HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

WAI WAYE ADON TAFIYA

WANENE SARKI FAROUK?

 Sarki Farouk adalin sarkine me sanin darajar ɗan adam da talakawansa yanada mata biyu  Fatimah da Bilkisu  Fatimah itace uwar gida se Bilkisu amarya Fatimah nada yaro me suna Nuraddeen Bilkisu amarya ko Allah bebata haihuwaba sosai Nuraddeen yake samun kulawa tako ina sakamakon  shikaɗaine ɗa a gurin sarki Farouk  sosai Fatimah takejin daɗi domin ita kaɗaice me ɗa a cikin gidan koba komai shine magajin sarki Farouk shiyasa take taka kowa a cikin masarautar hankalinta kwance Nuraddeen nada shekaru 7 ciki ya bayyana a jikin Gimbiya Bilkisu  sosai kowa yayi farinciki da hakan amma banda Fulani Fatimah da hankalinta yayi mugun tashi   nan taje gurin bokanta kan ya temaketa yabata maganin da za'ah zubar da cikin dake jikin gimbiya Bilkisu anan ne bokanta ya tabbatarmata daba yadda za'ayi cikin ya zube cikin se an haifeshi koda ta tambayeshi meza'ah haifa anan yake shedamata data kwantar da hankalinta mace za'ah haifa sosai tayi murna da jin zancen boka nan takoma gida cikin farinciki bata ƙara bi takan cikin jikin Bilkisu ba har wata tara yayi ta santalo ɗanta namiji sosai hankalin Bilkisu yayi mugun tashi dajin namijine gashi guri ya ƙure dataje gurin boka inta   fita za'ah ce baƙin ciki takeyi haka ta haƙura ranar suna yaro yaci suna Muhammad bayan shekaru talatin yara sun kammala karatunsu a ƙasar Malaysia suka koma gida sosai mahaifinsu yayi farinciki nanya sanar dasu yayimusu mata buɗar bakin Nuraddeen se cewa yayi ba wata budurwa da za'ah zaɓamasa shize zaɓi matarsa da kansa yanama da wadda yakeso shikuma Muhammad ya amshi zancen cikin farin ciki ya duƙa yayi godiya hakanne yasaka sarki Farouk yayiwa ɗansa alƙawarin bashi sarauta dukda bashine babba ba ƙara duƙawa yayi godiya washe gari aka naɗa sarki muhammad bayan sati ɗaya aka ɗaura musu gabaki ɗayansu har Nuradeen daya kawo tashi zaɓin haka rayuwa ta cigaba da tafiya bayan shekaru uku matar Muhammad tahaifi ɗanta namiji aka sakamasa sunan mahaifin memartaba wato Farouk bayan suna da sati biyu matar Nuradeen tahaifi ɗiyarta mace yarinyar takoma hakan yasaka matarsa cikin damuwa ganin yadda ta damune yasaka  shi sanarwa  Fulani damuwar da matarshi tashiga nan Fulani ta yanke shawarar zataje wani biki masarautarsu ta Agadaz    sesu tafi harda ita da shi sosai yaji daɗin wannan shawara lokacin tafiya yayi suka hau jirgi suka tafi Niger da zasu dawo se kakarshi ta buƙaci yabarta taɗan huta nan suka tafi a hanyarsu ta dawowa sukayi  wani mummunan accident ɗin jirgin sama suka mutu shida Fulani sosai hankalin kowa ya tashi bayan tagama takaba tace zata koma  kasarsu sarki me murabus wato sarki Farouk ya kirata koda taje kallonta yayi cikin so da ƙauna yace"zaki auri ɗana Muhammad?".

saurin ɗagowa tayi ta kalli Maimartaba murmushi yayimata tare da nunamata alamar da gaske yake shiru tayi se can tace ta amince sosai sarki Farouk me murabus yayi farin ciki nan ta tafi da magriba ya aika aka kiramasa ɗansa Muhammad ya sanarmasa beji daɗin zancenba saboda yana masifar son matarsa Khadija saboda biyayyar da yikewa mahaifinsa yasa ya amince sosai Sarki Farouk yaji daɗi yayita sakamasa albarka nan sarki Muhammad ya tafi ya aika aka kiramasa Fulani Khadija ya sanarmata duk abinda yake faruwa cikin damuwa a tinaninsa zata fishi jin haushi se yaji tace Allah yabamu zaman lafiya meye abun damun kai kasandai Abbah baze taɓa cutar dakaiba bare kuma wadda zaka aura me tarbiyya ce kodama becemaka dama jiya naso nima nayimaka wannan zancen murmushi yayi yace to Allah yabamu zaman lafiya ina Son yashiga ne ina missing ɗinsa tinda aka kaishi makarantar nan me 6-6 anyako ba canzamasa zanyiba nasaba kullum injisa a jikina a’ah ka barshi a makarantarsa toh nan sukayita hirar soyayya domin baƙaramin son junansu sukeba har takai takawo duk wanda ya kwana koda ɗayane a masarautar nan yasan irin son da sarki Muhammad yake yiwa matarsa Gimbiya Khadija da ɗanta Farouk wanda kakarsa Gimbiya Bilkisu tamaidashi kamar ɗanta saboda son da takemasa wato Ammi.

Bayan fitar Zainab daga gurin sarki Farouk me murabus ta nufi ɓangarenta zuciyarta cike da tinani kala-kala samun ƙawarta Rukayya da tayi tin zuwanta garin tayi tazo zama tayi suka gaisa Rukayya tace”lafiya ƙawata naga hankalinki tashe?”.
“wlh Rukayya ba lafiya ba sirikinane ya kirani aida kinsan yau zan koma ƙasarmu shine yake cemun zan auri sarki Muhammad dakyar na amince saboda ina tinanin wuya zansha yadda sarki Muhammad yake nuna son matarsa da ɗansa Farouk shiyasa hankalina yayi mugun tashi narasa me zanyi jikina duk ya mutu”.
dafata Ruƙayya tayi tare da cewa”meye abun damun kai ki kwantar da hankalinki indai kinasonshi?”.
“inasonshi man amma ainasan bazemun sonda yakeyiwa matarsaba”.
“toh ki kwantar da hankalinki zan kaiki inda sonda da zemikima seyafi nata wlh”.
cikin farinciki Zainab tace”dan Allah da gaske kike “.
“wlh da gaske nike amma kibari auren muga kamun ludayinsu”.
“toh Allah yakaimu”.

Bayan sati ɗaya aka ɗaura auren sarki Muhammad da matarsa Zainab akakai amarya ɗakinta Fulani Khadija dakanta ta raka gimbiya Zainaba turakar sarki tayimusu nasiha zata tafi kenan sarki Muhammad yajawota ta faɗa jikinsa ba kunya ya haɗe bakinsa da nata idonshi ya rife wata irin kunyace takama Fulani Khadija ta kwace jikinta a nashi tace”amarya ga angonki nan nabarmikishi”.
dakyar gimbiya Zainaba ta haɗiya wani abu daya tsayamata a maƙogoro tace”godiya nike babbar Yayah agaida Farouk”.
“zeji”.
nanta raɓa ta wuce yayinda sarki Muhammad kebinta da wani shu’umin kallo harta ɓacemasa yana juyawa ga mamakin Zainaba setaga ya wani haɗemata rai ya zauna ɗan nesa da ita a wannan daren ai banda ta matsamasama da baze bata haƙƙintaba sosai abun nashi ya tayarmata da hankali da sassafe ta kira ƙawarta Ruƙayya ta sanarmata nan Ruƙayya tace “zasu gane kurensu zan kaiki gurin boka Matsatsaku ki zayyanemasa komai aikinsa kamar yankan wuƙa yike sekun zama tamkar raƙumi da akala ke dashi zebiki itakuma wannan tsinannar seta barmiki gidan gabaki ɗaya”.
“godiya nike muje”.
washe gari sukaje gurin boka Matsatsaku suka zayyanemasa komai nan ya dubamusu yace sede a hankali ze rabasu domin matar tana addu’ah sosai shida zeɗan iya yimasa wani abun domin duk randa ba a ɗakinki ya kwanaba matarsa tana sakashi yana addu’ah zeɗan rage sonda yake mata itada ɗanta godiya tayima boka yabasu magani ta zubawa sarki Muhammad gani tayi ba wani canji akan sonda yakewa matarsa bayan wani lokaci ciki ya bayyana jikin Zainaba ba’ah wani yi shagaliba saɓanin gimbiya Khadijat da cikinta itama ya bayyana baƙaramun murna sarki yayiba sosai Zainaba takejin takaicin yadda sarki yake nuna banbanci ƙiri-ƙiri har lokacin haihuwarsu yayi Zainaba ce ta ruga haihuwa aka sakama ɗanta suna Marwan bayan wata biyu Khadija ta haihu aka sakama ɗanta suna Abdallah bayan wani lokaci zamansu yaƙi canzawa gashi ƙiri-ƙiri sarki Muhammad yake nuna son Khadijat da ƴaƴanta hakan ya hassala Zainaba da sukaje gurin boka tacemasa so take duk yadda za’ayi a raba sarki Muhammad da Khadija dariya boka ya sheƙe da ita yace in an rabasu ai akwai sauran rina a kaba saboda yadda sarki Muhammad keson ɗansa Farouk ya wuce duk inda kike tinani koda taji haka se cewa tayi to shima a haɗa hardashi ya tsanesu nikuma duk abinda kakeso zan baka dariya boka yayi yacemata shi jikinta kawai yakeso intabashi zemata aikin da setasha mamaki kallon ƙawarta Ruƙayya tayi nan Ruƙayya ta nunamata data amince hakanko akayi ta amince boka yayi lalata da ita sannan suka bashi kuɗi me yawa yabasu magani yace a zuba a abincin da zasuci su duka ukun zatasha mamaki nan suka tafi ranar dake girkinta ne ta samu damar zubamusu sukaci abincin sarki Muhammad lokaci ɗaya yafara ja baya da matarsa da Ƴanƴanta biyu amma kuma dukda haka yana caring ɗinsu amma ba kamar da ba .

Zainaba na yaye Marwan tasamu ciki abin mamaki sarki yayita ririta cikin kamar ba’ah taɓa yimasa haihuwaba bashida zance sena cikin watan cikin takwas Allah yayiwa sarki Farouk rasuwa sosai kowa yaji mutuwar bayan wata ɗaya da kwana bakwai Zainaba ta haihu inda dukda a lokacin ba’ah dena alhinin mutuwar sarki Farouk ba haka Zainaba tasa ƙawarta taje gurin boka yabata maganin da aka gusarmasa da tinaninsa ya mance da kowa se abunda tace ranar suna tasa har kiɗe-kiɗe akayi aka sakama yarinya suna Maryam bayan suna da wata ɗaya Khadija tashiga laulayi kamar zata mutu ba abinda take buƙata se ƙanshin turaren mijinta koda Zainaba taji meke faruwa dariya tayi tayi satar fita taje gurin boka tace so take ya bata maganin da sarki zeji Khadija tana warin jaɓa hakanko akayi yabata ta saka amintacciyar kuyangarta ta zuba a ruwan wankan Khadija tayi wanka da ruwan tana fitowa ta shirya ta kwanta aka sanar da isowar sarki part ɗinta nan yashiga yana shiga ɗakin yaji wani irin wari yashiga dube-dube haka yaƙarasa inda take ya zauna anan ne yaji ai ita keyi jiyayi baze iya jurewaba yace warin me kikeyi hakane Khadija shinshina jikinta tayi taji ita ƙanshin turarema takeyi shigowa su Fatouk sukayi da ƙaninsa suka ruga da gudu zasu rungume mahaifinsu ya dakamusu tsawa yacemusu suma wari sukeyi karsu ƙara gisgirin taɓa jikinsa Farouk bejiba saboda ya saba da jikin mahaifinsa yaje ze rungumesa ya kwaɗawa Farouk mari ya fice a fusace a wannan rana Khadija tayi kuka kamar ranta zefita ta rungume ƴaƴanta sukayita kuka koda labari yaje kunnen gimbiya Bilkisu aikawa tayi aka kiramata sarki Muhammad tayimasa faɗa memakon taji yace zeba Khadija haƙuri setaji yanata zayyanemata laifin Khadija da yaranta sosai tayi mamaki anan takira Khadija tabata haƙuri tacemata tabata Farouk nan ba musu tabatashi.

Bayan wata takwas abubuwa da yawa ciko harda wata muguwar tsana data shiga tsakanin sarki Muhammad da ɗansa Farouk sarki ya dena kwana ɗakin Khadija ya dena shiga sabgarta saboda fitsarin kwancen da Zainaba taje gurin boka aka sakama gimbiya Khadija duk randa sarki yake a ɗakinta setayi fitsarin kwance randa ba a ɗakin yakeba ba fitsarin da takeyi hakanne yasa sarki yaƙara tsanar Khadija yakoma komai gimbiya Zainab ce ta iyashi baƙin cikin abubuwan da suke faruwa ya haddasawa Khadijat ciwon zuciya ba tare da kowa yasani ba daga ita se Farouk da a lokacin yanada shekaru goma sha biyar cikinta Khadijat na wata tara duk tarin da zatayi setaga jini rannan tana cikin tari Farouk yashigo ganin jinin baƙaramin tayarmasa da hankali yayiba ya nufi gurin mahaifinsa ya sanarmasa buɗar bakinsa se cewa yayi shiya ɗoramata sosai Farouk yaji takaicin mahaifinsa yakoma gurin mahaifiyarsa anan yasamu Abdallah na zubamata ruwa tana wanke bakinta zama yayi suka gama suka fito kuka Farouk ya fashe da kuka Abdallah ma ya fashe dashi suka rungume mahaifiyarsu tana kuka suna yi har seda sukayi me isarsu sannan sukayi shiru shigowa sarki yayi da gimbiya Zainaba suna toshe hanci sarki ya kalli Farouk yace”kai wato ɗazu daka shiga ka sacemata agogon hannunta ko to bani baza’ah kai uwartaka asibitin ba koni na ɗoramata”.
“Alhaji dakabarshi danasan abinda ze kawomu kenan ba dubata mukazoma ni”.
tafaɗi maganarta cikeda ƙissa Farouk yayi rantsuwa bemaga agogontaba sarki yaƙi yadda seda yayiwa Farouk tatas sannan suka tafi bayan suntafi sosai Khadija sukasha kuka da ƴaƴanta nan Farouk yacema mahaifiyarsa a sanarwa da kakarsa wato Hajjo ta Adamawa Umminsu tace batason kowa ya sani har Ammi karya faɗawa tana addu’ah in Allah na sane dasu haka Farouk da Abdallah suka haƙura saboda koda yaushe haka mahaifiyar tasu take cewa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button