HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Surutunsu ne yasa F2 miƙewa zaune yakai hannu ya tsiyayi Alchol yayi niyyar kaiwa bakinsa kenan idonsa ya sauka akan kyakyawar fuskarta glass cup ɗin hannunsa ne ya subuce a hannunsa jikake tass yayinda ya sarƙe yashiga tari.
Tallah! Tallah!! Tallah!!!
Ina kuke masoyana na haƙiƙa kufito ku nunamunso ta hanyar siyan book ɗina me suna BAR RAINA ALLURA(Itama ƙarfe ce) ta wannan account number 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank aiko da shedar biyanka ta wannan number 08108362334 ko transfer vtu ta katin Mtn or Airtel ta wannan number 08108362334 sena jiku.
_*Daga Alƙalamin ƴar M???? *HASKEN RAYUWATA*
MALLAKIN
REAL EESHOW
HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION
PAGE 3️⃣7️⃣➡️3️⃣8️⃣
Ruwa Abbakar ya zuba a cup da sauri ya miƙamasa amsa yayi da sauri ya shanye nan ya sauke wani numfashi me zafi haɗa baki suka sukacemasa"sannu F2".
ido a lumshe yace”yauwa”.
yayinda yakejin wani irin haushinsu Ahmad gyara kwanciyarsa yayi.
Shiru falon ya ɗauka ba abinda kakeji se ƙira’arta tana gama tangimi aka yimata tambayoyi ta amsa ta sauka daga step ɗin datake karatun ta ɗaura niƙab ɗinta ta wuce gurinsu Fatimah ta zauna ba tare da anƙara haskota ba.
Ahmad ne ya furzar da iska me zafi haɗe da cewa”guys gaskiya babe ɗinnan ta haɗu ƙarshe ce wanne plan zamuyi akanta ne danni so nake nanda gobe ko jibi naji mun haɗe kunsan dai ni bani da wasa indai a wannan fannin ne”.
“nima haka wlh kawai abinda za’ai mutura su Bengement su ɗakkomana ita ko ɗiyar waye semun sha romonta”.
“good idea kirasu yanzu su fara gabatar da aikinsu domin wannan aikin nan na saurine domin ni wlh ba yarinyar yau da nike sha’awa se ita”.
“toh bara na kira nasaka tin yanzu afara shirin binsu a ɗakkomana ita”.
“aikinka nakyau Adam yimaza ka kira domin aƙalla kowannenmu zeyi spend 1hr yanayi”.
dialing number Adam yayi tare da cewa”Bengerment kana inane yanzu?”.
“ina Club ɗin One Day ranka shidaɗe meyafaru”.
“kayi maza ka tafi Saudia akwai wata yarinya yanzu zan turamaka da photon ta so nake duk yadda za’ayi ka ɗakkkota saboda tare take da ƴan uwanta banaso asamu matsala yanzu zakayi maza kaida jama’arka ku ɗakkota Nigeria zasu tafi”.
“toh megida angama bara naje nasamesu semu tafi ka kwantar da hankalinka yau da wannan yarinyar zaka kwana megida”.
“yau kayi sauri wannan baƙaramin aiki bane domin yarinyar itace ta wakilci musabaƙar da akeyi a Riyadh itace ta Nigeria 5DBCP ke buƙatar kasancewa da ita a daren yau”.
“toh angama oga bara muje”.
“yauwa good bara na fara bada advance kafin aiki ya kammala”.
“godiya nake Oga”.
nanya kashe Ahmad ne ya miƙe tare da tsalle yace”aikinka na kyau Adam bara naje na shirya domin nizan fara”.
“toh Auta aikafi ga haka ka faraɗin”.
Sosai hankalin F2 ya tashi a zuciyarsa yace”abunda bazan taɓari ayiba kamilar yarinya kusa a ɗakkota danku lalatamata rayuwa abinda baze yiwuba kenan”.
wata zuciyarce tace”kai meye naka na damuwa da damuwarta ne ina ruwanka inma sun ɓatamata rayuwar”.
wata zuciyarce tace”gwara ka ceceta daga shiga tarkon 5DBCP koba komai ai musulmace kuma kayi temakon iyayenta dukda batada kunya”.
tashi yayi tare da yin tsuka yace”bara naje sama koda wani yazo kar a tasheni”.
“toh”.
nanya haye Ahmad ne ya kalli Habib yace”nifa kwana biyu nakasa gane meke damun F2″.
Habib dake chart ne ya ɗago tare da sakin murmushi yace”nima haka amma mood ɗinsa ya canza lokaci ɗaya tun ranar da mukaje Saudia kamar kuma yafara soyayya fa amma da alama bemasan yanayiba”.
waro ido waje Adam yayi tare da cewa”kai gaskiya ban yaddaba da yafara soyayya da zamu sani ko banza kasan irinsu insun faɗa soyayya haukacewa sukeyi”.
“kaima kace wani abu Adam amma ni ina ganin kamar damuwarsa ceta motsa kawai koya tino da Amminsa”.
“hakane kam Amminsa ya tino Allah yajiƙanta yasa ta huta”.
“Ameen”.
Suna cikin magana wata mata tasha atach zabe-zabe tashiga falon fuska tasha mai da mini skirt ɗinta riga iya cibiya tana taunar chewing gum ƙaras-ƙaras bako shape ɗin arziƙi cikin karairaya takarasa falon da suke tace”guys hutawa akeyine ina masoyina yakene bangansaba”.
tafaɗa tare da miƙamusu hannu alamar su gaisa bata hannu sukayi sukayi shaking Abbakar yace”Shona kin makaro yanzu yahau sama “.
“toh kai zomuje inbaka saƙo ka fadamasa ” .
“toh Shona Babe”.
suka ware gefe farr Shona Babe tayi da ido tare da tauna chewing gum irinna ƴan bariki tace”yaufa wanka na ciyo dan mutumin yagani inaso ka faɗamasa idan be amshi soyayyataba sena kashe kaina”.
cikin tsoro Abbakar yace”tofa Shona Babe duk me yayi zafi haka bafa ke kaɗai bace ɗiya mace dakeson F2 ba kinsan dai akwai mata da yawa kizauna kijira ya fito seki faɗamasa da kanki yafiji”.
“toh bara na zauna na jirasa kodai beda lafiyane da bayako sha’awar mace”.
dariya Abbakar yayi haɗe da cewa”ko ɗaya kawaidai shi gani yake tsayawa soyayya ko kula mace duk ɓata lokacine yama fimu lafiya wlh”.
“hmm bara na zauna na jirasa yau senaci nasara akansa barama na haye saman”.
taƙarasa zancenta tare da hayewa saman bene su Ahmad suna mata magana amma ina harta haye dariya sukayi Adam yace”Shona yau kin ɗakko ruwan dafa kanki F2 hmm mudai ƴan kallo ne”.
kowannensu nata dariya.
Ɓangaren su Hafsat ko tana zama Aunty Fido tace”mu bara mu tafi saboda Abbansu Salman yace kwatakwata ba’ah ga Salman ba ku seku zauna”.
tausayinsa ne yakama Hafsat tace”Aunty muma bari mu biki tunda inmun zaunama ba yau za’ah sanar da sakamako ba”.
“toh kije ki sanarwa da wancan Malamin semu tafi Fatimah rakata”.
“toh”.
nansukaje itada Fatimah suka tambaya ba tare da sunkira Abdallah ba suka tafi gida hankali tashe suna yin parking suka sauka shiga cikin gida kowa hankalinsa tashe Abbah suka samu zauna a falo yayi tagumi jiki a sanyaye Aunty Fido taƙarasa inda yake ta ciremasa tagumin da yayi tace”Abban Salman kuma anduba ko ina na gidannan kuwa”.
“eh na duba Abdallah ma na turashi gidajen abokan Salaman duk inda yaje ace bezoba”.
yaƙarsa zancensa cikin tsananin damuwa sosai yabawa su Hafsat tausayi Hafsat tace”Abbah bara mu ƙara dubawa”.
“toh ku ƙara”.
nansuka tafi itada Fatimah jiki na ɓari sun duba ko ina har zasu wuce ɗakinsa dake part ɗinsa se Hafsat tace”Fatimah mu duba bedroom ɗinsa mugani”.
“toh muje amma tunda akace Yah Abdallah ya duba ai anduba amma muje ɗin”.
“kidaizo muje arashin tayi akan bar arha”.
tafaɗa tare da kutsa kanta cikin ɗakin ko ina tsaf kamar na mace ga ƙanshi ƙarasawa sukayi har cikin bedroom ɗinsa ganin ɗakin sukayi da duhu laluben switch Hafsat tayi ta kunna nan take haske ya gauraye ɗakin hangarshi sukayi a cikin bargo ƙarasawa sukayi tare da yaye bargon mezasu gani idanu sun kakkafe gefe guda kuma yayi amai har akan gadon taɓa hannumsa Fatimah tayi taji lakab ƙara suka kwanyara wadda hakan yaja hankalin duk wanda ke cikin masarautar wanda hankan yasa su Abbah suka zabura sukayo bedroom ɗin suma suna ganinsa Abbah ya ciciɓesa yayi falo nan Aunty Fido doctors ɗin Masarautar aka shiga bashi temakon gaggawa wani numfashi yasaki nan doctors suka yimasa allurar bacci suka juya gurinsu Aunty Fido sukace”ku kwantar da hankalinku damuwa ce tayimasa yawa amma insha Allahu inya tashi ze samu sauƙi ranka shidaɗe sannan a sashi yafaɗi abinda ya haddasamasa wannan damuwar a nemamasa abun tun da wuri dan kar asamu matsala”.
“toh mungode insha Allahu”.
nansuka yimusu sallama suka tafi kallon Abbah Aunty Fido tayi cike da damuwa tace”Son meyasa a ransa da har ciwo yake ƙoƙarin shigarsa haka bara yatashi a tambayeshi dan gaskiya yakamata a nemomasa abinda yakeso”.
cikin sanyin jiki yace”toh bara ya tashi muji”.
nan duk suka tafi suka bar Abbah a zaune a gurinsa 1hrs ya tashi da kuka yana cewa”Hafsat idan ban samekiba bansan ya zan kasanceba ki daure ki amshi soyayyata zan dena komai ta dalilinki indai zaki aureni sankine yayimun yawa shiyasa na taɓaki kiyi …”.
be ƙarasaba Abbah ya rifemasa baki tare da cewa”Son ka tsaya muyi magana”.
yunƙurin tashi zaune yayi yakasa Abbah ya temakamasa ya zauna ya kalleshi sauke numfashi Abbah yayi cikin yanayin damuwa yace”Son kayi haƙuri domin Hafsat matar aurece nima kaina naso ace ba matar aure bace da zanfi kowa farincikin haɗa zuri’ah da kamilar suruka kamar Hafsat amma kash tanada aure da ace da yadda zanyi na auramaka ita danayi amma ba dama”.
ɗaga jajayen idonsa yayi cikin yanayin cuta me zafi yace”Abbah waye mijin nata”.
sauke numfashi Abbah yayi haɗe da cewa”Farouk”.
a zabure Salman ya kalli Abbah yace”Farouk kuma Abbah a sanina Farouk aibeda mata”.
“shikuwa Ammi ce ta nemasa aurenta shima yanzu zancen da ake bemasan taba domin lokacin da aka auramasa ita Ammi takirasa ta faɗamasa baze taɓa komawa Nigeria ba kasandai halinsa da baƙar zuciya shinefa Ammi da kanta ta tambayeni kan su zauna anan kafin Admission ɗin da ake nema musu yafito akoyi abubuwa kayimun alƙawarin cireta daga zuciyarka sannan karka faɗawa Auntynku domin banason tasani Son”.
share hawaye Salman yayi tare da cewa”yanzu nasan manufar su Abdallah da suke cewa Aunty bakomai Abbah insha Allahu zanyi ƙoƙarin cireta daga zuciyata amma zansha wahala domin soyayyarta ta shigeni sosai Abbah”.
“yauwa Son Allah yayimaka Albarka insha Allahu, Allah za zaɓamaka mace tagari kayi ƙoƙari kayita addu’ah zakasamu sauƙi”.
“toh Abbah insha Allahu zan tayata kwatar ƴancinta agun F2”.
“yauwa Son”.
suna cikin haka Aunty Fido ta shiga zama tayi kusa da Salman ta kalleshi cikin kulawa tace”Son sannu mekasa a zuciyarka haka da kake niyyar salwantarmana da rayuwarka”.
murmushin yaƙe Salman yayi tare da cewa”wlh kuma Aunty bakomai danasa a zuciyata”.
“toh Son Allah yasa amma dai dole ka faɗamun anjuma”.
“hmm Allah bakomai Aunty”.
“toh Allah yabaka lafiya”.
su Hafsat ne suka shiga suka gaidashi amsawa yayi kamar bakomai dake damunsa nan suka fara hira.