HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Koda suka isa gidansu Zully suka fara zuwa suka shiga har ciki suka ajemata abin arziƙin dasu Ammi da Abdallah suka basu sannan suka nufi gidansu Billy nanma seda su Hafsat suka shiga suka gaida mamansu sannan suka ajemusu tsarabar suka fito suka shiga mota suka bar Billy da Abdallah a waje kallon juna sukayi cikeda shauƙi Abdallah yace”ammafa Queen zanyi missing ɗinki dan Allah kiyi ƙoƙari kisaka charge ga no ta da kuɗi a layin ki kirani “.
“toh sweetheart zan kiraka insha Allahu ,Allah ya tsare”.
“ameen “.
nan suka ɗan taɓa ƴar hirar soyayyarsu daga ƙarshe ta rakashi har gurin mota yashiga taima su Hafsat Allah ya tsare suka tafi.

3:20pm
sarkin ƙofa yashiga part ɗin Ammi samunsu yayi gabaki ɗayansu sunakan dining suna lunch ƙarasawa yayi gurin Ammi yace”ranki shidaɗe wai Aminu yazo gurin gimbiya Hafsat”.
Hafsat najin haka tayi murmushi murmushi Ammi tayi Hajjo tace”ya shigo”.
“toh ranki shidaɗe”.
nanya tafi bejimaba sega Aminu yashigo bakinsa ɗauke da sallama tashi Hafsat tayi tare da cewa”oyoyo Yayah sannu da zuwa”.
“yauwa”.
nan ya zauna tace”bara su Ammin su gama semuje ka gaidasu “.
“toh”.
nan cikin zumuɗi taita tambayarsa ƴan gidansu harsu Lantana segasu Hajjo sun fito ba tare da Hajjo ta kalleshiba sakamakon wayar da takeyi har suka ƙarasa falon da yake Ammi ce tace”sannu da zuwa Aminu”.
ƙasa ya sauka tare da cewa”yauwa Ammi ina yininku “.
“lafiya ƙlau yasu Ummitan”.
“lafiyarsu ƙlau”.
“masha Allah”.
“kishigar dashi ɗayan falon ku kuma ku haɗamishi abinci”.
“toh Ammi bara su gaisa da Hajjo”.
“toh”.

Hajjo na aje wayar taji ance”ina yini Hajiya”.
dammm ƙirjinta yabada ta ɗaga kanta da niyyar!!!!!

Cigiya dan Allah wanda yake da littafina me suna NABARWA ZUCIYATA bafa NABARMA ZUCIYA ba nawa doc ne ba txt ba ya temakamun dashi ta wannan number 08108362334.

Tallah! Tallah!! Tallah!!!
Ina kuke masoyana na haƙiƙa kufito ku nunamun ƙauna ta hanyar siyan book ɗina mesuna BAR RAINA ALLURA(Itama ƙarfe ce) ta wannan account number 2411022356 Aisha Ibrahim Zenith Bank aiko da shedar ki/ka ta wannan number 08108362334 ko kuma transfer katin Mtn /Airtel VTU ta wannan number 08108362334 masoyana na Niger zaku iya turo da katin Airtel ta wannan number 08108362334 sena jiku.

_*Daga Alƙalamin ƴar Mutane???? *HASKEN RAYUWATA*

MALLAKIN
REAL EESHOW

SUBSCRIBE
DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION

PAGE 2️⃣7️⃣➡️2️⃣8️⃣

     Ganin wacece sukayi ido huɗu da Yayah Aminu kallonsa Hajjo tashiga yi yayinda tashiga duniyar tinani taɓata Ammi tayi tare da cewa"ana gaisheki".

“sorry wlh ina can ina tinanin maganar dana gamayi lafiya ƙlau Amin ya gida”.
“lafiya ƙlau ranki shidaɗe”.
“masha Allah”.
kallon Hafsat Ammi tayi tace”ku wuce ciki ɗiyata”.
“toh Ammi “.
nan Hafsat tayi gaba yabita a baya suka nufi wani falo yayinda Hajjo ba abinda take se aikin binsu da ido kamar wata gunki har suka ɓace taɓata Ammi tayi tare da cewa”lafiya daiko aminiyata naga kinshiga wani hali zuwan yaronnan ko wani abunne yafaru”.
sauke numfashi Hajjo tayi tare da cewa”kinsan muryar yaronnan kamar ta ɗiyata”.
dariya abin yabawa Ammi tace”gaskiya ƙawata kinada wani tinani meze haɗa ɗiyarki da ruga wannanfa asalin fulanine a ƙauye kima dena wannan tinanin aminiyata mudai bazamu gushe da yimata Addu’ah ba intana raye Allah ya bayyanamana ita ƙawata yakamatafa yanzu ki dangana kibarwa Allah ikonsa”.
“gaskiya kumafa kika faɗa aminiyata Allah dai ya bayyanamana ita”.
“ameen”.
nan Ammi ta janyo wata hirar har suka manta da zuwan Yah Amin.

Sakawa tayi aka cikamasa gabansa da kayan motsa baki kallon Hafsat Amin yayi tare da cewa”gaskiya banda nayiwa ƙanwata farin sani da bazan ganekiba kingako yadda kika ƙara yin wani haske kamar balarabiya kuwa Hafsat”.
“kai Yayah harda tsokana toya mutanen gidan”.
“duk lafiyarsu ƙlau sis suna gaisheki”.
“masha Allah ammafa nayi kewarku wlh”.
“muma haka domin kullum semunyu hirarki da Ummita da Bappah muce kome kikeyi yanzu oho yanzunma Bappah ne ya dage senazo naga gidanki shinefa nazo”.
“wato da Bappah beceba bazakazoba kenan Yayah”.
“zanzo mana”.
“to kaci abubuwan mana”.
“toh”.
nan yafaraci se sukaji sallama Fatimah ce tashigo hannunta ɗauke da wani plate tace”sorry Aunty dama fruit ɗinda muke yankawa na ƙarasa”.
“toh ai shikenan taho muci”.
“toh Aunty Yayah Amin ina yini”.
Fatimah ta faɗa cikin girmamawa murmushi Amin yayi cikin jin daɗi yace”lafiya ƙlau Fatimah”.
wani daɗine ya ziyarci zuciyar Fatimah data kasa gane na menene taƙarasa ta aje plate ɗin gaban Hafsat suka zauna yanaci suna hira suma sunacin fruit ɗinsu duk ɗaga idon da Fatimah zatayi sesun haɗa ido da Amin se ya nuna kamar ba ita yake kalloba Hafsat dake kallonsu dasu haɗa ido tagansu sesu wayince a haka har suka gama cin abinci kuyangi suka kwashe kwanukan Fatimah tayimusu sallama ta haye sama.

Bayan tafiyarta Amin yace”toni sister bara nazo na tafi kar dare yayimun”.
“toh Yayah dama da maganar da nikeso muyi dakai dama inata tinanin wanda zansa ya faɗamuku”.
“toh inajinki sister”.
yafaɗi hakan tare da maida hankalinsa kanta numfasawa tayi tare da cewa”Yayah dama gobe zamuje taron karramar nan da za’ayi shine nakeson ku shirya kaida Bappah ku halarci taron saboda so nake kuɗinda akace nasamu asakasu a account ɗinka”.
“bangane a account ɗinaba”.
“eh Yayah so nake abawa makarantarmu 1million sannan ka ɗauki million ɗaya ka siyarwa su Ummita gida ɗan madaidaici a Gwarzo su dawo sannan million ɗayan kuma kaja jari saboda banason ciranin nan da Bappah yake tafiya kasamu gidan meɗan shago a ƙofar gida seka zuba kayan trader ka riƙa siyarwa kaga a ribar se a riƙa cefanen gida”.
“aiko dai wannan shawarar taki tayi sis to zanyi hakan insha Allahu domin nima kaina banason ciranin da Bappah yakeyi dandai bamu dashine”.
“yauwa Yayah amma ka faɗawa Ummita tinanin danayi kaji mezatace”.
“toh zan sanarmiki yadda mukayi amma da wanne kuɗi zamuzo mu to”.
“akwai kuɗinda Ammi tabani dazami shopping Abdallah yayimana na bata tace na kyalesu su zanbaka”.
“toh kace sunzo ai kinyi dacen ƙawaye sosai sister”.
“wlh kuwa ni ba abinda zance se Allah yaƙara haɗa kanmu bara na ɗakkomaka kar yamma tayi”.
“toh”.
nanta tashi ta haye sama bata jimaba ta fito harta fara sauka daga stairs taji wata kuyanga tace”Gimbiya Mai babban ɗaki na kiranki”.
tafaɗa cikin girmamawa ƙarasawa inda take a duƙe Hafsat tayi tare dasa hannu takamata ta miƙar da ita tace”kicemata ganinan zuwa”.
“toh nagode ya shugabata”.
nanta tafi ta sanar da Ammi sannan Hafsat ta juya ta nufi wani haɗaɗen bedroom tashiga bakinta ɗauke da sallama amsamata Ammi tayi nanta ƙarasa gaban Ammi da take zaune gefan gado ta duƙa kenan Ammi ta makamata harara da sauri ta tashi ta hau gefen gadon tace”gani Ammi”.
murmushi Ammi tayi ganin kallo yasa Hafsat kintsuwa tace”ga leda nan kibashi yakaiwa Ummita wannan kuma nashine da kuɗin mota”.
“toh Ammi angode Allah saka da Alkhairi”.
hararta Ammi tace”ɗazu daughter banacemiki karki ƙara yimun godiyaba”.
“ya haƙuri Ammina”.
“toh shikenan good girl”.
nanta ɗauki ledojin guda biyu da kuɗi ta tafi.

Ƙarasawa tayi har inda Amin yake kuyangi nabinta da kaya niƙi-niƙi Amin na ganinta ya miƙe nanta miƙamasa farar ledar tace”gashi wannan ka kaiwa Ummita inji Ammi wannan kuma na mutanen gida dakai sekuma wannan ka hau mota gakuma wannan kutafi Abujan da Bappahn”.
“toh angode Allah saka da Alkhairi muje nayimata godiya”.
“toh”.
nan sukaje yayimata sallama Fatimah ta tafi rakasu itama suna zuwa fita daga part ɗin Hajjo na shirin shigowa nan suka matsa ta wuce yayimata sallama tsayar dasu tayi tasaka aka ɗakkomata wata ƙanƙararriyar gizna fara da turare a ciki da dubu hamsin a emvelop godiya yayimata sosai sannan suka tafi har bakin get suka rakasa yayinda suketa satar kallon juna da Fatimah da Amin yi Hafsat tayi kamar batasanma sunayiba suna ƙarasawa get Fatimah takira driver yakaishi gida ba musu ya shiga aka zubamasa kayan a boot akaja sunawa juna bye-bye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button