HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Tun daka nesa ya hangeta zaune a garding tana rera karatun Alqur’ani megirma wasu hawayene masu zafi suka zubomasa ya share ya nufi gurinta zama yayi a kujerar dake facing ɗinta Hafsat ko naganin Salman ya zauna a kusa da ita jikinta yafara rawa a zuciyarta tace”ga wannan sakarannan bara na tashi tinkan ya taɓamun jiki “.
dakyar tabari takai aya ta miƙe tsam tashiga tattara kayanta jiki na ɓari wayarta ce ta faɗi ta duƙa zata ɗauka taga yakai hannu ya ɗauka zata shiga yimasa masifa taga zube a gabanta hawaye masu zafi nabin kuncinsa yace”Hafsat kiyi haƙuri da abubuwan dana riƙa yimiki so ne ya jawo haka tin randa na fara ɗora idanuna akanki naji ina masifar sanki yayinda nakejin bani da burin da ya wuce najiki a jikinaba rannan da kika kwaɗamun kwalba naje nasamu Abbah na sanarmasa da nasamu matar aure sosai yayi farinciki koda ya tambayeni wacece na sanarmasa da kece anan ne yake sanarmun da ke matar Farouk ce sosai naji banji daɗiba ta sanadin haka cuta takamani kiyi haƙuri ki yafemun sheɗan ne yasani nayita taɓaki insha Allahu bazan sake taɓa jikin wata ɗiya mace ba matsawar ba matata bace”.
yaƙarasa zancensa tare da fashewa da matsanancin kuka jikin Hafsat ne yayi mugun sanyi lokaci ɗaya tace”kadena kuka Yah Salman ban taɓa riƙeka a zuciyataba dama ni na yafemaka Allah ya yafemana baki ɗaya dan Allah ka tashi”.
“nagode Hafsat inaso daga yau kizama ƙanwata duk abinda ya shigemiki gaba ki tambayeni kanki tsaye zankuma tayaki kwatar ƴancinki gurin F2”.
“toh Yah Salman nagode da wannan matsayi daka bani amma dan Allah inaso kayimun wata alfarma”.
gyara zamansa yayi a kujerar dake kallonta tare da cewa”faɗi kanki tsaye sis anmiki”.
“kayi haƙuri karkace na rainaka Yayah dan Allah kadena saka sarƙa da ɗan kunne sannan kariƙa saka kaya normal kaya ba ɗan wando iya guiwaba”.
“angama Sis ɗina daga yau na dena”.
“nagode Big Bro”.
nan sukayita hirarsu cikin nishaɗi da fahimtar juna.

IYAS POV

Zaune Ummita suke da Bappa suna hirarsu sukaji muryar Iyah tace”Salamu Alaikum”.
da murnarsu suka fita suka haɗa baki gurin cewa”wa’alaiki salam Iyah sannu da zuwa”.
taɓe baki tayi tare da cewa”yauwa “.
Ummita ce tace”Iyah ina yini”.
taɓe baki tayi tare da cewa”bashakka ansamu duniya dole a daɗa shanyemun ɗana to ta Allah ba takiba aradu da ban wuniba kya ganni”.
ta wuce fuuu tashiga falo ta zauna Bappa ne ya kalli Ummita yace”kiyi haƙuri watarana se labari ba’ah taɓa dauwama a abu ɗaya”.
murmushi tayi haɗe da cewa”meye abun bani haƙuri Iyah mahaifiyata ce nima kadena bani haƙuri kajeka gaidata bara na kawomata ruwa”.
jin Iyah sukayi tace”ko se uwar taka tabaka izinine sannan zakazo”.
jiki na rawa ya shiga ɗakin ya zauna ƙasa tana kan kujera cikin girmamawa yace”gani Iyah ina yini”.
“lafiya ƙlau jiya wasu kitika-kitikan ƙarti sunzo neman shaffafa da mai ƴar lelenka domin banda Allah yayi da sauran kwanana da tini sede labarina sun kasheni tawa bata jamunba ta wani tajamun me ake da irin tsintacciyar mage mara asali duk wanda yaƙiji bayaƙi ganiba ba wanda ya isa ya shafamun kashin kaji kwana nayi ina gudawa dan haka daka yau zankoma gidan ƴar uwata Jummala se abu ya lafa na nakoma bame jamun mutuwa lokacina beyiba nama sanarwa da duk mutanen gidan kowa ya fashe dan karsu dawo “.
taƙarasa tare da miƙewa Ummita dake aje ruwa a gaban Iyah ce tace”Iyah ga ruwa kisha”.
wani kallon banza ta watsamata ta juya zata fita su Furera sukayi sallama washe baki tayi tare da cewa”ina kuka shigane haka”.
rungumeta sukayi Furera tace”wlh Iyah muna makaranta Ummita sannu da gida”.
“yauwa Furara “.
“makaranta kuma”.
“eh”.
“mekukeso kucemun makaranta ko yawon barikin kuma kuka koma”.
zame jikinta daga na Iyah tayi tare da cewa”karki ƙara cewa ƴar uwata yawon bariki neman ilimuke kikasa muka tsani ƴar uwarmu kawai dan wata son zuciyarki inma munyi yawon barikin ai iyawa ne infutsari banzane kaza yanzu mungane gaskiya”.
ɗora hannu aka Iyah tayi tare da cewa”yau mezan gani ni Hajara tsinananniyar yarinya ta rabani da kowa nawa senayi maganinki aradu bazan barkiba”.
nan ta tafi tana masifa .

8:30pm
Zaune suke a bedroom ɗinsu Hafsat na yiwa Fatimah kitso Aunty fido tashigo cikin farinciki tare da cewa”ku kuna nan kuna wani kitso har an faɗi sakamako “.
damm gaban Hafsat yabada Fatimah tace”Aunty wacce ƙasar ce taci”.
“Nigeria yanzu duk gidan tv daka kunna karatun Hafsat akeji gobe za’ah bada kyaututtuna kufito kusha kallo gasu Abdallah can suna kalla”.
“toh”.
wasu siraran hawayen farincikine suka zubowa Hafsat Aunty Fido ce ta rungumeta tace”gaskiya Ummita tayi sa’arh haihuwa mahaƙurci mawadaci ki kirasu ki sanarmusu nima bara na kira su Ammi”.
“toh Aunty”.
nan Hafsat tayi dialing number Yah Amin bugu ɗaya ya ɗauka tare da cewa”ƙanwata ina tayaki murna ga Ummita nan se kukan farinciki takeyi bara na bata”.
cikin shashsheƙar kuka tace”nagode Yayah “.
nan yabama Ummita cikin muryar kuka Ummita tace”ɗiyata abar alfaharina kidena wannan kukan farincikin haka “.
share hawayenta tayi sukayita murna nan suka gaiggasa da ƴan uwanta sannan sukayi sallama kiran Zully yashigo ɗagawa tayi suka gaggaisa tayimata murna sannan sukayi sallama takira Billy.

9:30am
Suka isa gurin taro zama sukayi inda aka tanazarmusu sannan m.c ya buɗe taro da addu’ah bayan angama ne yace”salamu Alaikum “.
“wa’alaika salam”.
“munama kowa barka da isowa wannan taro me albarka inda za’ah gudanar da karrama haziƙan dalibai guda uku na ƙasashe uku wanda suka samu nasarar cin wannan musabaƙa da aka gudanar kafinnan zamu kira haziƙar dalibar da tayi nasarar zuwa na ɗaya data sanyayamana ziciyoyinmu da daddaɗan karatunta wato Malama Hafsat Ibrahim in tana kusa muna jiranta kafi sarki Abdul’jalal da manyan baƙi su ƙaraso”.

Kallon Hafsat Aunty Fido tayi tare da cewa”kifita daughter Allah yabada sa’ah ana kammalawa zamu wuce”.
“toh”
nanta miƙe cikin hijabinta burmeme har ƙasa da niƙabinta cikin nutsuwa tashiga tafiya harta isa ta zauna gurin da zatayi karatu m.c ne ya kalleta tare da cewa”Malama Hafsat a ɗan ɗaga niƙab inba damuwa “.
“toh”.
nanta cire ta ɗakko wani siririn farin glass ta saka kowa na gurin kallonta ya shigayi saboda tayi mugun kyau m.c ne yace”Malama Hafsat kizaɓi surar data yimiki ki fara muna saurarenki”.
“toh”.
nanta gyara zama tashiga karanta suratul Nisa’ih.

Zaune yake a office idanunsa a lumshe ba abinda yake gani se fuskarta buɗe ƙofa akayi ya buɗe lumsassun idanunsa ya sauke akan ƙofa wata baturiya ce ta shiga hannunta riƙeda files jikinta sanye da farin uniform cikin girmamawa ta ƙarasa gabansa ta gaidashi ba tare daya buɗe idoba ya amsa aje files ɗin tayi tare da cewa”sir akwai patient da yawa wa’inda za’ah musu aikin zuciya”.
“ok ganinan zuwa “.
“toh”.
nanta fita tashi F2 yayi yashiga bedroom ɗin cikin ofice ɗinsa ya canza kayansa zuwa green na theater yayi kyau sosai yafito sak balarabe har ze tafi yaji ba abinda yakeso face yaga fuskarta ɗaukar wayarsa yayi dake gefensa yayi dialing number Ammi bugu ɗaya Ammi ta ɗauka tare da cewa “salamu Alaikum”.
“wa’alaki salam Ammi anyini lafiya”.
“lafiya ƙlau me sunan malam ya aiki”.
“Alhamdulillah dama Ammi tambayarki zanyi wani abokina ne yake cikin matsala”.
“inajinka me sunan Malam wa kenan a ciki”.
“wanine watarana yaje wani store ya haɗu da wata yarinya zata faɗi ya ɗan tareta tana tashi ta tureshi tayimasa rashin kunya tayi tafiyarta memakon tayimasa godiya shikuma abokin nawa tindaka ranar komai yayi ganinta yake ko rife ido yayi ganinta yake shine nace bara na tambayarmasa naji me hakan yake nufi”.
murmushi Ammi tayi wanda har F2 yanajin sautinsa tace”mahaukacin sonta yake wanda shi kansa besan yanamata ba sannan kuma da alama zesha wahala kafin tasoshi duk yadda akai da abunda ya taɓa haɗata dashi”.
ƙirjin F2 ne yabada damm inda yaji maganganun Ammi namasa yawo a kwakwalwa lokaci ɗaya jiɓi yashiga ketomasa dukda sanyin a.c dake aiki jiyayi yawun bakinsa ya bushe yakasa cewa komai Ammi dake dariya ƙasa-ƙasa ce tace”lafiya magajin Malam naji kayi shiru”.
dakyar yasamu nutsuwarsa ta dawo yace”bakomai Ammi anyako so ne kuwa ba rashin kunyar da tayimasa bace ta tsayamasaba kuwa?”.
“ba wata rashin kunya sonta yake me tsanani ma kuwa”.
“toh zan sanar dashi se anjuma zanshiga theater”.
murmushi tayi tare da cewa”toh se anjuma”.
nanya kashe wayar haɗe da furzar da iska me zafi yace”what so never ko soyayyar zanyi inrasa wadda zanso se wannan mara kunyar yarinyar never F2 da kula kwaila “.
yaƙarasa zancensa cikin ɗaga muryacanza kaya yayi yaji wayarsa na ringing ƙin ɗauka yayi seda aka kira ana uku sannan ya ɗauka tare da yin shiru daga ɗaya ɓangaren Adam yace”F2 mu zamu wuce Saudia ɗakko yarinyar nan yanzu ake taron bata kyaututuna ita tayi first position semun dawo”.
Adam na shirin kashe wayar yaji F2 yace”bara nazo mitafi”.
“toh”.
nanya kashe cikin sauri ya fita ya tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button