HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Abdallah suna haɗa ido da Fatimah yace”gaskiya Fatimah Hammah yayi dacen mata wlh insha Allahu itace zata zama silar shiryuwarsa”.
“wlh kuwa Ya Abdallah ai sede fatan zaman lafiya”.
“hakane amma bakisan wani abuba wai haka yacewa Ammi baze dawoba meyasa ta auramasa baƙauya mara ilimi da wayewa “.
“haka nima Ammi take faɗamun dandai beganta bane”.
“hakane dole muma mu taya su Ammi kwatarwa Aunty ƴancinta a gurinsa ze gane kurensa”.
“hakane kam”.
nan ta ɗora hannunta suka haɗesu alamar alƙawari.

“Ummah dolenema na mallaki yarinyar nan kijifa irin karatun da take zubarwa agaban jama’ah kalli irin dirin da take dashi dan Allah ga kyau ba kalar wancan mara tarbiyyar miskinin bace kalar matar manyace irinmu”.
“ka kwanta da hankalinka indai wannan yarinyace kamar tazama taka domin yanzu Hassana ta tafi gurin boka Matsatsatsaku yau kome zezo ƙarshe”.
“yau Ummah na sannan kiyiwa Maryam magana ta dena son shiga gonar yarinyar nan domin tawace ni kaɗai”.
jisukayi Maryam tace”aiko baka isaba dan tun randa nafara ganinta naji inason in kasance da ita kabarni nayi sau ɗaya”.
“baki isaba wlh sakarai kawai”.
itako Ummah ba abinda take se dariya tace”kaɗan barta taɗan ɗana kaɗan”.
“haban Ummah wannan dai bazan barta ba ta tafi ga Cicilia can nabarmata”.
nan sukaita sakarcinsu harda faɗa kan Hafsat.

Bayan angama komai kowa yaci abinci Hafsat taje tagaida Malamansu can ta hangi M. Jalaludeen gefe suna soyewa da Habibah murmushi tayi tace”Fatimah muje ki rakani gurin M. nagaidashi semu wuce gurinsu Bappah”.
“toh”.
nan suka ƙarasa gurinsu M. Jalaludeen har ƙasa ta duƙa tagaidashi sannan ta kalli Habibah tace”sister anyini lafiya”.
cikin jin kunya Habibah tace”lafiya ƙlau Hafsat ya kwana biyu dan Allah kiyi haƙuri da abubuwan da suka faru nagode sosai”.
“bakomai sister dama ni bantaɓa riƙarkiba a zuciyataba ai ɗan adam ajizine bakomai kidena damun kanki”.
“nagode sosai”.
nansuka ɗan gaisa sannan suka nufi gurinsu Bappah taddasu Ammi sukayi agurinsu sunata hira gaidashi tayi sannan ta matsa kusa da Yayah Amin tace”ya kukayi da Ummitan”.
“ta yarda “.
“yauwa”.
nansuka shiga hira harda Fatimah .

Misalin takwas na dare a Airport da alama unguwa zasu Ammi tace”Hafsat ga wayarki nan nasakamiki ita a charge da layi inkunje ki kirani akwai numbers nasa Abdallah duk yasakamiki sannan idan result ɗinku yafito kamar yadda na sanarmuku zaku wuce U.k a gurin zuwa makarantarki inaso kituna ke matar aurece a cikin kayan danasaka aka shiryamiki akwai niƙab dasu zaki riƙa using gurin zuwa makaranta ko fitar gari ki kulada ƙanwarki Fatimah kinji “.
“toh Ammi insha Allahu zanyi abinda ya dace Ammi”.
“yauwa ɗiyar kirki sannan kema Fatimah kibi Yayarki kinji”.
“toh Ammi”.
“Allah yayimuku Albarka ku kula sosai “.
“Ameen”.
“ku kula sosai muma gobe zamu juya Adamawa kugaida su Firddausin “.
“insha Allahu Hajjo ki gaidasu Aunty Fauziyya”.
“zasuji Abdallah Allah ya tsare”.
“ameen”.
nan Hafsat ta anshi danƙareriyar wayarta aka kira jirginsu na AIR PEACE suka ɗaga Saudia!!!!!!!!

Qusition
wacce irin rayuwa Hafsat zatayi ?a Saudia kubiyoni danji yadda zata kaya

Yau inaso naga masoyana na haƙiƙa a duk inda kuke indai ke masoyiyata ce ki suburbuɗamun comments me zafi a duk inda kike

Tallah! Tallah!! Tallah!!!
Yadda zaki biya kuɗin BAR RAINA ALLURA
Ina kuke masoyana na haƙiƙa kufito ku nunamun ƙauna ta hanyar siyen littafina BAR RAINA ALLURA (Itama ƙarfe ce) ta wannan account number 2411022356 Aisha Ibrahim Zenith Bank aiko da shedarki ta wannan number 08108362334 ko kuma transfer VTU ta wannan number 08108362334 sena jiku.

Yanzu zamu shiga labarin

More Vote and Comments
More typing
Plz share

Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.✍️n Gwarzo.*_✍️???? *HASKEN RAYUWATA*

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION

PAGE 2️⃣9️⃣➡️3️⃣0️⃣

      Zaune suke a gaban boka Matsatstsaku sunata zayyanemasa komai abinda yake faruwa wata uwar dariya yaɓaɓɓake da ita lokaci ɗaya ya gintse tare da cewa"ai seda na faɗamuku dama kar a bari wani yagani to wani ne yaga lokacin da kika zuba ya hana yarinyar  ci amma yanzu zan baki wannan shine kat  maga me ƙara temakonta gashi".

boka yaƙarasa tare da ƙara sakin wannan dariya ɗaukar abinda ya ajiyemusu Fulani tayi tare da cewa”boka so nake ya kasance taji duk duniya ba wanda takeso se Marwan idan itace da bakinta tace batason wannan ɗan iskan yaron kaga dole wannan munafukar tsohuwar ta haƙura itama kuma zanzo na musamman ayimun aiki akanta a dubamun wa’incan a gani”.
“ki kwantar da hankalinki muddum kikabi yadda zan faɗamiki to dolenta dukda tanada addu’ah tasoshi sannan kuma kallarsu ai suna nan ai wannan farraƙun danayimusu bazasu taɓa dawowa su haɗeba toh sekinzo amma itama se anyi dagaske domin itama tanada Addu’ah sosai”.
yaƙarasa tare da ɗakko wata kwarya ya buɗe nan take mutane biyu ƴan mitsimitsi suka bayyana wato Maimartaba ya juyawa Farouk baya shima Farouk ya juyamasa baya dariya Fulani tayi tare da cewa”yauwa boka aikinka na kyau sosai tsinannu bazaku taɓa juyowaba a haka zaku dawwama harku mutu mu kwashi gado eh gaskiya semunyi da gaske domin wannan tsohuwar a tsaye take itama sannan kuma boka ka faɗi sharaɗi kona menene zanyishi indai yarinyar nan zata dawo taso ɗana”.
“hhhhh ki kwantar da hankalinki dolenta duk Addu’arta ta dawo ta biku sannan kuma kima dena tinanin ɗanki ze dena neman mata idanko ya dena sede ke ki mutu ko kinmanta abinda nacemikine seda mukayi dake cewar ki yanki jikinki bawa su ɗan tsitu jininki kuma kikayi dana baki maganin seda na gargaɗeki kan karki bari ki zuba wani ya tsallaka inba Farouk ba kika amince da kikaje se aka samu matsala Marwan ya tsallaka “.
“toh yanzu Boka Matsatstsaku ba yarda za’ayi a karya?”.
“hhhh da akwai amma sede ki mutu”.
kallon juna Fulani sukayi da ƙawarta Rukayya sannan Rukayya ta sauke numfashi tace”gaskiya ƙawata ki barshi kawai yayita neman matansa inba so kike ki wuceba bakiba cin gado sede ki kalla anayi”.
furzar da numfashi tayi tace”toh boka a kyaleshi yayitayi faɗamana yadda za’ayi da wannan maganin”.
“hhhh yadai fimiki wannan magani zakije ki haɗashi da jinin Al’adar yarinyar ki dafamata abinci taci dashi zakisha mamaki sosai sannan kuma karki bari ya kwana domin da matsala yanada hatsari sosai”.

Dafe ƙirji Fulani tayi tare da cewa”nashigesu Boka ina zansamu jinin Al’adarta ni kuwa”.
“ba kin iya makirciba kiji har ɗakin da yarinyar take kuɗanyi hira har kisamu domin yau ɗinnan ma zata gama Al’adar”.
“hmm to shikenan mushiga daga ciki dan a buƙace nake dakaiba saboda nayi kewarka sosai”.
“hhhh ai nasan za’ayi haka nima kuma haka mushiga “.
” Rukayya ki zauna anan banaso yarancan su fuskanci komai”.
“toh karku daɗe”.
nan suka shige cikin wani dannin kara .

Sun jima sannan suka fito lokacin gari yayi duhu sosai around takwas samun Rukayya sukayi inda suka barka gyara ɗaurin zane Fulani tayi tare da cewa”tashi muyi mu tafi banaso a fuskanci ban dawoba”.
“toh nima da kin bari naje naɗan ɗana domin nima yau ina network kinsan abunka da mara miji”.
“hakane kam to kuyi sauri 30mins”.
“yau godiya nake Uwar soron gobe”..
nan farinciki ya mamaye zuciyar Fulani tace “dole nayimiki kyauta me tsoka kuwa inkun fito”.
“godiya nake Fulanin sarki Muhammad yanzu kika fara juyashi”.
nansuka shige seda sukayi 1hrs sannan itama suka fito tana gyara zani nan Fulani ta ajewa boka kuɗaɗe masu yawa sukayimasa sallama kan zasu koma suka tafi.

9:00pm
Ammi da Hajjo suka koma gida nan Hajjo tace”Allah yakaisu lafiya”.
“Ameen ai gaskiya Magajin Malam yayi dacen mace tagari dubafa kigani dukda bamu wani jima da dawowaba nace su shirya bakiga yadda ta ƙal-ƙale bedroom ɗinsu da toilet ɗinsuba ko ina se ƙamshi yakeyi”.
“ai yarinyar natsatsace sosai wlh Allah yakaimu lokacin da Magajin Malam ze ganta ya ruɗe zesha mamaki dan sena kwatarmata ƴancinta”.
“wlh kuwa ai nima zan tayaki ze gane baida wayau ne”.
nan suka shigarsu ta aminai .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button