HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Kwance yake ya lumshe ido ba abinda yake gani se hotonta namasa gizo a ido buɗe idonsa yayi ya tashi yaƙarasa gurin fridge ya buɗe ya ɗakko Alchol ya tsiyaya a glass cup da niyyar sha a karon farko dayaji yakasasha maida ita yayi ya ɗauki Jus ya tsiyaya yasha ya aje ragowar akan drower ya koma kan bed yashiga tinani ba zato yaji anfaɗo kansa buɗe sexy eyes ɗinsa yayi kamarna mejin barci ya saukesu akan Shona dake ƙoƙarin taɓa joy stick ɗinsa wani irin baƙin cikinta ne ya turniƙe F2 da tsanarta bazato yaji hannunta a joy stick ɗinsa ɗaga hannu yayi ya ɗauketa da wani gigitaccen mari ya nunata da yatsa yace”ke wacce irin tinkiyace ficemun a ɗaki mara tarbiyya sakarai”.
yafaɗa a harzuƙe yayi kan Shona da sauri ta miƙe tayi waje ko jakarta bata ɗaukaba tayi waje tana ihu tsaki yayi tare da ɗaukar jakarta yabita da ita a stairs yaga tana niyyar fita saboda ruɗu cikin murya me cikeda haiba da kamala da nuna shiɗin Gwarzone yace”ga tsiyarki nan kuma daga yau naƙara ganin ƙafarki sena karyaki nonsense kawai”.
yafaɗa tare da cillamata jakarta ɗauka tayi tana kuka ta fice shikuma yakoma sama.

Dariya su Adam sukai tayi Abbakar yace”ai gwara da yayi maganinta hakafa tacemun wai zata kashe kanta idan F2 be anshi soyayyarta ba zanyi magana kawai naga ta haye sama aigashi nan yayi maganinta nifa ko sha’awarta banayi saboda ita kowama yi yake da ita kamar karya”.
“ai gwara daka barta aidama nasan taje gurinda za’ah saukemata haukan dake kanta yamun daidai da yayimata haka ita inbanda abinta duk ƴammatan dake son F2 yana wulaƙantasu wa’indama suka fita komaima be kulasuba bare ita wadda kowa yasan ragowar maza ce”.
“wlh iska ke wahal da me kayan kara amma ni duk jarabata banasonta wlh”.
cewar Habib yana dariya wayar Adam ce tayi ƙara ɗagawa yayi tare da cewa”Bangerment ya akayi kun ɗakkota”.
“a’ah ranka shidaɗe ance sun tafi amma yanzu gamu mun nufi Nigeria anbamu address ɗinta zamu har gidansu mu ɗakkota”.
tsaki Adam yayi yace”toh kuyi sauri jira muke”.
“toh Oga”.
nanya kashe yace”gaskiya bamu taɓa samun Babe ɗin data wahal damu tamkar wannan yarinyar ba dole mu rama”.
“wlh kuwa”.
sakkowa yake daga step fuskar nan ba annuri kamar kullum dagashi se three quarter se riga armless ƙarasawa yayi ya zauna kusa da Adam yace”guys yakamata kuzo muje muyi refreshing ɗin kwakwalwarmu”.
“toh amma bari muji yadda masu ɗakko yarinyar nan suke”.
ba tare daya ɗago daga danna phone ɗinsaba yace”ok”.
a taƙaice.

Su begements sun isa Nigeria inda suka sauka a filin jirgin saman Aminu kano direct daga nan suka wuce local government ɗin Gwarzo suka nufi ƙauyen ɗannafada acanma Rugar Rumada suka shiga nan suka aje motarsu a nesa suka sauka suka fara tafiya sunyi nisa suka haɗu da wata Bafulatana da kwaryar nono zata wuce tsaida ita sukayi dakyar ta tsaya domin ganinsu da tayi kitikan-kitikan kamar wasu samudawa jiki na rawa tace”lafiya kuyi haƙuri in wani abun nayimuku aradu banyi sallama da yaranaba karku kasheni”.
ɗaure fuska Obama yayi tare da cewa”ba abinda zamu yimiki inkika faɗamana gaskiyar abinda muka tambayeki”.
jiki na rawa tace”aradun Allah zan faɗamuku”.
“yauwa dama wannan yarinyar nakeso ki kaimu gidansu”.
“anyako wannan ba masu jajayen kunnuwa bace kuwa aradu ni bansan wannanba a rugar nan”.
“ke bamason shashanci zamu kasheki Hafsat ɗince baki saniba semu buburma miki wannan wuƙar a fuska”.
jiki na rawa tace”kuyi haƙuri bara nakaiku gidanmu da wata Hafsat ɗiyar wan mijina ce amma dai wannan mejan kunnen gaskiya ba a rugar nan takeba”.
tafaɗa jiki na rawa haɗe rai Bangermen yayi tare da cewa”muje ko kikaimu inkuma itace zaki sanine”.
“toh”.
nan tayi gaba jiki na ɓari suna bin bayanta har suka isa ƙofar gidansu.

Tace”bara nashiga na kiramuku Iyah”.
“toh yimaza dan sauri mukeyi”.
nanta shige samun Iyah tayi tana dakan daƙuwa jiki na rawa tace”Iyah kije waje kinyi baƙi “.
tsaki Iyah tayi tace”ko wanene da wannan tsakar ranar haka bara naje sena cimasa mutunci yanzu hakama Rabe ne yakorota aiko bade gidannanba aradu zasuga ƙarshen bala’i ƴan iska kwai”.
tafaɗa tana masifa ta wuce tana gyara ɗaurin Ilajon dake jikinta tana leƙa ƙofar gida mezata gani kitika-kitikan ƙarti majiya ƙarfi da baƙaƙen kaya zabura tayi zata komai Bengemen yasha gabanta jikin Iyah ne yashiga karkarwa kamar mazari bakina magyagyaɓa tace”kuko menayimuku bayin Allah kodai gamo nayine ni Asama’u”.
Bengemen ne yace”Babah ki tsaya ki nutsu tambayarki zamuyi inkika yimana ƙarya yankaki zanyi”.
murya na rawa Iyah tace”inajinku zan faɗa”.
“yauwa wannan yarinyar muke nema mesuna Hafsat”.
waro ido Iyah tayi ta kalli hoton fes tagane Hafsat saboda tsananin kamanninta da Bappah amma Iyah seta shafawa idonta kashin kaji tace”aradun Allah bansantaba wannan ai irin masu jajayen kunnuwace wanemu da haɗa iri da irin wa’innan manyan a ƙauye”.
“akace kuma kinada jika Hafsat”.
damm gaban Iyah ya yanke ya faɗi ta fashe da kuka tace”aradun Allah ƙarya ne ni jikata a ƴan muradi tayi aure harda yaranta huɗu wato Kande ce ta tahomun daku danta cimun mutunci”.
Iyah taƙarasa zancenta tare da fashewa da matsanancin kuka Bengemen ne yace”ya haƙuri Iyah kikoma gida bara muje mungode anyako Obama daidaine kwatancennan yaza’ayi ace haɗaɗiyar yarinyar nan ace a wannan ƙauyennan take mu tafi mu ƙara tambaya”.
Iyah ce cikin kuka tace”gaskiya dai aradu bamu santaba”.
nan suka yimata godiya suka tafi Iyah nashiga gida ta wuce ɓangaren Kande tace”aradun Allah da kincemusu jikatace da kinga tsiya ƴannan aradu”.
nan Iyah ta tujare Kande ta fuce tana cewa”haka kurum a haifomun ƙaya ina zaune ƙalau kome tayimusu oho koda yake ance rannanma ankamata tana satar gandar sarki ita ta jiyo daban murje idoba da tini sede labarina”.
nanta koma ta cigaba da dakanta.

Suna zaune a falo wayar Adam tayi ƙara ɗauka yayi tare da cewa”yadai an samota?”.
“a’ah ranka shidaɗe zamu ƙarasakawa a turomana Address ɗinta domin wannan gaskiya ba daidaibane wani ƙungurmin ƙauye aka kaimu”.
tsaki Adam yayi tare da cewa”toh”.
ya kashe wayar Ahmad ne yace”an ɗakkota”.
“inafa wrong address aka basu inko aka ɗakkota dole muɗauki revenge”.
“wlh kuwa”.
F2 dake danna wayarsa zaka ɗauka hankalinsa baya kansu ne ya sauke ajiyar zuciya me ƙarfi wadda taja hankalin kowa na falon ya kallesa!!!!!

Tallah! Tallah!! Tallah!!!
Ina kuke masoyana na haƙiƙa kufito ku nunamun ƙauna ta hanyar siyan book ɗina mesuna BAR RAINA ALLURA (Itama ƙarfe ce) ta wannan accoun number 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank aiko da shedar biyanka ta wannan no ba 08108362334 ko tranfer kati ta wannan no 08108362334 sena jiku siyan nagari maifa kuɗi gida.

Daga wannan page ɗin zan ɗan tsaya saboda Exam ɗinda zamu fara semun gama zan cigaba kuyi haƙuri

Votes and Comments
plz Share

Kutemaka kuyi sharing dan masu karatu susan da wannan sanarwar.

Daga Alƙalamin ƴar mutanen Gwarzo.✍️utanen Gwarzo.*???? *HASKEN RAYUWATA*

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION

PAGE 3️⃣9️⃣➡️4️⃣0️⃣

    Yi yayi  kamar besan shi suke kallo ba yana danna phone ɗinsa ba tare da ya ɗago ba ya daɗa haɗe rai  cikin tambayar rainin hankali yace"lafiya naga kun wani tsareni da ido kamar wanda baku taɓa gani ".

murmushi Adam yayi dan inda sabo sun saba da tambayar rainin hankalin F2 yace”wata ajiyar zuciya mukaji ka sauke me ƙarfi shine muka kalleka danjin meya faru”.
murmushin gefen baki F2 yayi wanda ya ƙara bayyanar da tsintsar kyawun da Allah yayimasa yayi tare da cewa”to sarakan sa ido bakomai se hankalinku ya kwanta”.
tafa hannu Abbakar yayi tare da kallon 5DBCP yace”guys yau wacce rana rabonda muga murmushin F2 har munmanta komeyasashi wannan farin cikin oho bayan yau 5DBCP suna cikin ɓacin ran rashin samun wannan yarinyar”.
miƙewa F2 yayi tare da yin miƙa yace”the weather is so nice guys kutaho mu tafi tunda kun gama jin abinda kuka tsaya ji”.
yaƙarasa zancensa cikin halin ko inkula da damuwar 5DBCP kallonshi Ahmad yayi yaga yadda fuskarsa ta ƙara saki da alama yana cikin farinciki yace”gaskiya ne nawan yau wacce rana ammafa Adam dolene mu hukunta yarinyar nan wlh ko ƴar waye”.
“kaikama faɗa wani yaji domin yanzu ni nafasa spending ɗin 1hrs seta gane shayi ruwa ne wlh ita wacece da zata ɓatama 5DBCP lokaci har haka “.
“wlh kuwa zata sanine hmmm badai ta faɗo tarkonmu ba semunyi kuma mun dagargazata”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button