HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Zaune yake a dining tin fitowarsu ya kalleta ya saki wani shu’umin murmushi har suka zauna Fatimah ce tace”to Aunty ayi serving ɗinmu danni harna ƙagara naci wannan daɗaɗen abincin naki wlh”.
dariya Hafsat tayi tare da cewa”to sarkin kwaɗayi fara zuzuba”.
“naji indai akan wannan girkin me daɗine”.
zatayi magana sukaji wayar Salman dake zaune bako riga tana ringing yi sukayi kamar basujiba tace”Fatimah bara na zubana Rice and chicken pappe soup ko”.
“eh yayi”.
nanta zubamusu ɗaukar wayar Salman yayi tare da cewa”yah Ahmad kace yau kun tina dani kenan”.
daga ɗaya ɓangaren akace”eyi gobe mu haɗu a Al-hayat Mall zamuzo siyayyen perfumes”.
“wow Allah ya kawoku ku duka kenan”.
“eh mana F2 ne yasa na sanarmaka”.
“ok kace ina gaidasu semun haɗu”.
“toh zasuji”.
nan ya kashe tinda yafara waya gaban Hafsat ke faɗuwa jin an ambaci F2 shiko ba abinda yake se aikin binta da kallo dakewa tayi kamar ba abinda yake tsakaninsu tace”Yah Salman me za’ah zubamaka?”.
“Queen ki zubamun komai da zakuci”.
“toh “.
nanta zubamasa suka fara ci shigowa Abdallah yayi yana waya yaƙarasa kusa dasu tare da cewa”Sweetheart zan kiraki ina zuwa”.
nan ya kashe tare da cewa”wannan abincifa haka Aunty yanata zabga uban ƙanshi shine ko ku kirani wa yayi”.
“sorry Abdallah meza’ah zubamaka”.
“haɗamun shinkafa da miyar kifi da plantan”.
“toh”.
nanta zubamasa shima Abdallah ne ya kai lomar farko yace”wayyo daɗi dan Allah wa yayi girkin nan nasan dai ba waccan uwar son jikin bace”.
yafaɗa yana kallon Fatimah .
“Aiko dai nice kaidai kaci a hankali karka shaƙe garin santi bara na sakamaka waigi a bayanka”.
“hhh kedai kici a hankali domin tunkan na ƙaraso dining ɗinnan na hangeki kinata zuba loma”.
dariya kowa na gurin ya kwashe da ita Fatimah tace”girkin Aunty nefa Yah Abdallah”.
“haba koda naji ashe na Yayas ne shiyasa naji yafita daban da jagwal-gwalonki”.
“hhh aidai gobe ranata ce nima Aunty zakiji irin santin da zeyi”.
“Allah ya kiyaye na yima jagwal-gwalonki santi kamar a films”.
“Allah dai yakaimu Abdallah magani tsakanin kaida ita”.
“Ameen”.
nan Hafsat ta tsiyayi jus a glass cup tasha tare da cewa”Fatimah ni bara na koma main falo sekin tawo”.
“toh sena tawo dan ni sena ƙara”.
“toh”.
nan Hafsat ta tafi yayinda Salman ma ya miƙe ya tsiyayi jus a glass cup ya nufi falo yana bin Hafsat da kallo kamar wani ƙasurgumin maye ganinsa yasa Hafsat ɗaukar wayarta tashiga chart dasu Billy tana cikin chart Fatimah taƙarasa tare da cewa”Aunty to mutafi falon Aunty tana can tana jiranmu mufara”.
“toh”.
“mumafa Salman yakamata muzo mu fara shirin Birthday ɗin twins ɗin Aunty fa”.
“hakane kam tozo muyi budget”.
nan suka shiga budget sukuma suka tafi falon Aunty Fido.
Samunta sukayi zaune da glass tanata rubuce-rubuce zama suma sukayi Aunty Fido tace”sannunku se yanzu anacan ana surutu daughter aini harna kusan gamawama kayan kawai da zakusaka zaku faɗi kalarsu ammani harnasu Afnun da Anun nasa wacce kalar kukeso”.
“ya haƙuri Aunty yanzu muka gama cin abinci”.
“to aibakomai nidai ku faɗi kalar so nake daga gobe idan sun dawo da Dadynsu mu fara shiga kitchen tare daku mufara abinda aka kawoku Fatimah gobe sekiyi na safe kawai”.
“toh Aunty Allah yakaimu lfy”.
“Ameen”.
“nidai nafison white and red ɗin English wears sannan da sari shikuma red and golden”.
“toh yayi Hafsat fa”.
murmushi Hafsat tayi tace”ki zaɓarmun Aunty duk kalar da kikeso”.
“toh shikenan daughter bara a sakamiki English wears white and pink se sari ɗin ya kasance iri ɗaya sekuma abayoyi suma kuyi iri ɗaya”.
“toh mungode Allah yaƙara arziƙi”.
“Ameen daughterna nidai abinda nakeso dake ki saki jikinki kamar yadda Fatimah takeyi”.
“toh Aunty insha Allahu”.
nan suka cigaba da hirarsu cikin jin daɗi basu suka yimata sallamaba sha ɗaya suka tafi suka kwanta.
Tin shida suka tashi saboda cikin Fatimah daya ɓaci kwana tayi tana gudawa seda Hafsat taje ta amsar mata magani tasha sannan taɗan samu bacci sosai tashi Hafsat tayi ta gyaramata kwanciya ta luluɓamata blanket kallon ɗakin tayi taga duk angyara se ƙamshi ketashi ta ko ina murmushi Hafsat tayi tare da sauka a zuciyarta tace”gaskiya gidan sarauta yayi a rayuwa”.
nanta tuɓe sleeping dress ɗinta ta ɗaura towel ta shige wanka bata jimaba ta fito ɗaure da towel ƙarami kuma tana goge kanta daya ɗan jiƙe sannan ta wuce ta zauna kan kujerar dressing mirrior tashiga shafa tana gamawa ta nufi drowers ɗinsu ta ɗauki wasu riga da skirt na atamfa a cikin kayanta na gidan Ammi ta saka ta ɗaura ɗankwali simple ta kalli madubi taga lokaci ɗaya yadda ta canza murmushi tayi ta ɗauki wayarta taɗanyi selfie ta fice cikin sauri ta nufi kitchen samun Ashwariy tayi me aiki tana kici-kicin fere doya gaida ita Hafsat tayi tare da cewa”kawo Momy ki huta yanzu zan gama insha Allahu”.
“a’ah ƴata kibarshi saura soya doya kawai ya ragemun nagama komai”.
“a’ah dan Allah Momy kibarshi nima so nake na kware sosai”.
“toh ai shikenan yame jikin ta kwana”.
“da sauƙi Momy kide ki tafi idan na kammala sena kiraki mu shirya dining ɗin”.
“toh Allah yayimiki albarka ƴata”.
“Ameen”.
nanta tafi Hafsat ta fere doya ta wanketa ta zuba a tukunya ta ɗora akan gas bata jimaba ta kwasheta a kwalanda sannan ta fasa kwai ta yanka albasa ta zuba spices ɗinta ta ɗora kasko ta zuba mai tashiga soyawa lokaci ɗaya ƙanshi ya cika gidan dan-danan ta kammala ta ɗakko wasu haɗaɗun warmers wanda tagani akan table Ashwariyy ta aje ɗauka tayi ta zuba ta mayar ta rife sannan ta fita ta sanar da ita tare suka dawo nan suka ɗauka suka kakkai dining suna ajewa Hafsat tace”Momy bara na gyara kitchen ɗin kekuma ki shirya nan”.
“ƴata bakya gajiya da kin barshi nayi ki huta”.
“a’ah Momy ai ba wani aiki nayiba kedai kiyi wannan bara naje”.
Hafsat tafaɗa tare da tafiya murmushi Ashwariyy tayi tare da cewa”toh Allah dai yayi Albarka”.
“ameen”.
nanta wuce kitchen tashiga goge gas tana karatu batayi auneba taji an rugumeta ta baya jikinta ne yashiga rawa hankalinta yayi mugun tashi jin ƙanshin turaren datayi ne yasakata gane Salman ne kalle-kallen inda zataga wani abun tashiga yi yayinda shikuma Salman yace”to yau gaki a hannuna Baby maga me zaki iyayi bake wai me ƙarfin halin iya marina ba yanzu maga yadda zaki kwaci kanki domin bantaɓa sha’awar wata mace a duniya tayimun wulaƙanciba se a kanki”.
mutsu-mutsun kwacewa tashigayi yaƙara wani riƙeta yana shashshafata karaf idonta ya sauka akan kwalbar curry dake kan gas saurin fisge hannunta tayi shiko sakaran yanacan yana shafe-shafe idonsa a lumshe tana kuka ta ɗauki kwalbar ta makamasa a goshi ta kwasa a guje ta haye sama tana kuka lokaci ɗaya ya tafi taga-taga ze faɗi dakyar ya kama ƙofa yayinda lokaci ɗaya ɗaya jini ya wankemasa fuska ƙarasawa yayi jikin sink ɗin kitchen ɗin ya wanke ya ciccire kwalbar data maƙalemasa ya wanke ya goge gurin da jinin ya ɓata ya fita dafe da kansa hankali tashe ya nufi bedroom ɗinsa.
Hafsat na shiga ta wuce gurin wardrobe ɗinsu ta buɗe tashiga kwasar kayanta tana kuka Fatimah ce tafito daga toilet da alama ta daɗema ta shiryawa domin cikin kwalliya take itama ganin Hafsat tayi tana kuka tana shirya kayanta a box cikjn ruɗewa ta ƙarasa gurinta tace”meyake faruwa Aunty naga kina kuka kina haɗa kaya ina zaki ko wanine yayimiki wani abun “.
cikin kuka tace”Fatimah ba wanda yayimun wani abun nidai kawai nafison gurin Ammi banason zama a garinnan nafison gurin Ammi”.
“haba Aunty gaskiya ban yaddaba sede in wani abun aka yimiki gaskiya bara na faɗawa Aunty Fido ko Yayah Abdallah ne yayimiki wani abun”.
“a’ah nidai kawai gida zan tafi nafison gidan Ammi”.
“toh bara insanarwa da Aunty”.
nan tafi cikin sauri tabarta tanata kuka.