HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

IYAS POV

Bappa ne duƙe gaban Iyah yagama zayyanemata komai kan harkar tafiyarsu Saudia!!!!

Sister dan Allah idan kin karanta kiyimun share zuwa groups ɗin da kike ciki shine zallar soyayyar da zakiyimun koda bana ganinki.

A duk inda kike dan Allah kiyimun comments koda ban ganiba

Tallah! Tallah!! Tallah!!!
Ina kuke masoyana na haƙiƙa ku fito ku nunamun ƙauna ta hanyar siyan littafina mesuna BAR RAINA ALLURA (Itama ƙarfe ce) ciki farashi mafi sauƙi #200 kacal ta wannan account ɗin 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank aiko da shedarka ta wannan number 08108362334 ko katin Mtn or Vtu ta wannan number 08108362334 sena jiku.

Votes and comments
Plz share to others

_*Daga Alƙalamun ƴar Mu???? *HASKEN RAYUWATA*

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION

PAGE 4️⃣7️⃣➡️4️⃣8️⃣

        Abin mamaki se Bappah yaga Iyah ta washe haƙora tace"kardai kacemun jikata to duk ya akayi tayi kuɗi haka ni bansaniba amma dai Iro ka munafunceni banji daɗin abinda kayimunba aradu aida ka sani ka faɗamun nima na roƙeta da yanzu nima dani hajjin bana ze gudana kai amma aradu kaci amana".

mamaki ne yakama Bappah yarasa abinda zece gani yake kamar a mafarki wai Iyah kecewa Hafsan a zuciyarsa yace”Allah na godemaka daka ganar da mahaifiyata tin guri be ƙoremataba”.
yana wannan zancen yaji Iyah nacewa”wai Iro ba dakai nikebane dakayi shiru dani duk ya akai haka duk tayita faruwa ku kasa sanarmun nasa a gari duk akabi aka tsani yarinya da uwarta saboda fita garin da takeyi ta wuni ashe suɗin HASKEN RAUWARMU ne aradu nayi nadamar abinda na aikatawa Sa’ah ita da ɗiyarta yanzu ka tashi muje na bata haƙuri domin duk ni yanzu kunyarta nikeji aradu ashe ta silarta zamuci arziƙi”.
“haba Iyah kinsan Sa’adatu bazata taɓa riƙeki a zuciyarta ba”.
“eh dai dukda haka ka tashi muje na bata haƙuri”.
“toh Iyah”.
nan Iyah ta yafa gyalen Ilajon dake jikinta suka fito kaciɓus sukayi da Lantana ƙanwarta Iyah na ganinta tashiga zayyanemata komai tana kukan farinciki sosai Lantana tashiga farinciki tace”shiyasa Yayah inke faɗamiki komai na duniya ɗan haƙurine bare na tabbata Iro baze yiwu ya zuba ido yana kallon ɗiyarsa tana karuwanciba be ɗauki matakiba”.
“wlh kuwa yanzu dai muje in nemi gafararsu inhuta”.
“ai Iyah Hafsat tana makaranta sede Sa’adatu”.
“inane makarantar tasu bade garin masu jajayen kunnuwaba de ko”.
murmushi Bappah yayi yace”eh Iyah tana can”.
“aiko dai Allah yasa karsu cutarmun da jika dan aradu basu da mutunci nida sukazo nan zasuyimun ɓalli-ɓalli Allah ya temakeni na ɓoye aida tini ana wani labarin ba wannanba”.
“hhh Iyah kenan aiba abinda zasuyimata tare take da mijinta acan”.
“auto madallah naɗauka ita kaɗaice”.
“a’ah”.
suna wannan zancen sukaji sallamar Babar Haladu da Haladu na kuka ya duƙa gabansu Iyah yana kuka yace”dan Allah Babah Iro ka temakeni adawomun da Furera aradu cikin jikinta nawane tinkafin aurenmu nayimata shi kutemakeni dan Allah”.
Babar Haladu ce tace”dan Allah Iya ayimana rai Haladu yace baze iya rayuwaba inba Furera kitemakamana”.
cikin masifa Iyah ta kama ƙugu tace”ke yanzu Hasiya har kunada kunyar zuwa gabanmu kan zancen Furera to bari kije in gayamiki ko mutuwa Haladu zeyi bashi ba Furera bayan cimana mutuncin da kukayi a gari kuka watsamana ƙasa a ido kan cikin jikinta ba nashi bane kukaja akayita yimun gori a gari jikata tayi cikin shege to ko mutuwa Haladu zeyi sede yayi sakaran banza”.
“haba Iyah a temakemu dan Allah zan riƙa kulada Furera sosai inason ɗan cikin jikinta sosai kutemaka Bappah”.
numfashi Bappah ya sauke tare da cewa”a gaskiya bazance Furera takoma ɗakinkaba sede idan munje tace zata koma idanko ta nuna bazata komaba bazanmata doleba saboda yanzu ita ba yarinya bace”.
dakyar Iyah ta aminta su tafi saboda ballin tsiyar data tayar suna isa Gwarzo suka tarar gidan a rife an tafi kai Furera Asibiti tana naƙuda suna isa cikin asibitin Furera na haihuwa tahaifi ɗanta namiji amma bezo da raiba tasha wahala seda aka sakamata ƙarin jini sannan akabarsu Ummita dasu Iyah suka shiga samunta sukayi kwance ƙarasawa sukayi gurinta Iyah tace”sannu Furera kin auna arziƙi Allah ya maisheda na aike”.
“ameen”.
“sannu Furara”.
“yauwa Ummita”.
nansu Bappah sukayimata sannu Bappah ne yafita waje segashi ya shigo bayansa su Haladu ne da mahaifiyarsa Furera na fara’ah ta ɗaure fuska tayi kamar bata taɓa ganinsaba Haladu cikin zumuɗin ganin yadda Furera tayi kyau ta goge ya nufeta cikin murna saurin ɗagamasa hannu Furera tayi tare da fashewa da kuka tace”karka matso inda nike Allah ya isa bazan taɓa yafemakaba mekazo yi gurin wadda ta gama zubar da mutuncinta a waje wadda ta shigarmaka da cikin shege gidanka wadda gidansu basu gaji tarbiyyaba Haladu nayi danasanin saninka a rayuwata nayi danasanin kasancewata matarka ada nasoka sona haƙiƙa kaikuma ka ƙini lokacin da nike tsaka da neman temakonka da kulawarka ka koreni kajamana abun gori a rugarmu wanda baze taɓa gogewaba har zuri’armu su bar duniyar banason ganinka na tsaneka yanzu niba matarka bace saboda nayi idda ɗakuma daka nuna ba naka bane Allah ya ɗauki rayuwarsa sekaji daɗi”.
taƙarasa zancenta tare da fashewa da wani matsanancin kuka me cin rai tausayinta ne yakama duk mutanen gurin yayinda Haladu ya duƙa har ƙasa.

Yace”dan Allah Furera kiyi haƙuri ki yafemun aradu bazan sake yimiki hakaba nima banji daɗin abinda nayimikiba ko Babah Wuro?”.
“eh aradu Furera yanzu mungane kurenmu ki yafemana ko abinci Haladu bayaci yanzu saboda zallar soyayyarki data addabi rayuwarsa kiji tausayinmu dan Allah”.
murmushi takaici Furera tayi tace”nina rigada na gama iddah ba gidanka da zankoma ni yanzu Allah ya nunamun haske nafita daga cikin jahilci kuma kowa nason cigaba a rayuwarsa domin yanzu wutsiyar raƙumi tayi nisa da ƙasa ka tafi Allah ya haɗa kowa da rabonsa na Alkhairi”.
fashewa da kuka Haladu yayi tare haɗa hannu biyu gaban Bappah yace”Bappah kaji abinda take cewa ai saki ɗaya nayimata ba ukuba aradu ka temakeni”.
“to yanzu ya kakeso ayimaka yarinyar nan haihuwar nan da tana yinta yazamana tagama iddah dadai kafin ta haihu ka faɗi hakan da ta mayu yanzu shikenan ka koma ƙauye Allah yabaka mace tagari tunda tace bata sonka kuma inbaka mantaba na faɗamaka bazan yiwa ƴata doleba saboda ita ba yarinya bace ke Khadijatu kinason Haladu?”.
“a’ah Bappah”.
“to kaji tun wuri ku kama gabanku tinkan dare yayimuku”.
kuka Haladu ya fashe dashi yayita magiya cikin takaicinsu Iyah tace”waiku wa’inne irin mayune ne ku tafi ku barmu muɗan sarara haba tinda tace bata auren seku tafi ana dolene”.
Haladu na kuka da Innarsa haka suka bar cikin asibitin suna fita Furera ta share hawayen daya zubomata ta rife idanunta tanajin wani iri a zuciyarta.

Fashewa da kuka Iyah tayi hakan yaja hankalin kowa na ɗakin ta tashi ta nufi gaban Ummita zata duƙa kenan Ummita ta riƙeta tace”meyafaru Iyah”.
a mamakin Ummita setaji Iyah tace”ki yafemun Sa’adatu na cutar da rayuwarki keda yaranki cuta mafi muni nasa a gari an tsaneku ana kyararku bakuda mesonku namanta da Allah shine meyi segashi yaran dana fifita akan naki suka watsamun ƙasa a ido kiyafemun dan Allah kona samu Allah ya gafartamun ace jikokina basu taɓa samun daɗin kakaba kullum cikin hantararsu nike da tsinemusu segashi Allah ya nunamun ishara dama haka duniya take kaƙi naka duniya tasoshi kitemakeni ki gafartamun”.
taƙarasa zancenta tare da fashewa da matsanancin kuka sharemata hawaye Ummita tayi tare da cewa”Iyah kidena kuka ni dama ban taɓa riƙarkiba saboda ke uwace a gareni na yafemiki suma su Hafsat nasan sun yafemiki Allah ya yafemana gabaki ɗaya”.
“Ameen Sa’adatu nagode Allah yayimiki Albarka”.
wani irin sanyi ne ya ziyarci Ummita a zuciyarta tace”Alhamdulillah Allah na godemaka”.
tana cikin maganar zuci wayarta tayi ƙara dubawa tayi tace”gama Hafsat nan takira bara na ɗaga”.
ɗagawa Ummita tayi tare da cewa”salamu Alaikum”.
“wa’alaikumus salam Ummita ya Fureran ta haihu”.
“eh ta haihu amma yaron ya koma”.
“ayya Allah ya jiƙansa ni nan ina tinanin nakusa zama uwa”.
“Ameen to sarki san girma Allah ya baki naki kema”.
“Ameen Ummita musha goyo tare dake dama yanzu Aunty Firdausi ta kirani wai sarkin makkah yabani kujerun makkah guda biyar dana kira Ammi na sanarmata setacemun wai abama Iyah da Bappah Shafi’u da Bappah Murtala da Furera da Yayah Idris shine nace bara in sanarmiki yayi ammafa a yau za’ah yimusu komai saboda tare zaku taho”.
“yayi Alhamdulillah ,Allah kema ya baki masu yimiki Allah yayimiki Albarka bara na saki a speaker sesuji da kansu”.
“Ameen Ummita toh”.
nan ta maimaita kukan daɗi Iyah ta fashe dashi tare da cewa”bani jikartawa ɗaya tamkar da dubu”.
Ummita ta miƙawa Iyah cikin kukan farinciki Iyah tace”Allahu akhbar Allah na godemaka jikata abar alfaharina ki yafemun abinda na aikata miki nasan na cutar dake ki yafemun segashi kuɗin dana tsana kune masu sharen kukana “.
taƙarasa tana mai fashewa da kuka wani sanyine ya ratsa zuciyar Hafsat saboda farincikin abinda kakarta take cewa yasata harda kuka murya na rawa tace”Iyah yau kece da bakinki kike cewa haka Allah na godemaka na yafemiki Iyah damani ban taɓa damuwaba saboda watarana se labari”.
“nagode Hafsatu Allah yayimiki Albarka yaƙara ɗaukakaki fiye da da”.
“Ameen Iyatah”.
nansukayi sallama kowa cikin farinciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button