HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Ƙarasawa Bengement yayi jikin motarsu F2 Adam ya zuge glass Bengements yace”Oga anbamu address ɗinta waccan yarinyar tace basu daɗe da tafiya ba tare da iyayenta”.
“toh kubisu ku ɗakkota muma yanzu zamu juya ma haɗu a U.K zakaji alert”.
“okay Oga semun dawo”.
nan suka shiga mota suka nufi Airport Abbakar ne yace”da harnaji daɗi da aka kawota amma yanzu duk raina ya ɓaci dole mu biya naɗansha abinda ze saitamun brain ɗina”.
“wlh nima haka to mu biya Happiness muɗan kora driver muje”.
“toh oga”.
nansuka tafi suna isa sukayi parking sauka sukayi gabaki ɗayansu suka shiga gurin wani ƙawataccen mall ne me gurin abubuwa kala-kala suna shiga F2 yayi hanyar wani haɗaɗen garding basuyi mamakiba kawai suka nufi inda zasusha kayayyakinsu.

Yana isa yaga wata balarabiya mijinta yasa ta rife ido kneeldown yayi yazaro rose flower a aljihunsa ya miƙamata tana buɗe ido a mamakinsa seyaga ta rungume mijinnata tayimasa kiss tace”Happy valantine day my Nisful-hayat”.
murmushi F2 yayi tare da sosa kansa yayi baya dan ganin yadda mijin ya kwaƙume matarsa saurin kauda kansa yayi tare da yin baya ya furta”Valantines day”.
yayi murmushi ya nufi wata hanya nan take ya ɓullo ta cikin store ɗin gurin kayan masoya gani yayi mutane nata wucewa da kayan bawa masoyansu irinsu teddy binsu yashigayi da kallo idonsa ya sauka kan wani haɗaɗen teddy White da heart red a jikinsa yayi kyau ƙarasawa yayi gurin yasa wani me aiki ya ɗakkomasa murmushi yayi tare da yima teddyn kiss tinowa yayi da zancen Ammi ne yasa a zuciyarsa yace”anyako zan iya kuwa amma kuma tace nayi ƙoƙari na faɗamata kodako zatayimun rashin kunya faɗuwar gaba asarar namiji”.
wata zuciyarce tace”gaskiya yakamata ka ɗauki shawarar Ammi ba hakaba zaka iya samun matsala a halin yanzu ka gama gane kana sonta”.
wata zuciyarce tace”to wani hanzari ba guduba a ina zaka ganta?”.
wannan tambayarce tasakashi cikin wani yanayi ya ɗauka ya haɗa da wasu teddies ɗin masu kyau white and red yasa aka ɗaukarmasa aka cira a atm ɗinsa aka sakamasa a boot ɗin motarsu ya shiga seda ya daɗe sannan suka fito suka nufi Airport suka hau Jet ɗinsu suka tafi.

Wani katafaren mansion suka tsaya akayi horn getman ya wangale get suka cinna hancin motarsu ciki sosai gidan yayi mugun burge Hafsat nan suka shiga tsayawa faɗin tsarin gidan ɓata lokacine ya haɗu over parking sukayi a gurin adana motoci fitowa sukayi nan masu aikin gidan suka taryesu tare da ɗibar kayansu suka shiga dasu suma suka shiga zama sukayi a wani haɗaɗen falo tare da cewa”wash”.
murmushi Aunty Fido tayi tace”wato angaji kenan tashi zakuyi kuyi wanka ayiwa su Anun semuzo muci abinci mu kwanta mu huta kafinnan su Abdallah sun dawo”.
“toh Aunty”.
nan suka kama hannun yaran suka nufi stairs.

4:00pm
Zaune suke a dining masu aiki sungama serving ɗinsu fara ci sukayi Abdallah ne yakalli Fatimah yace”acici mala’ikun tauna yanzu se a sassaita ci karatu akazoyi kar azo a baje ciki aita ci kamar gara mufa yanzu zamu samu sauƙi Aunty gara ta tafi”.
cikin shagwaɓa Fatimah tace”Aunty wai kinji nice gara sarkin cin abinci “.
dariya kowa na gurin yayi Aunty Fido ta hararesa tace”rabu da sarkin tsokana shida wandama yakaishi ci”.
“wlh kuwa Aunty kinga idan yazage yayita loma yana santi har waigi nakemasa besaniba”.
dariya suka kwashe da ita nan suka cigaba da cin abincinsu cikin soyayya washe gari Aunty Fido dakanta takaisu har school tayimusu ƙawaye sannan suka tafi cikeda kewar juna.

Su Bengement na sauka a Kano suka kira wani abokin aikinsu wato Emanualla suka nunamasa address ɗinda aka basu nanya yimusu kwatance anan suka gane ai rugar Rumada ne Bengement ne ya kalli Obama yace”kai amma gaskiya tsohuwar nan ta renamana hankali ai garinsu ne wannan kwatancen zata gane kurenta”.
“dole tagane kurenta ba ruwanmu da shekarunta ko itace dabino yau semunyimata ɓalli-ɓalli a ɗuwawu wlh”.
nan suka nufi ƙaramar hukumar Gwarzo ta jihar Kano har suka isa Rugar Rumada ƙofar gidansu Iyah shiga sukayi kansu tsaye tararwa sukayi ba kowa a cikin gidan mamakine yakamasu Obama yace”wanne tsohuwarfa inajin sun gama raina mana hankali sun ware aiko zamu duduba gida-gida inbata semu tafi”.
“haka za’ai mu duduba semu wuce”.
nan suka fita suka shiga dudubawa har suka isa gidan Lantana dake ƙarshen gari Iyah najinsu tashige ƙarƙashin gado ta ɓoye dudubawa suka shigayi sukaga ba kowa tsayawa sukayi Obama ne yace”ammafa wannan tsohuwar yau da munganta da semunmata ɓalli-ɓalli ladan wahalar data bamu bakaji yadda nikejin jikinaba duk nagaji”.
“wlh kuwa mu wuce mu sanarwa dasu Oga karmuyi laifi”.
“toh”.
nansuka tafi Iyah ko najin za’ah yimata ɓalli-ɓalli cikinta ya karta gudawa ta ɓallemata seda Lantana ta temakamata ta gyara kanta saboda tsoratar da tayi.
tace”Lantana yauni nashigesu da wannan yarinya ta zamarmun ƙaya tawa bata jamunba ta wani na niyyar jamun tagama yawon dandinta tayi sata anata nemana yanzu naji wa’innan yaran nacewa wai da sunganni sesunyimun ɓalli-ɓalli a ɗuwawu ni Hajara naga takaina Allah ya isa Sa’ah da kika jefani cikin wannan halin”.
taƙarasa tare da fashewa da kuka Lantana ce tace”kidena kuka tunda an auna arziƙi da basu gankiba “.
“hakane bara naɗan zaga cikina yaƙara ɓaci”.
“toh”.
nan Iyah ta shiga bayi.

AFTER TWO DAYS

Fitowa yake daga cikin hospital ɗinsa yana gyara agogon hannunsa yaji yabigi mutum mace ya gani sanye da niƙab ta tafi zata faɗi ya rungumeta tsam a jikinsa inda itakuma taƙara lafewa a faffaɗan ƙirjinsa jiyayi wani ƙayataccen murmushin dabe shirya yinsa bane ya kuɓucemasa lokaci ɗaya zuciyarsa tashiga azazzalarsa da cewa”Allah na godemaka bara na sauke ajina nabi shawarar Ammi na furtamata “.
wata zuciyarce tace”karfa ajinka ya zube”.
wata zuciyarce tace”ka rife ido ka faɗamata kawai ka wuce gurin”.
nan yakai hannu daidai fuskarta ze!!!!!!

Tallah! Tallah!! Tallah!!!
Ina kuke masoyana na haƙiƙa ku fito ku nunamun ƙauna ta hanyar siyan book ɗina me suna BAR RAINA ALLURA (Itama ƙarfe ce) akan farashi mafi sauƙi #200 ta wannan account number 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank ko katin Mtn or Airtel ta wannan number 08108362334 aiko da shadar biyanka ta wannan number 08108362334 sena jiku.

Votes and Comments
Plz Share to others

_*Daga Alƙalamun ƴar mutane???? *HASKEN RAYUWATA*

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION

PAGE 4️⃣3️⃣➡️4️⃣4️⃣

       Ze buɗa kenan iska ta bankaɗe niƙab ɗin mezegani Shona anci bleaching fuska se kyallin mai take ƙara lafewa jikinsa take niyyaryi taji an saketa ƙasa  tafaɗi cikin ɓacin rai F2 yace"ke wacce irin tinkiyace mara tarbiyya dik abinda nayimiki rannan beshiga jikinkiba ko to zan koyamiki hankali".

yayi kanta saurin tashi tayi ta ruga tsaki ya saki ya wuce fuuu ta gaban Abbakar ya shige motarsa yajata fuuuu.

Murmushi Abbakar yayi tare da ƙarasawa inda Shona take yace”gaskiya Shona shawarar dazan baki kifita harkar F2 yau ranshi yakai ƙololuwar ɓaci baki kyautaba wlh”.
“aini dama baso nike in kyautamasa ba wato dama akwai wadda yake taɓa jikinta kenan amma ni yake rainamun hankali to wlh ka faɗamasa sena kashe kowa yake tare da ita dan indai ban sami F2 ba bawadda zanbari wlh ta aureshi dama ashe zancen da Hussy ta faɗamun ashe gaskiya ne wai taganshi rungume da wata a wani store a Riyadh to ko wacece zata gane kurenta dan bazan bartaba sena kasheta wlh koma wacece har wani murmushi ya saki a tinaninsa itace kallifa wannan vedeon dandai fuskarta bata fitoba ya kareta shi kaɗai ake gani”.
mamakine yakama Abbakar yace”Shona anya ko kina cikin hankalinki kuwa tinda nike a rayuwata da F2 bantaɓa ganin ya kula mace da sunan so ba hasalima duk ɗinbin ƴammatan da suka mutu akansa baya kulasu gani yake ɓata lokacinsu sukeyi”.
“kalli ka gani wannan bashi bane da wata”.
ansa Abbakar yayi meze gani F2 rungume da yarinya me niƙab ya yayemata nan take dogon gashin yarinyar ya bayyana mamaki abun yabashi yace”tabbas F2 ne amma itako wannan yarinyar wacce me sa’ah ce haka da har ya kulata naso an nuno fuskarta naga wacece ammafa koda banga fuskartaba nasan ta haɗu tinda ya kulata wow kalli gashinta dan Allah wannan yarinya ƙarshe ce akwai kyau daka gani tinda harta ja hankalinsa yau dole 5DBCP susan da wannan abun farincikin”.
yaƙarasa zancensa cikin zumuɗin lalubo wayarsa yashiga turawa cikin takaici Shona tace”amma kabani mamaki a cikin 5DBCP na zabeka munzo nan tare danka saita komai seka ɓige da tura wannan abun baƙincikin a wayarka har wani rawar ɗuwawu kake zaka nunawa abokanka inkunsa wata bakusan wataba ko wacece dole ta baƙunci lahira”.
“keeh harni kike faɗawa maganganu san ranki anƙi tayaki baƙin cikin kije ki kasheta karki fasa zakiga abinda ze faru dake wannan yarinya tafiki komai wama ze haɗa daka gani kuma ƴar gidan mutunci ce ba irinkiba ballagaza taya F2 zesoki”.
yaƙarasa zancensa tare wucewarsa yabarta tanata kukan maganganun daya faɗamata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button