa lallai seta faɗi inda tasamo cikin jikinta itakuma tace”aradun Allah Bappah na Haladu ne”.
zasuyi magana sukaji muryar mahaifiyar Haladu tace”ƙarya kike ja’irar banza kinemi wanda yayimiki tunkan dare yayimiki dan baki baki isa kin ɗorawa ɗanaba”.
“yanzu kenan Zuwaira duk bin matan ɗanki harkike iya buɗar baki kice banashi bane kijira yazo aji”.
“na buɗi bakin aigashi tare muke kai Haladu kainkayiwa Furera ciki?”.
Haladu ne ya kalli Furera da itama shi take kallo tana kuka yace”ƙarya takemun aradu ita tasan wanda yayimata abinta dan haka ta nemi wanda yayimata”.
Furera ƙara fashewa tayi da kuka tace”yanzu nan Haladu abinda zakayimun kenan kainefa kayimun”.
“ƙarya kikemun ni”.
nan sukaita rantse-rantse daga ƙarshe Haladu ya furje bashi bane nan uwarshi ta tasashi suka tafi nan itama Lantana ta haɗa inata- inata ta tafi kan Bappane yafara saramishi tsabar baƙin cikin abinda Furera tayi dafe kansa yayi Ummita takamashi da niyyar tafiya Iyah tace”kema da kike wani fifila ashe ƴar takima bawa ta aura ba ɗan sarkiba “.
murmushi Ummita tayi ba tare da tace komaiba takamashi suka shiga ɗaki nan Iyah taita zagin Furara sannan takoma kan uwar indo itama tayimata tatas sannan ta wuce.

Sosai Ummita tashiga kwantarwa da Bappah hankali haryaji yadenajin ɓacin ran da yake ciki tace”ka kwantar da hankalinka komai a hankali ake binsa zan saka Furera ta faɗamun wanda yayimata cikin jikinta”.
“toh Allah yasa amma wallahi duk Iyah ce ummul-aba’isin faruwar komai da bata ɗakkomun Lanatana ba aida duk haka bata faruba kiduba ki gani tare da Hafsat nasaka Furera makaranta amma seda Lantana tasan yadda tayi ta cireta tamaidata tallar rogo ta kuma maƙalawa Hafsat cewa wai iskanci take zuwa ba wata makaranta”.
“eh dukdai da haka haƙuri zakayi komai me wucewane watarana se labari”.
nan tayita lallaɓarsa harya kwantar da hankalinsa.

8:30pm
Zaune suke sunata hira gabaki ɗayansu sega Abdallah yashigo tare da cewa”salamu alaikum yau wunin yau banga babbar Auntynmu ba”.
murmushi Hafsat tayi tare da cewa”nima dai tin da rana naketa zuba idon ganinka naji shiru ai gani ɗan ƙanena”.
murmushi yayi tare da ɗaga kansa ganinsu Billy yayi suna murmushi kasa ɗauke kansa yayi daga kallon Billy dakyar ya ɗauke idonsa tare da cewa”Aunty kace baƙi mukayi ba labari”.
yafaɗa haɗeda sosa ƙeya yaƙarasa kusa da Hafsat ya zauna murmushi Hafsat tayi tare da cewa”eh wlh Abdallah manyan aminaina ne sukazo kawomun ziyara”.
“kice Aunties ɗinmu ne kenan sannunku”.
“yauwa ina yininka”.
“lafiya ƙlau”.
nan suka gaisa Abdallah ya miƙe tare da cewa”Aunty nizan tafi da magana saboda banason waccan ƴar sa idon taji”.
yafaɗa haɗeda kallon Fatimah itako Fatimah dariya tayi tare da cewa”intayi wari maji duk ɓoye-ɓoyen mutum”.
“badai zakiji wannanba sirri zamuyi da ɗan ƙanina”.
nanta miƙe suka fita yayinda su Billy keta santinshi suma da farko sun ɗauka F2 ne seda sukaga sumar suka tabbatar dabashi bane .

Suna fita Abdallah yace”gaskiya Aunty naga wani diamond kuma yayimun inafatan babu meshi”.
murmushi Hafsat ta faɗaɗa a zuciyarta tace”Alhamdulillah Allah yasa yace ze auri ɗaya daga cikinsu kaga shikenan “.
a fili kuma setace”bangane diamond ba Abdallah”.
sosa ƙeya Abdallah yayi tare da cewa”Aunty a cikin ƙawayen can naki ina me golden ɗin doguwar rigar nan itace gaskiya ta kwantamun shine nakeson ki shigemun gaba dan nasan suma irin halinki garesu”.
murmushi jindaɗi Hafsat tayi tare da cewa”aiko dai ɗan uwa zan shigemaka ammafa bata da waya kamarni itama haka take”.
“to ai ba matsala gobe semuje shopping a siyamusu danke nasan Ammi tabayar a siyomiki “.
“toh shikenan Allah yasa matarkace yasa Albarka a tsakaninku”.
“ameen Aunty amma baki faɗamun sunan taba”.
“au naɗan shafa’ah sunanta Bilkisu”.
“tnx my Aunt”.
nan suka ɗanyi hira sannan takoma ta faɗama Billy abinda yafaru murmushin jindaɗi tayi tace”amma dai baki kwafsamun ba daiko danni inasonshi”.
“a’ah ni ban kwafsamikiba sema jindaɗi danayi”.
“aidama nasan tatsunniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi cewa zeyi yanason ɗaya daga cikinsu Aunty Billy harda wani cemun ƴar sa ido”.
dariya duk sukayi Hafsat tace”au namanta sirrine da banbari kinjiba”.
“aidai naji”.
nan sukaita dariya suka cigaba da hirarsu.

AFTER ONE DAY

Fitowa suke daga wani katafaren gurin shopping suka shiga mota ma’aikatan mall ɗinne suka fito da kaya niƙi-niƙi suka zuba a boot ɗin motar Abdallah nan boot ɗin ya rife kansa kallon Billy yayi data wani hakimce a gaban mota yace”sweetheart dan Allah idan kinje kina zuwa ki kunna wayar dukda akwai sims a ciki”.
“toh shikenan My “.
Hafsat ce tace”gyara kintsi dani dai Abdallah”.
sosa ƙeya yayi na yaja Land cruser sa suka nufi Gwarzo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button