HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

9:30pm
Motarsu Fulani tayi parking a parking space ɗin ɓangarenta sauka sukayi cikin sauri suka shige part ɗin suna shiga sukayi kaciɓus da Jakadiya na shirin futowa daga falon tana ganinta ta zube tayi gaisuwa tare da cewa”ranki shidaɗe Maimartaba ne yasa na kiraki”.
“toh kicemasa gani nan zuwa yanzu na dawo na biya gaida Hajiya ne”.
“toh shikenan ranki shidaɗe”.
nan ta wuce Jakadiya ta fita shiga tayi bedroom ɗinta tayi wanka sannan tasaka wasu ƴan iskan sleeping dress ta ɗora Alkyabba shigowa Marwan yayi cikin yanayin damuwa ya zauna gefan gado kallonsa Fulani tayi da take fesa turare ta madubi tace”waya taɓamun sarkin gobena meyafaru”.
“Ummah gaskiya inajin tsoron abinda Cicilia take shirinyi”.
aje tureren Fulani tayi tare da ƙarasawa inda yake tace”me take shirinyi kenan?”.
“hakafa tace seta kashe Hafsat yanzuma text ɗinda ta turomun kenan a wayata dana kirata kuma naji wayar a kashe”.
“rabu da tambaɗaɗiya bata isaba wlh duk abinda take taƙama dashi nafita domin zansaka a kauda ita kadena wani jin tsoro tayi duk abinda zatayi gani gata sena koyamata hanakali wlh aikai kasan waceceni”.
“hakane Ummahna nagode yanzu ina zakije”.
“zanje part ɗin waccan tsohuwar najadun nafara gabatar da aikin boka sannan na wuce part ɗin Maimartaba”.
“wow my Ummahna sekin dawo”.
“toh seda safe”.
nan tafita ya kwanta yayi ɗaiɗai akan bed ɗin shikuma.
Tana fita ta haɗu da Maryam cikin wasu sexy sleeping dress red riga da wando dasu da babu duk ɗaya tana ganin Fulani tace”Ummah ina zaki”.
“zanje part ɗin Ammi ne zanfara gabatar da aikin boka”.
“wow Ummah bara nazo mutafi nima”.
“toh”.
nansuka tafi yayinda ta kori kuyangi masu yimata rakiya suka tafi daga ita se Maryam ba tare data damu da kayan dake jikin Maryam ɗinba.
Bakinsu ɗauke da sallama suka shiga samun Ammi sukayi kashingiɗe akan kilisarta tana lazumi murmushi jindaɗi Fulani tayi tare da ƙarasawa inda take tace”sannu da hutawa Ammi”.
“yauwa Zainaba ya gajiyar hanya”.
wani takaicine ya ƙume Fulani a zuciyarta tace”wato tsohuwar nan abun natama gaba yake ƙarayi yauko Fulaninma bazata ceba saboda tana baƙinciki da sannu zanyi maganinki”.
a filiko murmushi tayi tare da cewa”ai komai nayi ban faɗiba amaryar Son ɗina ce danafi so ya gajiyar taku”.
“lafiya ƙlau Zainaba bakiga kayan dake jikin Maryam bane kika barta ta fito a haka”.
“ban luraba Ammi ayi haƙuri ke Maryam bana hanaki yawo da irin wa’innan kayanba a gidannanba”.
Fulani suna haɗa ido da Maryam ta kashemata ido marairaicewa Maryam tayi tace”ya haƙuri Ummah zafine ya dameni mantawa nayi insha Allahu bazan sakeba ina zumuɗin ganin Aunty ne nayimata murna”.
murmushi Ammi tayi jin gurin ɗiyarta sukazo tace”to ƴar gidan Aunty a gyara”.
“insha Allahu Ammi bara naje gurinsu”.
ta miƙe da niyyar tafiya Fulani ta ɗagamata ido alamar good harta fara tafiya Ammi tace”au namanta basu daɗe da tafiyaba”.
waigawa tayi tace”Ammi ina suka tafi”.
“Saudia itada su Abdallah kafin ayimusu jarabawa su wuce U.K”.
damm gaban Fulani yabayar lokaci ɗaya duk sanyin a.c part ɗin ita gumi take dakyar ba annuri a fuskarta kamar an aikomata da mutuwa dakyar ta iya control ɗin kanta tace”amma Ammi meyasa ba’ah sanar daniba aida munyi sallama”.
“hakane na aika mutafi Airport akace bakyanan”.
“eh naje gaida Hajiya ne kwana biyu banjeba”.
“toh ai sekuyi waya”.
“hakane kam”.
fira kaɗan sukayi sukaimata sallama suka tafi.
Hankali tashe Fulani takira Ruƙayya tace”anyanka ta tashi munafukar tsohuwar nan ta tura yarinyar nan Saudia”.
“kai amma anyi ƴar iskar tsohuwa yanzu yaza’ayi kenan gaskiya kije da safe gurin boka ki sanarmasa dan kinji dai abinda yace banaso wani abun yafaru dani”.
“toh da sosamu nema yanzu yakamata aje saboda kinji dai abinda yace gashi shiba wayaba bare a sanar dashi yanzu sede mubar da safe naje”.
hankali tashe Fulani tace”to mezesa bazaki tafi yanzuba ko nawane zan inbiyaki”.
daga ɗaya ɓangaren Ruƙayya waro ido tayi waje tare da cewa”aini ko nawa zaki biyani bazaniba saboda kin rainamun hankali intafi wannan ƙasurgumin dajin yanzu da daddarennan ashema banson rayuwata kenan tabɗijam inzaki bari gobe da safe to inkuma bazaki bariba ki tafi da kanki”.
“haba Haj. Ruƙayya banason ne a samu matsala wlh ki temakeni”.
“wlh ba wani temako da zan iya yimiki inzakiyi haƙurin gobe da safe to dan bazan halakar da kainaba mitsss”.
ta kashe wayarta kuma kiranta Fulani tayi tare da cewa”kiyi haƙuri da safen sekije ɗin”.
“yanzu kikayi magana amma da banda kin rainamun hankali intafi wato ni wani abun yasameni ba damuwarki bane kenan bakida asara”.
“toh naji seda safe zan turamiki kuɗin zuwan yanzu”.
“toh”.
nan sukayi sallama ta kashe ta turamata sannan ta nufi part ɗin Takawa rai ɓace.
IYAS POV
Labari Bappah yaketa bawa Ummita na tarin jama’ar da suka halarci taron karramawa sega Yah Amin yashigo ɗakin zama yayi tare da cewa”sannunku da hutawa “.
“yauwa ya gajiyarku”.
“Alhamdulillah Ummita yanzu Hafsat ɗinki ana Saudia ƙila”.
“eyi Allah dai ya tsaremun ita a duk inda take yakaisu lafiya”.
“Ameen Ummita to yanzu Bappah gobe semuje Gwarzon a duba a ɗan sayi madaidaicin gidan me shagon”.
“Allah yakaimu semu shirya da wuri Allah dai yayiwa wannan yarinya Albarka daku baki ɗaya”.
“Ameen Allah yakaimu”.
“amma dai harda Iyah zamu komako bama barta ananba”.
“toh”.
“ni bara naje gurin ɗiyata “.
“toh sekin dawo Allah yasa dai ta faɗamiki domin taurin kan yarinyar nan ya isa”.
“insha Allahu zata faɗama”.
nan ta tafi tabarsu suna tsarin tafiyar da zasuyi.
Zaune tasamu Furera tana cin tuwo ƙarasawa inda take Ummita tayi cikin rarrashi tace”ɗiyata ki kwantar da hankalinki ki sanarmana da wanda yayimiki a bimiki haƙinki “.
wani ƙallon wuƙanci Furera ta watsawa Ummita tace”Allah ya kiyaye na faɗamiki ai ko zan faɗawa kowa bazan faɗamikiba har kinada baki faɗawa mutum yafaɗamiki abu zaki bimasa haƙƙinsa kifara biwa ƴarki magani tadena karuwanci sannan kibimun haƙƙin nawa inkura na maganin zawo tayiwa kanta mana”.
Ummita zatayi magana kenan taji an ɗauke Furera da wani gigitaccen mari zata fasa ihu Bappah yace”wlh tarinki naji a gurinnan senayimiki dukan kawo wuƙa baki isa kizo har gidana dukda abinda kika aikata kizo kiyiwa matata rashin kunyaba”.
yaƙara kai mata duka saurin taremata Ummita tayi tace”kayi haƙuri yarinya ce ai”.
“zata ci ubanta da yarintar wlh dama taci sa’ah nabarta ta zaunamun a gida yanzu tunda abunnan yafaru duk inda na gifta a Rugar nan ba abinda ake se aikin gulmata”.
“kayi haƙuri inka daka ta mutane ba abinda zakayi a duniya”.
nan dai Ummita ta lallaɓashi suka tafi yanata masifa.
Zaune Iyah take tana cin kwaɗon Zogala ita da Indo tana bata labarin da tace”aini nan da kike gani na da munyi rashin ji a Rugar nan danku bakuyi komaiba aradu “.
“tab kice mu yanzu bamuyi komaiba kenan”.
“eyi”.
suna cikin hirarsu yarinya ta shiga bakinta ɗauke da sallama tace”Adda Indo wai kije inji Rabi’u”.
“wa aiko be isaba yayi kaɗan rannan danaje gidan ba ɗebemun Albarka yagama yiba yayi kaɗan”.
“Iyah ki kwantar da hankalinki bara inje nima incimasa mutunci ze gane kurensa zesan ya taɓo jikar Iyah”.
washe baki Iyah tayi tace”yauwa Indo ki wankeshi tas da soso da sabulu dan ubanshi Jauro”.
“toh Iyah”.
“yauwa karki daɗe”.
nan ta tafi a zuciyarta tana kissima irin ruwan masifar da zatayimishi.