HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Washe gari su Hafsat suna idar da sallar asuba suka wuce kitchen suka shiga haɗa break fast suna gamawa suka haye sama sukayi wanka ƙarfe goma daidai kowa ya hallara dining akashiga cin abinci bayan sun gama Hafsat tace”kuzo muje nayimiku wanka Afnun “.
“toh Aunty”.
nanta kamasu suka shige bedroom ɗinsu sosai Aunty take jin daɗin yadda take kulamata da babies ɗinta bayan sun tafi akayi sallama Fatimah ce ta tafi bakin ƙofa dan ganin waye tana zuwa tagaida mutumin nan yace mata”me decoration ne”.
“toh ka shigo ka fara”.
nan tayi gaba yabi bayanta ta wuce sama ita tararwa tayi Hafsat tagama tsarawa su Afnan kwalliya sunyi kyau sosai murmushi tayi tare da cewa”amma my babies ɗina kunyi kyau sosai kuje ku anso kayanku na shiryaku”.
cikin murna sukace”toh”.
nan suka ruga suka tafi anso kayan da zasu saka Hafsat ce ta kalli Fatimah tace”ki shirya kema idan me make-up ɗin tazo a fara yimiki ni bara naje na amso cake ɗinda kika bayar da order a mall ɗinnan”.
tinowa da abinda yafaru Fatimah tayi murmushi tayi haɗe da cewa”toh Aunty sekin dawo bara nashiga nayi wankan nima dan yanzu zaki iya ganin me make-up ɗin kuwa”.
“toh”.
nan Hafsat ta tafi ta buɗe drower su ta ɗauki pink ɗin mayafi da ze shiga da super holland ɗin jikinta ta yafa ta ɗauki wayarta da niƙab ta fita tana sauka ƙasa taji muryar Aunty Fido suna tahowa daga part ɗinta dasu Afnun suna tayimita surutu zama tayi akan kujera tana jiran su ƙaraso fitowa sukayi Aunty Fido na ganinta tayi murmushi tace”daughter tafiyar zakiyi?”.
“eh Aunty”.
“toh Abdallah na waje kije ku tafi tare”.
“toh”.
nan tayimata sallama ta tafi samun Abdallah tayi a mota yana jiranta ya buɗe ƙofa da niyyar ya zaga ya buɗemata ta nunamishi ta buɗe ta buɗe suka tafi.
Suna shiga Mall ɗin ta kalli gurin turaruka nan take abubuwan da suka faru tsakaninta da F2 suka shiga dawomata tsaki tayi Abdallah dake gefanta ne ya kalleta seyaga gurin turarennan ne murmushi yayi tare da cewa”babbar Auntyn lafiya naji kina tsaki”.
murmushi tayi tace”lafiya ƙlau Abdallah mu fara zuwa can akwai wani turare dana ɗauka rannan yayi kyau sosai na mantashi a gurin”.
“toh”.
nan suka nufi gurin Abdallah nata danne dariyarsa suna isa gurin sukaga fayau babu sema wani turaren da sukaga an jera a gurin mamakine yakama Hafsat ta kalli Abdallah tace”kaga gurin ba turaren ba alamarshi sema wani da aka jera kuma wlh inasonshi”.
Abdallah daya gane turaren da take nufi ne yace”anyako Aunty kinga turarennan kuwa ai beci ace jiya kunzo kun ganshi yau kuma ace harya ƙare ko muje office ɗin manager mu tambayeshi”.
“wlh dagaske nake Abdallah har ɗaukarshi nayi muje ka tambayeshi muji danni ba ƙaramin son turarennan nakeba”.
Hafsat bata kawo komaiba tabi bayan Abdallah suka hau sama office ɗin manager knocking sukayi ya buɗemusu suka shiga yabashi hannu suka zauna a kujerun dake gabansa Abdallah ne yace”jiya sisterna tazo gurinnan zata siyi turare harta ɗauka seta manta kuma yanzu munje gurin da niyyar ɗaukarshi mu siya mukaga anjera wani ko har an siyar”.
“eh an siyar dashi”.
Abdallah a zuciyarsa yace”gaskiya da zancen ji bara nasaka Aunty ta tafi ta duba cake ɗinda suka bayar ayimusu nikuma na tambayeshi sosai Allah yasa Hamma ne ya ɗauka ma daɗa shan dariya”.
a fili kuma kallon Hafsat yayi tare da cewa”Aunty kinji an siyar dasu seki duba wani daganan seki duba cake ɗin kafin nazo zanyi magana da manager”.
sosai mamaki yakama Hafsat tace “toh seka taho bara naje”.
“toh”.
nan ta tafi tana tinanin wayeko wannan ya siye wannan turare bayan ta fita Abdallah gyara zama yayi ya kalli manager yace”waye ya siyi turaren ne wai”.
murmushi manager yayi yace”F2 ne ya siya yace kada a ƙara kawoshi nan mall ɗin saboda turaren yana lalata tarbiyyar yara…..”…..
be ƙarasa faɗan maganar ba dariya ta kuɓucewa Abdallah yace”toh mun gode”.
yafaɗa tare da miƙewa yana kallon agogon hannunsa ya fita a zuciyarsa yana cewa”wato shi sarkin kishi shine yasaka gabaki ɗaya a kwashe turaren saboda kishi”.
yana tafiya yana dariya samu yayi har angama cake ɗin ana shirin ɗaukar mata ƙarasawa yayi kusa da ita yana murmushi yace”kice har angama ban ƙarasoba”.
hararsa tayi tare da cewa”eyi tunda kasamu hira ina zaka tuna da watani”.
“wlh a’ah Aunty”.
nan suka tafi yanata dariya ƙasa-ƙasa.
Misalin biyar su Hafsat ne zazzaune cikin kwalliyarsu me ɗaukar hankali suna tafa hannu ana yiwa su Afnun waƙar birthday seda suka gama sannan aka hure wutar jikin candle ɗin dake jikin cake ɗin nan yaran suka yanka ɗaya taba Abbanta ɗaya kuma tabawa Aunty Fido tafi akayi sannan Afnun ta yanka tabama Hafsat Anun kuma tabama Fatimah Abdallah yakama baki yace”wato lallaima yarannan saboda ni kunmaidani ɗan kishiya ba wadda tabani cake ɗin ko”.
dariya Aunty Fido tayi tare da cewa”baka siyomusu choculate shiyasa suka manta dakai “.
nan Afnun ta yanka da niyyar kauda kai yayi waishi ala dole fishi yakeyi dariya Afnun tayi tabashi amsa yayi tare da cewa”nadai temakeki badan halinkiba”.
dariya duk akai tayi Abbansu Afnun yace”kaidai baka raboda sakarci da ƴaƴan cikinka kake wannan abun salon su rainaka”.
“kaima dai ka faɗa Abban Afnun”.
cewar Aunty Fido Abdallah ne yace”ƙanwata sarkin kwaɗayi zokiji wata magana”.
“toh muje ina jinka”.
nansuka tafi gefe guda dariya Abdallah yayi yace”mutuminfa saboda tsabar kishi ya hana ƙara kawo turarennan “.
“dan Allah fa kace mukamashi kenan aiko ze gane kurensa”.
“wlh kuwa”.
nansuka koma aka shiga hotuna kala-kala da kayayyaki da suka siyo.
AFTER ONE WEEK
Zaune Abbah yake a ɗakinsa yana karanta daily thrust ƙarasawa yayi bakinsa ɗauke da sallama ɗago kai Abbah yayi cike da mamaki dan yasan Salman ba abinda yasani se kiɗe-kiɗe murmushi yayi ya ansamasa ƙarasawa yayi cikin ladabi ya zauna aka ƙasa kusa da ƙafar Abbah yace”Abbah ina yini”.
“lafiya ƙlau Salman”.
shiru ne ya biyo baya tsakaninsu Abbah ne yayi murmushi yace”Salman meya faruwa ne”.
inda-inda yashigayi murmushi Abbah yaƙarayi ya aje jaridar da yake karantawa akan stool yace”Son yi maganarka straight forward”.
ƙasa yayi dakansa yace”Abbah dama nasamu matar aure”.
murmushi Abbah ya faɗaɗa yace”masha Allah a ina take Son kuma ya sunanta”.
“Hafsat fa Abbah ƴar uwar Aunty “.
haɗe rai Abbah yayi yace”kai wanne irin sakaraine kai matar aure cefa to karna ƙaraji banason shashanci”.
wata irin bug
a wagaban Salman yayi cikin murya kamar tame shirin yin kuka yace”Abbah kayi haƙuri bansan matar aure bace wlh”.
“bakomai ka kula sosai idan kaga wata yarinya data kwantamaka ka faɗamun insha Allahu”.
“toh Abbah nagode”.
nanya tafi jiki a sanyaye yana haɗa hanya ya isa part ɗinsa ya zube kan three seater ya fashe da wani matsanancin kuka.
Fitowa tayi daga kitchen tana yarfe hannunta taƙarasa falo tace”Aunty an kammala fa”.
“toh daughter sannu da ƙoƙari “.
“yauwa Aunty”.
tana duba wayarta taga baƙuwar number dialing ɗin number tayi bugu ɗaya aka ɗauka jin muryar M. Jalaludeen tayi yace”salamu Alaikum”.
murmushi tayi me sauti tace”Wa’alaika salam Malam anyini lafiya”.
“lafiya ƙlau Alhamdulillah”.
“masha Allah ya Aunty Habibah”.
“lafiyarta ƙlau dama zancen musabaƙane anata kiran wayarki ba’ah samu gobe za’ah gudanar anan ƙasar Saudia shine shugaban makaranta yace nasanar dake misalin 11:00 za’ah fara”.
“toh Malam bara na faɗawa Aunty”.
“toh shekaran jiya duk aka yimana passport dasu Ummita”.
murmushi jin daɗi tayi tace”kuma wlh basu faɗamunba a ranar kuma munyi waya harda Ummita kuma”.
“ƙila ta manta shiyasa to se anjuma”.
“toh se anjuma agaidamun da Auntyna”.
“toh zataji”.
nanya kashe Aunty cetace”daughter meyake faruwa”.
“dama yanzu aka kirani wai gobe za’ayi musabaƙa misalin 11”.
“Allah yakaimu yakuma baki nasara seki kirasu Ammin taki da Ummita ki sanar dasu”.
“toh bara nakira”.
nanta kirasu ta sanar dasu sukayita yimata Addu’ah.