HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Warning
Rashin comments and votes ka iyasa namaida book ɗinnan na kuɗi .

More votes and comments
More typing
plz share

Yanzu zamu fara shimfiɗa

_*Daga Alƙalamin ƴa???? *HASKEN RAYUWATA*

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME OF QUALITIE’S WRITER’S ASSOCIATED

PAGE 0️⃣3️⃣➡️0️⃣4️⃣

_ Fuskar wani haɗaɗen gient guy wanda ya gaji da haɗuwa cikin riga armless da wandon jeans three quarter hannuwansa yasha zanen tatu raɗa-raɗa sumar kansa tasha askin nan na ƴan iska wato batalatoni an aske gefe da gefe tsakiya kuma anbarshi da suma me tsayi tasha gyara baƙa wuluk da ita se sheƙi take gefen kuncinsa wani kwantaccen sajene yasha gyara yayi luf dashi farine tas me fararen ido manya yanada dogon hanci da ɗan ƙaramin bakinsa pink ya haɗu sosai kallon ƙirjinsa tayi taga yasha sarƙoƙi saurin kallon kunnensa tayi taga yasha barima jitayi gabanta yayi mumunan faɗuwa a zuciyarta tace”anya wannanko ba mace bace ba kuwa to inkuma macece da banganta da ƙirjiba”.
jitayi an sheƙe da dariya hakan yasata kallon su Billy dafata Zully tayi tare da cewa”amma keko anyi ƴar ƙauye namijinefa bakiga sunansa bane da harkike maganar ƙirji”.
waromusu fararen idanunta tayi alamar sunji dariya suka ƙarayi tare da cewa”munkoji aiba a zuciya kika faɗaba “.
“ammako baida tarbiyya gaskiya wannan ba wanda zece ba mace bace wlh”.
“hmm wankan kenan be wise mana baby”.
“indai wannan wayewarce bana fatan nayita yanzu wannan wazecema ɗan musulmine dan Allah”.
“hmm ke yanzu nan bakisan 5DBCP na Nigeria ba kenan”.
“eh”.
“nimafa Billy bansansuba ki haɗa dani nima me ake nufi da 5DBCP da hakan”. ( 5DBCP, 5 Dangerous Beauties Crown Prince).
murmushi Billy tayi tare da cewa “nasan bazaku ganeba kubari mugama kallon sauran hotunan”.
taƙarasa tare da nuno musu sauran hotunan sauran guda huɗun suma kowannensu cikin irin shigar riƙaƙun ƴan iska nance jikinsu kuma kowannensu najida kyau amma basu kai na farkonba dukkaninsu zasu iya kai shekaru 33-32 amma kowannensu inka ganshi zaka ɗauka ƙasurgumin arne ne tabakin Hafsat ɗin seda suka gama kallonsu tsaf sannan Billy tace”wannan sunansa F2 wato crown prince Faruk Mahmud Faruk babban ɗan sarkin kano ne wannan kuma Abdul’Jalal muhammad Abdullah ɗan sarkin Jigawa ne wannan kuma sunansa Ahmad Sa’eed Abbakar ɗan sarkin Bauchi wannan kuma sunansa Adam Musa Ibrahim ɗansarkin ƙatsina se wannan autan nasu wanda ya kasance ɗan sarkin Zamfara wato Habib Aminu Mahmud dukkansu ƴaƴan sarakunane kuma jikikon sarakuna wa’innan da kuke gani bama Nigeriah kaɗaiba hattana ƴan abroad sunsan da zamansu domin sun gagari kowa a ƙasa kowanne daga cikinsu consultant doctors ne sannan kuma wannan shigar da kuka ganinsu da ita irinsu sune shigarsu sunada mugun haɗari sosai sannan kuma suna shaye-shaye suna neman mata yanzuma mutane cewa suke ba lallaine suna sallah bama ammafa sunada muhaukatan kuɗaɗe sosai domin dana tambayi Yah Munir haka yacemun a UK suke zaune wannan duk kuma club namasu dashi to zaki samesu 5 Dangerous Beauties Crown prince shine laƙabinsu inkika gansu musamman F2 zaki ɗauka macene saboda kyau gashi bashida hayaniya a cikinsu shine ogansu”.

Sauke numfashi Hafsat tayi tare da cewa”ni banga amfanin nunamana wa’innan mara tarbiyyar ba wlh natsanesu inmasu shiryuwawane Allah ya shiryasu inbamasu shiryuwa bane Allah kaikasan yadda zakai dasu”.
“ameen wai intambayeki Billy duka sunada aure kuma”.
Billy dama tasan halin ƙawayen nata shiyasa batayi mamakin tambayar da Zully tayimataba dantasan Zully dasan namiji mekyau murmushi tayi tare da cewa”ba wanda yake da aure a cikinsu Zully wanine yayimiki a cikinsu”.
washe baki Zully tayi cikin jindaɗi tace”aini duka summun amma nafison F2 ya haɗu gayen over wlh dama ze aureni aida naji daɗi”.
“keeh aini nakesonshi sede kizaɓi wani cikinsu narigaki”.
“haba Billy dan Allah kibarmunshi”.
“kefa Zully haka kike idan kikaga mekyau daban nunamikiba a ina zaki gansu bare kisosu Allah bazan barmiki shiba”.
nanfa gardama ta kaure tsakaninsu kowa yana kowa yabarmishi jisukayi Hafsat ta tintsire da dariya tsayawa sukai da gaddamar da suna kallonta seda tayi dariya me isarta tana kallonsu tana dariya har seda kowacce cikinsu ta fara jin haushinta sannan ta daure dakyar ta tsayar da dariyarta tace”amma kuko anyi shashashu lamba ɗaya yanzu ku da kuketa gaddamar nan kuɗi za’ah baku kome naga su wa’inda kukeyi dominsu ina tinanin bama susan da wasu halittunsu Zully da Billy ba a doron ƙasa amma kun haƙiƙance kansu dama wasu mutanen arziƙine da se intayaku da addu’ah Allah ya haɗaku dasu amma kuzauna kan wa’innan sheɗanun kuyita ɓata lokacinku a banza a wofi nifa wlh inkuna wani abun har mamaki kuke bani sede nace Allah ya shiryamunku”.
“ke aidama kullum cikin wa’azi kike idan mun haɗu dasu abin farko da zamu farayimiki hajji zamu kaiki”.
“wlh kuwa tona haƙura na ɗauki Habib auta kika sani komu zama silar shiryuwarsu ma”.
dariya Hafsat taƙarayi tare da cewa”ai ina fatan haka nima manyan aminaina suyi silar shiryuwarsu nagode da hajjin da zaku kaini”.
“waike mekike nufi bazaki zaɓaba kene”.
ƙara kwashewa da dariya Hafsat tayi ganin su bilhaƙƙi suke abun nasu tace”a’ah waneni da irin wa’innan manyan gayun sedeku manyanmu”.
a yanayin data ƙarasa maganar sukasan shaƙiyanci take musu hakan yasa Zully cewa”kefa ai babbar ƴar iskace mara m. kawai karki ɗauka ɗin Billy ƙara nunomin hotunansu musha kallo”.
“toh gwarama mucire wannan mara m. ɗin a lissafinmu tunkan ta kashemana zuciya muma mu zama irintata”.
“ai gwara da kuka cireni namaji daɗi nidai inkun haɗu dasu anyi auren nazo naci taliya da manja da yaji”.
taƙarasa maganarta tana dariya,dariyar suma sukayi Billy tace”aiba taliya kaɗai zakijiba har dajajatun sekinci da abinda take sakawa yarinya ko Zully”.
“sosai daka nan ma haɗata da ɗaya daga cikinsu itama”.
“ai yanzumma ba kyaleta zamuyiba semun zaɓarmata ina ganin mu ɗaukarmata Ahmad”.
“aiko hakan yayi wlh”.
dariya sukaita bata amma suko a jikinsu wunin ranar zancensu sukayita yi da an nuno Ahmad sesuce ga saurayin Hafsat da an nuno Habib sesuce ga saurayin Zully da sunga F2 sesu ruɗe da shewa har aka tashesu.

4:45pm
M. Jalaludeen yagama karin siratun nabiyyi yana rife littafin yace”kufita yau da akwai Assembly naga ƴan sauran classes sunfito Hafsat kizo office kisameni zaki amshi saƙo”.
“toh Malam”.
“yanzufa zaki tawo saboda Assembly”.
“toh”.
nanya fice tashi Hafsat tayi tare da miƙama Zully jakarta tace”ku tafimun da ita kafin nazo”.
“toh Mrs 5DBCP sekin tawo”
cewar Billy dariya Hafsat ta kwashe da ita tare da cewa”wlh mutanen nan kuna shagalinku wato har an raɗamun suna bansaniba”.
“sosai kuwa ke kike ganin abin namu wasane in Allah ya haɗamufa aimu inmuka gansu kobasu ce suna sanmuba tomu semun faɗamusu wlh”.
“ina fatan Allah ya haɗaku kodan nima inyagi arziƙi natafi karkuja M. Jalaludeen ya dakeni”.
nanta tafi cikin sauri tazo zata wuce kenan a ƙofa taji an bangajeta waigawa tayi taga Habibah hakan yasa ta wuce abinta ita kuma Habiba ganin ta nufi office ɗin M. Jalaludeen ne yasa ta bi bayanta ta raɓe ta bayan window cikin nutsuwa take tafiya harta isa ƙofar cikin zazzaƙar muryarta me sace zuciyar samari tace”salamu Alaikum”.
M.Jalaludeen dake duba littafi zadul-zaujain ne yaji muryarta ta daki dodon kunnensa wanda hakan yasa shi lumshe ido ya buɗesu ya kalli ƙofar shigowa dakyar network ɗinsa yadawo yasamu yace”wa’alaiki salam shigo”.
cikeda nutsuwa ta ƙarasa gaban table ɗin da yake ta duƙa tace”gani M.”.
jiyayi duk maganganun bakinsa sun ɓacemasa yashiga tinani dakyar ya aro jarumta ya yafawa kansa gyaran murya yayi tare da cewa”Hafsat”.
ɗago ido tayi ta kalleshi tare da cewa”na’am Malam”.
“a gidanku anmiki miji?”.
damm taji zuciyarta ta amsa jitayi yawun bakinta ya kafe-kaf tashi ga duniyar tinani Habibah dake raɓe jitayi gabanta yayi wata mumunan faɗuwa har jiri na ibarta ga wata irin tsanar Hafsat data ƙara ruruwa a zuciyarta dakyar ta nutsu danjin mezecemata Hafsat data tafi duniyar tinani ko jitayi M. Jalaludeen yace”kinyi shiru Hafsat”.
dakyar ta tattaro nutsuwarta tayi ƙasa da kanta tace”a’ah Malam”.
jitayi yakuma jehomata wata tambayar yace”kinada saurayi?”.
wata kunya taji ta yayyaɓeta tayi ƙasa da kanta tashiga tinanin itada a ƙauyensu bame sonta mezata cema M. wata dabara ce ta faɗomata hakan yasata sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya tace”a’ah ba yanzuba inji Ummita da Bappi”.
murmushi yasaki tare da cewa”Hafsat ina sanki ina fatan kizama abokiyar rayuwata ina barar soyayyarki gareni”.
zuciyarta taji ta ƙara bugawa mamaki takeyi anyako M. Jalaludeen ne wannan wanda kowa yake tsoronsa shine yake faɗamata wannan kalmar tana cikin wannan zancen taji yace”ko bammiki bane Hafsat”.
saurin rife fuskarta tayi alamar kunya tace”waye ze ganka yace bakaimasa ba Malam nidai tinanin zancensu Bappana nakeyi”.
murmushi yayi tare da cewa”ai nima banason kowa yasan inasonki har se kinkai s.s.2 sannan a faɗawa su Bappa inaso yazama sirri tsakanina dake nima nasan zuwa lokacin nagama n.y.s.c ɗina banason hakan yazama silar karatun danake biyamiki kidena kinji “.
kai kawai ta iya gyaɗamasa saboda kunya ganin yadda dukta takurane yasashi murmushi yace”kitafi Assembly sarkin kunya”.
sumi-sumi ta miƙe ta fice itako Habibah jitayi kamar taje ta kashe Hafsat a haka rai ɓace ta ƙarasa gurin assemblyn itama shima fitowa yayi yatafi yanata zabga murmushi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button