HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Zaune suke itada ƙawarta a ƙuryar ɗakinta tace”Ruƙayya nagafa har yau be saketaba itakuma mayyar duk irin rashin mutuncin da yikemata taƙi tace ya saketa”.
“ta ina zatace ya saketa ai mayyace anyako yau da daddare ba mu nemo Goje ya kwanta a ɗakinba a matsayin suna lalata kekuma sekiyi sauri ki kirawo sarki ina ganin in akayi haka ze saketa kinga shikenan seki zama Fulani”.
“aiko kema kince wani abu wannan itace shawara kinga kuma dole ya saketa shikenan nayarda kwallon mangwaro na huta da kuda”.
“hakane kam anjuma sekisan yadda zakiyi kisa a shigarda Goje “.
“toh inko abinnan yafaru zanbaki kyauta me tsoka ga wannan kifara dasu”.
taƙarasa zancenta tana miƙawa Ruƙayya damin kuɗi da magriba ta raɓa ta shigar da Goje ɗakin gimbiya Khadija.

Gimbiya Khadija na idar da sallar isha’ih ta kwanta sakamakon baccin da takeji ta kwanta bacci yayi awon gaba da ita gimbiya Zainaba a gigice tashiga tana cewa”sarkina ashe waccan munafukar munafuntarka takeyi yanzu naga tashiga da wani ƙato ɗakinta cikin sanɗa “.
a gigice sarki ya miƙe tare da cewa”muje aidama na faɗamiki batada hali kike wani kareta”.
nan suka tafi suna zuwa suka samu Goje yana kwance cikin bargon yana ganinsu ya yaye bargo ya zabura da gudu yayi waje sarki ko kan Khadija yayi ya kwaɗamata mari tashi tayi a gigice tana waige-waige yakuma ƙaramata da gudu gimbiya Zainaba ta nufi ɗakin uwar soro wato Ammi ta sanarmata abinda yake faruwa kafin kace meye wannan ko ina ya ɗauka ankama Fulani Khadija da kwarto seda yayimata mari uku sannan yace”na sakeki saki uku bani bake Khadija kin cuceni kin zalinceni Allah ya isa tsakanina dake bazan taɓa yafemiki ba kwarto a gidana”.
kuka Khadija ta fashe dashi tace”wlh mijina ban kawo kowaba hasalima bani da lafiya”.
gimbiya Zainaba ce tace”rifemana baki munafuka ina ganin lokacin da kika wuce dashi maciya amana kawai”.
kuka Khadija ta ƙara fashewa dashi ta kalli Ammi tace”wlh Ammi ban kawo kowaba ƙarya takemun ya sakeni ina zan saka kaina a rayuwata”.
Ammi jitayi bakinta yayimata nauyi takasa furta komai cikin kakkausar murya sarki Muhammad yace”ki tattara inaki yanaki kibarmun gida da wannan tsinannen cikin naki ki nemi ubansa”.
tashi tayi tana ganin jiri tafara tafiya tana tari jini na fitowa ta hanci ta baki da gudu Farouk da Abdallah suka rungumeta suna kuka cikin zuciya Farouk ya ɗago ya kalli mahaifinsa yace”in mahaifiyata ta mutu sena kasheka”.
nan take jini ya ɓallema gimbiya Khadija Ammi da Farouk ne suka kaita kan gado Abdallah da gudu ya kira doctors ɗin masarauta aka shiga bata temakon gaggawa harta haifi ɗiyarta mace jini be tsayaba sosai hankalin Ammi ya tashi itako gimbiya Khadija cikin zafin cuta tacewa Ammi a kiramata ƴaƴanta hakan ko akai nan Ammi tasa aka kirasu Farouk daketa kuka a waje suna zuwa suka kama hannun mahaifiyarsu suka fashe da kuka shafa kawunansu tayi cikin zafin cuta tace”Farouk ka kula da ƙannenka kaji ku zauna a hannun Ammi insha Allahu Allah ze kawo muku ɗauki Ammi ga sunan su zauna a hannunki banajin zan tashi”.
cikin kuka Farouk yace”Ummi bazaki mutuba zan zama likitan zuciya nayimiki maganin ciwon zuciyar dake damunki tinda Abbah ya kasa yimiki ni zan miki”.
gimbiya Khadija zatayi magana tari ya ɓallemata nan take jini yashiga anbaliya ba abinda take se salati har rai yayi halinsa kuka Farouk ya fashe dashi ya nufi fada yana kuka yace”kaji daɗi ta mutu ta barmaka duniyar seka zuba ruwa a ƙasa kasha”.
ya fice a fusace nan da nan aka sanar da mutuwar gimbiya Khadija jama’ar masarautar sunji mutuwarta saboda ba wanda yake kuka da ita kowa alherinta yake faɗa da Ammi takirasu Hajjo ta sanarmusu sosai suka shiga tashin hankali domin dama ƴaƴansu uku duk mata da Khadija da Sa’adatu da Zahara’u da Firddausi Sa’adatu itace ƙarama ta ɓace gurin bikinsu Khadija anzo kawo amarya Kano abinda akayi kenan ansha nema an rasa ba’ah sake ganintaba cikin kuka sarkin Adamawa yace akaita kafin su ƙaraso yanzu zasuzo nan Ammi taje dakanta gurin sarki Muhammad kan jana’izar Khadija yace bazashiba haka aka tafi aka kaita bashi sosai abin yayiwa Farouk ciwo yaje har fada ya faffalawa sarki Muhammad magana hakanne yasa yace ya barmasa gidansa Ammi ta hana da akai addu’ar arba’in su Hajjo sukace zasu tafi da yarinyar da ko suna sarki Muhammad be sakamataba seda aka gwagwadata aka tabbatar jininsa ce sannan ya sakamata suna Fatimah dakyar Ammi ta bari nan suka tafi harda Abdallah aka barwa Ammi Farouk tindaka nan Farouk ya ƙudiri aniyar yin duk abinda ze ɓata sunan Familynsa daga ƙarshe Ammi tasa aka kaishi ƙasar waje karatu anan ne ya haɗu dasu Adam suma ankaisu suna karatunsu suna jan magana sun gagari kowa har aka sakama ƴan clip ɗinsu suna 5DBCP saboda sunada mugun haɗari ba abinda basayi har suka kammala Farouk Muhammad Farouk yafito a babban likitan zuciya.

WANENE ARƊO
Arɗo bafulatanin ƙaramar hukumar Gwarzo ne cikin ƙauyen Ɗan nafada Rugar Rumada yanada matarsa mesuna Hajara yaransu biyar duk maza da Shafi’u da Iro , Murtala Audu ,Jamilu ba wanda suka saka a makaranta sede suna karatun allo shima ɗin ba wani kwakwaraba domin a ƙauyen ko hanyar mota babu bare makaranta cikin jahilci suke rayuwa ruwan shama na rafi suke ebowa su sha suyi wanka haka rayuwa ta cigaba da tafiya har zuwa lokacin da Iro yafara zuwa cirani gari, gari domin neman kuɗi harya samu wani uban gidansa ya siyamasa babur me ƙafa uku wato adaidaita yafaraja a cikin garin kano yana kaiwa uban gidansa balance yauma kamar kullum misalin tara da rabi na dare yana cikin jan adaidaitansa yana gudu be auneba yaga yarinya budurwa a gabanshi ya taka burki amma ina seda yayi awon gaba da ita adaidaitan duk ya samu matsala be tsaya bi takan adaidaitanba ya nufi wani ƙaramun clinic da yarinyar dakyar asamu jinin da yake zuba ta kanta ya tsaya likita ya fito yace waye ya kawo wannan yarinyar iro yace shine nan ya umarcesa daya bishi office ɗinsa binsa yayi jiki na ɓari suna zuwa likita ya shedamasa data bugu sosai har hakan yayi sanadiyyar ta manta da kowa sosai hankalin Iro ya tashi saboda besan ta inda ze fara neman iyayenta ba a ranar yaje ya samu uban gidansa ya sanarmasa da abinda yasameshi nan yace besan zanceba kuɗinsa kawai yasani ba yadda Iro ya iya haka yakoma rugarsu ya sanarwa da iyayensa duk abinda ya faru sosai hankalinsu ya tashi nan Arɗo mahaifin Iro ya yanke hukuncin siyarda shanayensa guda biyar aka biya uban gidan Iro yarinya dataji sauƙi se Iro koma Rugarsu ya shedawa mahaifinsa ya za’ayi da ita anan ne yace masa ya taho da ita gida kafin Allah yasa ta dawo cikin hayyacinta hakan ko akayi ya ɗauketa suka koma Rugarsu aka sakamata suna Sa’ah ba tare da sun san sunanta ne na gaskiya ba mahaifiyarsu Iro wato Iyah ta amsheta hannu bibiyu shikuma ya cigaba da zuwa cirani amma gadi yakoma yakeyi saboda rashin jari haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda shaƙuwa me ƙarfi tashiga tsakanin Iro da Sa’ah idan ya dawo gida sa’ah bataso yakoma tare suke komai har zuwa lokacin da za’ayi auren ƴan uwan Iro anan Arɗo yace shima Iro ya fitar da matar aure anan ne Iro ya nuna yanason Sa’ah sosai mahaifinsa yaji daɗin hakan inda Iyah tayi tsalle ta dire ba yadda za’ayi ɗanta ya auri tsintattar mage nan Arɗo ya nunamata bata isa ba aka ɗauramusu aure gabaki ɗaya bayan shekara ɗaya matar Iro ta haifi ɗanta namiji aka sakamasa sunan Arɗo wato Aminu bata daɗe da haihuwa ba Arɗo ya rasu sanadin ciwon daji bayan shekaru biyu Hajara(Iyah ) dakanta ta nemowa ɗanta auren Lantana saboda tsanar da tayiwa Ummita har aka ɗaura auren Lantana Iyah ta ɗauki son duniya ta ɗoramata bayan shekara ɗaya Lantana tahaifi ɗanta namiji ranar suna aka sakama yaron suna Idi bayan wata biyar da haihuwar Idi Ummita tahaifi ɗiyarta mace me kama da mahaifinta ranar suna aka sakama yarinya suna Hafsat ,Hafsat nada shekara biyu Lantana taƙara haihuwar ɗiyarta mace aka sakamata Furera haka rayuwa ta cigaba da tafiya harsu Hafsat suka kai shekara biyar watarana Iro ya dawo daga cirani yasamu matansa Lantana da Ummita yacemusu yanason ya saka yaransa a wata makaranta dake cikin garin Gwarzo bokoce da Islamiyya kamar yadda yasaka su Aminu sosai Ummita ta nuna farin cikinta tace hakan yayi kallon Lantana Iro yayi da take cika tana batsewa yace saura kuma wannan karonma ki hana yarinyarki zuwa tinda kin hana Idi zuwa banza tayi dashi taje ta sanarwa da Iyah nan Iyah ta tada ballin tsiya bame kaimata jikoki bariki sede yakai ƴaƴan Ummita dan ita bame ɓatamata suna a gari nan ya ɗauki Hafsat yakaita makaranta kullum take zuwa itakuma Furera ta riƙa tallar nono kasuwannai tinda Hafsat tafara makaranta shikenan Iyah ta ƙara tsanar Ummita da ƴaƴanta mutanen garima suka riƙa kyararsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button