HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

5:00pm
Ba abinda kakeji se ƙarar kiɗa dake tashi yayinda ƴammata da maza aketa cashewa gurin irin deep haskennan ne hakan yasa kowa yake harkar gabansa Zaune yake a bedroom ɗinsa yana danna phone ɗinsa Abbakar ya shiga bakinsa da sallama ya ƙarasa inda F2 yake kwance ya zauna yace”Bro ka tashi kai kawai muke jira”.
ba tare daya kalli Abbakar ba yace”zuwa ina kenan”.
“wani guri zamu ga kayanka nan kasaka “.
yaƙarasa zancensa tare da miƙamasa wata ƴar jaka ansa yayi tare sa zuge zip ɗin jakar anan yaga kaya irin na jikin Abbakar kalace kawai ta banbanta kallonsa yayi da alamar tambaya Abbakar yace”wani operation zamu gabatar a 5DBCP club na gidannan”.
“ok ganinan zuwa”.
nan Abbakar ya fita tashi F2 yayi ya saka kayan da Abbakar ya kawomasa wandon iyakarsa guiwa rigarkuma meɗan ƙaramin hannu nan faffaɗan ƙirjinsa yaƙara fitowa ga zanen tatoo ɗinsa da duk ya bayyana sarƙa da ɗan kunne yasaka sannan ya parker kitson dake kansa inka gansa seka zata wani ƙasurgumin arnene nan ya saka agogo da takalminsa black ya ɗaura baƙin glass ya fita yana buɗe ƙofa yasamu su 5DBCP zaune kowa ya haɗe cikin kaya irin nasa abinda ya raba na wani dana wani colour ce kawai ta banbantasu suna ganinsa suka haɗa baki gurin cewa”yoyo wazop men gaskiya wankannan yayi kutashi mu muje Emeka yace mu kawai ake jira”.
“toh mu wuce”.
nan suka tafi a jere har suka isa Club ɗin nasu suna shiga wutar gurin ta ɗauke gabaki ɗaya har seda suka isa tsakiyar gurin sannan wani haske ya gauraye gurin yayinda wani haɗaɗɗen kiɗa ya kauraye gurin duk inda ka duba hoton Hafsat ne da niƙab ɗinta da wanda suke rungume da F2 bin kowanne hoto F2 yariƙa yi da ido yana mamakin yadda duk su Ahmad suka shirya wannan abubuwan ba tare da saninsaba tafi gurin ya ɗauka nan suka zauna a kujeru guda biyar da suka kasance na zamansu kiɗa yafara tashi ƴammata da samari aka shiga cashewa inkagansu kamar ƴaƴan arna kai kace ba ƴaƴan musulmai saboda yadda zakaga mace da namiji ana mu’amala nansu Ahmad suma suka shiga sa ƴammatansu aka shiga cashewa seda sukayi rawa me isarsu sannan aka shiga shaye-shayen abubuwa serving ɗinsu F2 akayi aka zuba musu giya a cup biyar suka ɗauka suka haɗa hannun sukayi charls har ya kusa kaita bakinsa ya tinada abinda Hafsat ta faɗamasa ya aje yasa aka kawomasa jus yasha.

AFTER 1 WEEK

Suna shiga suka aje jakunnansu Hafsat tace”kai gaskiya Fatimah karatu akwai wahala kalli yadda dukna rame”.
“hmm Aunty kenan wai nan dan Allah ma ya temakeki ba medicine kikeyiba ninan ni kaɗai nasan wahalar da nike sha naso ace tare muke law ɗinnan dake da naji daɗi”.
“aiba wani daɗi kowanne karatu yanada wuya Allah dai yasa mu dace bara nakira Ummita ƴan tafiya naji shirin da sukeyi”.
“Ameen ya Allah”.
nan Hafsat takira Ummita bugu ɗaya ta ɗauka murmushi Hafsat tayi tace”Ummita ankusa zama hajiya”.
“wato ina wasa dake eyi”.
“ya haƙuri Ummitana anyini lafiya”.
“lafiya ƙlau ya karatu?”.
“Alhamdulillah dama kira nayi naji ya ake ciki da shirin tafiyar”.
“lafiya ƙlau ai Hajiya tasa angama yimana komai yanzu hakama Bappanku ya tafi ƙauye ya sanarwa dasu Iyah kiyimana godiya gurin Hajiya dan Allah tana ɗawainiya damu tunda Aminu ya tafi Madina”.
murmushi Hafsat tayi tare da cewa”toh insha Allahu zanyimata godiya yanzu wai yaushe ne tafiyar taku”.
“gobe da musalin takwas na dare ga ƴar uwarki Furera ta dameni da inbata”.
“toh Allah yakaimu Furera anyini lafiya”.
“lafiya ƙlau Aunty Hafsat ya karatu”.
sosai Hafsat taji daɗin yadda ƴar uwarta ta kintsu tace”Alhamdulillah yasu Yah Idiris”.
“lafiya ƙlau”.
“yanzu ku kaɗai za’ah bari a gida ko”.
“eh wlh”.
nan suka gaisa da Idiris sukayi sallama.
Fatimah ce tace”bara inkira Hamma Farouk ace ina garinnan koya kira ƴar ƙanwarsa yaji lafiyarta amma se yayi shiru dani”.
taɓe baki Hafsat tayi tare da cewa”kizo muci abinci gashi an kawomana”.
“toh”.
Fatimah ta faɗa tare da yin dialing number F2 seda tayi kira uku sannan ya ɗaga tare da cewa”Hammana inata kiranka baka ɗaukaba ace Hamma ina cikin garinnan kaƙi nemana ko bakomai”.
murmushi F2 yayi tare da cewa”sorry sweetheart bacci nike toya kike ya karatu”.
“Alhamdulillah inaso naga Hammana ina missing ɗinka sosai wlh”.
“ok yanzu ke kina hostel ne ko kina ina”.
“ina gidan Abbuh na nan “.
“ok to anjuma zanje Orphanage ɗina kisa driver ya kawoki “.
“wow kace yau zanga Hammana bara na tashi na shirya “.
“ok tom sekin zo”.
nanya kashe wayar cikin zumuɗi Fatimah tace”wow Aunty ki shirya muje Orphanage ɗin Hamma yace inje can yau zeje “.
Hafsat ko cin abincinta takeyi kamarma batasan da ita Fatimah takeba a zuciyar Hafsat tace”Orphanage kuma kodai kunnena ne bejiba wannan mara tarbiyyar ne ze wani buɗe Orphanage sede in na wani mutumin arziƙin bade na wannan mara tarbiyyarba”.
tana wannan zancen zucin taji Fatimah tana cewa”plz Aunty dan Allah muje”.
“ayya dana rakaki zanyi wani Assigment nima danaga gurin ai”.
“tom shikenan bara nayi wanka na shirya senaje na dawo”.
“ok”.
nan Hafsat tashi ta haye sama tabarta murmushi Fatimah tayi tace”Aunty nasan ba wani Assigment da kike dashi kawaidai bazaki gurin Yayah bane ina bayanki kema ki rama abinda yayimiki yasan mata nada daraja”.
nan tayita maganarta harta gama shiryawa ta bi bayan Hafsat samunta tayi tana waya da Ammi wucewa toilet tayi kai tsaye tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar riga peach tayi rolling ta kalli Hafsat dake karatun Alqur’ani megirma tace”Aunty zan tafi”.
“ok sekin dawo inkin dawo zuwa Isha’ih yakamata muɗanje ko shan ice cream ne danni yau shi nikeson sha”.
“toh Allah yakaimu bye”.
nanta tafi.

A orphanage ta sameshi zaune cikin yara yana basu alawa cikin kulawa sosai Fatimah taji daɗi ta ƙarasa inda suke harya gama bama yaran suka zauna sunata hirarsu har akayi magriba yaje masallacin cikin orphanage ɗin yayi sallah sannan ya raka Fatimah har ƙofar gida tashiga yakoma tana shiga tasamu Hafsat ta shirya tsaf cikin wata haɗaɗɗiyar lafaya red me adon golden ta naɗata tayimata kyau gefanta kuma niƙab ɗinta murmushi Fatimah tayi tace”har an shirya kenan “.
“eh na shirya kije kiyi sallah semu wuce”.
“A’ah nayi a orphanage ɗin Hamma mutafi kawai bara nima naɗan canza kaya nasaka niƙab”.
“toh muje”.
nan Fatimah taje ta canza kaya tasaka lafaya itama sukasha niƙab ɗinsu Hafsat akan niƙab ɗin aka zizara farin glass nan suka fita driver ya buɗemusu suka shiga yace”ina mukayi ranku shidaɗe”.
Fatimah ce tace”Aunty ina zamu”.
“kawai muje wani guri meɗan kyau ko ince wanda yake tashe a garinnan maɗan buɗe ido”.
“wlh kuwa”.
nan driver yajasu suka tafi har suka isa wani katafaren mall parking yayi nansu Hafsat suka shiga kowacce cikinsu ta nufi gurin abinda takeso Hafsat gurin turaruka ta nufa ko zataga turarenta tana zuwa ta duba wani turare tana dubawa taga babu seta ɗauki wani turare wayarta tayi ƙara ɗagawa tayi ta kara a kunnenta ta ɗauki turaren tashiga tafiya tana waya tana cikin tafiya taji tayi karo da mutum ɗaga idon da zatayi taga gabaki ɗaya 5DBCP ne a gabanta wayarta ce ta faɗi jitayi jikinta yashiga rawa dakyar ta dake zuciyarta ta duƙa ta ɗauki wayarta tacewa F2 “sannufa”.
ta wuce mamaki 5DBCP sukayi suka saka a bibayanta Hafsat na isa gun Fatimah tace”mu tafi gida”.
“toh”.
nansuka tafi suka shiga mota suka tafi wa’inda su Adam sukasaka su bisu suna fitowa basu gansuba sede ƙurarsu da suka gani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button