HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

IYAS POV
Zaune Furera take gaban Iyah tagama zayyanemata ƙarya da gaskiya akan zamansu da Ummita numfasawa Iyah tayi irin abun ya tumbatsa tace”aiko ko tana tsafi da bahaguwar jaɓa ƙarewar bokan da take taƙama dashi bata isa ta hanaki zamaba ai gidan ubankine kinjini”.
“nifa Iyah tsoro nakeji kartasa Bappah ya tsinemun domin rannan bakiga faɗan daya yimunba kamar ze dokeni”.
“tayi kaɗan shikuma zezo ya sameni ina zaune a shararren guri dako tasashi ya tsinemiki ba makawa nima sena tsinemishi seya tafi ta zama uwarsa tazama ubansa kajini da sakaran yaro kawai tunda ya haɗu da yarinyar nan nashiga wani hali aradu sannan abinda zancemiki karki kuskura ki ragamata daidai da kwayar zarr kinji dai na faɗamiki”.
“toh Iyah aidama ni bana ragamata aradu rashin mutunci nakemata”.
“yauwa haka nakeso kiriƙa yimata bata isa keda gidan ubanki ta wulaƙantakiba itaɗin me”.
“toh Iyah”.
“yauwa bara nabaki maganin magauta kisha dan wannan matar yadda ba imani garetaba tsaf zata jefeki arasa gane meke damunki”.
“toh Iyah wai niko ina Indo tana lafiya”.
“hmm Indo ko shegiyar yarinya data gama yimun rashin kunya rannan ai zata gane kurenta ƴar nan rannan mijinta ya korota na dawo da ita ɗakina daddare bayan kwana biyu segashi ya aiko wai tazo nace ƴar nan tabarni inje in cinyemasa albarka taƙi ta fita ita aiko tana zuwa ta buɗemasa gindi yayitaci yotoni harta faɗamun iskanci ke wannan yarinyar rashin kunyar datayimun tayi yawa”.
duk rashin kunyar Furera seda taji kunyar abinda Iyah tace”ai shikenan”.
nan Iyah ta ɗakko rubutu tabata ta shanye sukayi sallama ta tafi.
Gabda magriba ta isa gida tana shiga taga Ummita nayiwa Isah wanka wani tuƙuƙin baƙin cikine ta turniƙeta tace”ke wai meyasa bakyaji magana ne ko cewa akai dole sekin yimasa wanka”.
“ya haƙuri Furera gani nayi baki dawoba shine nakemasa”.
“ina ruwanki to da inda na tafi koko dole in zan fita se anji inda zani kai Isah zonan”.
maƙe kafaɗa yaron yayi zuwa tayi zata cafkoshi yaƙi wucewa tayi ɗaki tana cewa”zakazo ka sameni yaro badai kai ɗan iskaba”.
tashiga ɗaki samun Idris tayi a zaune zama tayi tare da cewa”kaikuma lafiya ka zauna anan ko hanaka abincin tayi”.
“a’ah ko ɗaya gaskiya abinda mahaifiyarmu da Iyah suke sakamu mukeyiwa Ummita bama kyautawa wlh domin ɗazu bakiji wa’azin da aka yimana a islamiyyaba gaskiya mu gyara kuma baiwar Allah nan yimusu mukeyi ita da ƴaƴanta amma daidai da rana ɗaya bata taɓa canzamana fuska ba inzakizo muyi karatun ta natsu kizo muyi muje mu bata haƙuri kinga kema da zaman nan da kikeyi da ko islamiyya kya shiga bakiji yadda naji ba danaji anata yabon Hafsat a islamiyyar da Yah Amin ya kaimu kinji yadda naji daɗi duk wanda yazo ya ganmu se yace Allah yasa mu gaji halinta kuma kinsan cikinki da mijinki yace banasa bane alhakin sune wlh segashi Allah ya duba zuciyarta yabata gidan hutu dan haka kizo muje yanzu mu bawa Ummita haƙuri”.
jikin Furera ne yayi mugun sanyi tace”gaskiyarka kuwa amma nagode sosai Idris amma nifa kunya nikeji wlh”.
“kidena jin wata kunya taso muje mu bata haƙuri”.
“toh sede kayimana jagora muje”.
“toh muje ko banza da kin kwantar dakai kyaci arziƙi ki koyi abubuwa gida kala-kala”.
“hakane kam to muje” .
nan yayi gaba tabi bayansa samun Ummita sukayi a ɗan kitchen ɗinta tana hura wuta jikinsu a sanyaye suka ƙarasa kusa da ita ƙasa sukayi da kansu suka haɗa baki gurin cewa”Ummita kiyi haƙuri da abubuwan da muka aikatamiki insha Allahu hakan bazata sake faruwaba”.
murmushi Ummita tayi tare da ɗaga hannu ta godewa Allah tace”ku kwantar da hankalinku dama ni ban taɓa riƙar kuba na yafemuku kunji ƴaƴana”.
Furera na hawaye tace”mungode Ummita amma ni yanzu ina zanga ƴar uwata na bata haƙuri domin na cutar da ita nasan ba lallai bane ta yafemunba”.
taƙarasa tana sakin kuka dafamata kafaɗa Ummita tayi alamar lallashi tace”ki kwantar da hankalinki nasan Hafsat bazata riƙekiba kinji ɗiyata”.
“toh Ummita dama inaso idan Bappah yadawo akaini nima islamiyya danko karatun sallah ban iyaba aradu”.
“to shikenan insha Allahu za’ah kaiki bara yayanku ya dawo”.
Bappah da duk yaji komai baƙaramin jin daɗi yayiba nan yashiga kitchen ɗin shima haƙuri shima suka bashi ya nuna shima bakomai nan ta amshi girkin da Ummita take tashiga tayata.
Washe gari misalin goma suka isa Royal Hall Riyadh zama sukayi inda aka tanada Fatimah ce tace”Aunty insha Allahu ita zata ci”.
“Allah yasa kiyita addu’o’in dana baki daughter kinji”.
“toh Aunty inayi dama “.
“yauwa ki gyara zaman niƙab ɗinki sosai kinji”.
“toh”.
“Aunty Allah yabada sa’ah bara naje inada karatu da yara gafda zaku kammala kwaɗayatu ki kirani”.
“uncle zan bika daganan muje shan ice cream”.
“toh ku taho tunda bazaku tsaya kuga karantun Auntynba”.
“magani a tv Uncle”.
“toh”.
“ga hulunanku saboda garin daɗan sanyi-sanyi gwarama ku tafi ma huta da surutunsu wai kana ganin Salman kuwa rabona da ganinsa tin shekaran jiya”.
“toh gaskiya nima bana ganinshi kuma wayoyinsa a kashe bara idan na tashi daga school ma biya ta gida na duba part ɗinsa kafin ku kirani ku kuma ku tawo nasamuku hulunan mutafi”.
“toh Uncle”.
nanya sakamusu suka tafi sha ɗaya daidai aka fara kiran ƴan musabaƙa suka hau wani step ko wannensu ya zauna akan kujera me tambarin ƙasarsa sannan aka fara kiran na United State of America(u.s.a).
Fitowa yayi daga kitchen dagashi se boxer faffaɗan ƙirjinsa a waje wanda yasha tatoo hannunsa riƙe da g cup ɗin tea yanasha yashiga sauka daga step cikin takun zaratan maza masu ji da aji harya sauka main falo zama yayi tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana sha 5DBCP ko wannensu na zaune yana chart Ahmad ne ya aje haɗaɗiyar wayarsa gefe ya ɗauki remote ya kunna tv yashiga canje-canjen tashoshi ba wanda ya kulashi cikinsu har ya kunna wata tasha me suna Africa tv3 remote ɗin yaƙi dannuwa cikin takaici Abbakar yace”kai wanne irin mutum ne da baka da tinani meye na wani kunnomana wa’azi “.
yafaɗa yana ɗaukar farin glass cup me ɗauke da Alcohol a ciki yasha dariya Ahmad yayi yace”wlh remote ɗinne ya ƙage ƙila ba bettery bara nasaka akawomun sena canza sorry my Man”.
ya miƙe kenan a tv akace”muna neman Malama Hafsat Ibrahim da zata wakilci Nigeria”.
Dariya Adam yayi haɗe da cewa”dama ƴan Nigeria suna irin wannan abun arziƙin itako wannan wacece haka zanso naganta kyale sakawa a ɗakko betteryn muganta ko banza maci dariya dan nasan bazasu wani kai labariba”.
dariya gabaki ɗayansu sukayi banda F2 da ya gama shan tea yakwantar da kansa jikin kujera ya lumshe ido kamar me bacci ba abinda yake gani se fuskarta tsaki yayi haɗe da tashi ya tsiyayi ruwa yasha ya kalli tv jiyayi gabansa ya tsananta faɗuwa aje cup ɗin yayi yakoma ya kwanta ya rife idonsa tashi Hafsat tayi cikin nutsuwa harta isa inda zata zauna tayi karatun ba tare da kowa yaga fuskarta ba ta zauna Malamin musabaƙar ne yace”a ƙa’idojin musaɓakar ba’ah faɗamiki banda saka niƙab ba Malama Hafsat”.
cikin kwarewa a harcen larabci tace”naman ne ayi haƙuri Malam”.
tafaɗa tare da yaye niƙab ɗinta gabaki ɗaya su Ahmad haɗa baki sukayi gurin cewa”wow gaskiya Babyn nan ƙarshe ce kodai hayarta ƴan Nigeria sukayo dan batayi kala dasu ba”.
nan gardama ta kauraye a tsakaninsu jin zazzaƙar muryarta tafara karatu ne yasasu ƙara ruɗewa Habib yace”dole a ɗakkomun ita in sadu da ita wlh “.
“ai bakai kaɗaiba kowa cikinmu seyayi ko guys”.
“sosaima kuwa kuma ko nawane zamu biya wlh”.
suka haɗa baki gurin cewa.