HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Rungume Aunty Fido Ummita tayi tare da cewa”ƴar uwata rabin jikina wai yanaga duk wa’innann mutanan ne su waye su kuma”.
“ƴar ƙanwata kinga mijinki ga surukarki ga yayyen mijinki ga ɗiyoyin mijinki”.
kanta ne ya sake saramata taɗan cije leɓenta na ƙasa tace”yanzu na tinasu suma inasu Aunty Khadijat take naga bangantaba”.
dammm ƙirjin su Hajjo ya buga itada Aunty Fido Hajjo najin haka tace”kibari anjuma kwayi waya da ita tana gidanta”.
“toh Hajjo saboda inason jin muryar Aunty Khadija rabonda injita tin randa aka kaita gidan mijinta na ɓace”.
“toh ki kwantar da hankalinki Firddausi shiga dasu ciki nikuma bara nakira su Abbih ɗunku dasu Aminiyata da mutane na sanarmusu da anga Sa’adatu na”.
“toh”.
nanta shiga dasu ciki kowa ta nunamasa ɗakin daze zauna taja Ummita sukayi ɗakinta zama sukayi a gefan gado Ummita ta kama hannun ƴar uwarta tace”yanzu ƴaƴan Aunty Khadijat nawa?”.
“su ukune maza biyu mace ɗaya Auntynmu fa ta mutu gurin haihuwar ƙaramar ƴarta babban sunansa Farouk ,Abdallah dakuma Fatimah”.
wasu hawayene masu zafi suka wankewa Ummita fuska lokaci ɗaya cikin kuka tace”ashe ba rabon mu sake ganawa da ƴar uwata Allah ka jiƙanta kasa ta huta”.
“Ameen ya Allah haka nikesonji daga gareki ƙanwata ba kukaba ai babban ɗanta Hafsat take aure”.
“masha Allah ,Allah yabasu zaman lafiya”.
“ameen”.
shigowa Hajjo tayi tana waya tace”gata ma kaji muryarta Sa’adatu ga Abbih ɗinku”.
“toh Hajjo”.
nan Ummita ta anshi wayar ta kara a kunnenta bakinta ɗauke da sallama tace”Abbih ina yini “.
wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Abbih yace”sannu daughter yanzu Hajjo take sanar dani duk abinda yafaru mijinki ya sanar da ita komai ashe loosing memory kikayi su mijinki ne suka temakamiki wani ikon Allah kuma se Allah ya haɗa auren Hafsat da Farouk wannan abu yayi kyau nima gobe zanzo naga autata konaji daɗi dan yanzu jinike kamar nayi tsuntsu naganki Auta”.
“eh hakane Abbih to Allah ya kawoka lafiya”.
“Ameen ya Allah bani Maman taku”.
“toh”.
miƙawa Hajjo wayar tayi Abbih yace”haɗani da mutanen arziƙinnan da suka riƙemun ƴa ba tare da sun san wacece itaba nayi musu godiya”.
“toh bara nakaimusu”.
nan Hajjo ta tafi ɗakinsu Bappah tabashi wayar ansa yayi suka gaisa Abbih yayimasa godiya sosai sannan aka kaiwa Iyah Abbah nanma yayita yimata godiya.

Bayan fitar Hajjo Aunty Fido tasaka Ummita tayi wanka tasaka wasu haɗaɗun kaya lokaci ɗaya tsananin kamanninsu ya bayyana sejan ƴar uwarta takeyi da hira Hajjo tazo itama suka ɗaura ko wannensu cikin farinciki kafin kace meye wannan zance ya rewaɗe ko ina harsu Hafsat sosai sukaji daɗin abinda yafaru Hajjo seda takira Farouk ta shedamasa anga ƙanwar Umminsu data ɓace sosai yayi nuna farincikinsa yace”da gaske a ina aka ganta Hajjo”.
“zuwa sukayi nan Saudia zasuyi aikin Hajji”.
“masha Allah abani Momyn tawa nagaida ita insha Allahu a yau zanzo naganta”.
“toh gata bara abata in Allah yakaimu ana gama aikin Hajji zamu tafi gida za’ah gudanar da walima a Adamawa”.
“toh Allah yakaimu”.
miƙawa Ummita waya Hajjo tayi ansa tayi tana murmushi tace”Salamu Alaikum”.
lokaci ɗaya komai nasa ya tsaya sakamakon jin da yayi sak muryar Umminsa wasu siraren hawayene suka zubomasa yayinda murya na rawa yace”Momy anyini lafiya”.
hawayene yafara bin kuncin Ummita tace”ɗana ka dena kuka ubangijinmu yafimu sonta”.
sheshekar kukace taci ƙarfinsa kiiitttt ya kashe wayar share hawaye Ummita tayi taga ita Aunty Fido ke kallo saurin kauda kai tayi ƙarasawa Aunty Fido tayi kusa da ƴar uwartata takama hannunta ta haɗa da nata tace”nasan muryarki dayajine yasashi kuka ko”.
ɗagamata kai Ummita tayi alamar eh hakan yasa Aunty Fido ƙara cewa”kidena kuka kinji ze denanane saboda yaji muryarku iri ɗaya data Aunty Khadija ne shiyasa dole mutuwar ta dawomasa sabuwa”.
nan Aunty Fido tayita lallashinta saboda baƙaramin son junansu suke ba barinma Khadijat da Sa’adatu shaƙuwace me tsanani.

Ɓangaren F2 kukane ya kuɓucemasa sosai yake kukan kamar wani ƙaramin yaro yayinda yakejin wata irin muguwar tsanar Maimartaba na ƙara shigarsa seda yayi me isarsa sannan ya share hawayensa da hankynsa a aljihun wadonsa yashare hawayensa ya kalli tsadadden agogon hannunsa ya miƙe ya ɗauki wasu files guda biyu ya fita yana fita ya yaga wani yaro matashi wanda zasu iyayin sa’annin juna ya turo wata mata a keken guragu daka ganinsu kasan masu dashi ne mutumin yana kuka yana cewa”kitemakamun yadda Allah ya temakeki ita kaɗai ta ragemun a duniya mahaifinmu ya tsanemu inta mutu mu mukayi asara bamuda kuɗi ko Doctor F2 ɗinne ki barni naganshi”.
cikin masifa Nurse ɗinnan tace”bazaka ganshiba inkazo da kuɗi kaje ka biya a shiga da mahaifiyarka inko baku dasu ku tafi gida lokacin da kuka samu kwa dawo inkuma ta mutu ku kuka jiyo”.
cikin kakkausar murya sukaji muryar F2 yace”keeeh Dija dama abinda ake faɗamun akanki gaskiyane na wulaƙants patient idan sunzo Abigirl kitura wannan patient ɗin akaita theater ganinan zuwa”.
yaƙarasa maganarsa yana jifan Nurse Dija da wani kallon zaki gane kurenki yaron daya kawo matar ne yashiga godiya ba tare daya tsaya saurarensaba ya juya ya nufi office ɗinsa ya canza kaya yashiga theater seda yasha wahala kafin ya kammala ba tare daya kalli kowaba a theater room ɗin da muryarsa kamar an takuramasa dole yayi magana yace”akaita rest room sannan abata kulawa sosai ni zan wuce Saudiyya”.
“okay sir”.
nanya wuce yafita seda yafara zuwa office ɗinsa ya canza kaya sannan ya ɗauki files ɗinsa yashiga motarsa ya wuce gida.

Ɓangaren Abdallah ko yana shiga gida ya wuce bedroom ɗinsa yayi wanka yayi dialing number Salman bugu ɗaya ya ɗauka tare da cewa”ya ka dawone?”.
“eh na dawo kazo mu shiga mu gaida iyayen matar Hamma”.
“kaiwai bakasan abinda yike faruwaba ne ashe babar Hafsat itace ƙanwar Umminku data ɓace aketa nema”.
a zabure Abdallah yace”what aiko gani nan zuwa ammafa kaci amanata wlh dabaka kirani ka sanarmun ba kuma yanzu muka rabu da Al’ameen ɗinma yacemun anjuma ze shigo shida Malaminsu matar Hamma su gaida su Hajjo”.
“yimaza ka taho kafin ta huce”.
“aiko gani nan zuwa”.
zura jallabiya yayi cikin sauri ya nufi cikin gida yana zuwa yasamesu duk a falo ɗaga idon da zeyi yaga me kama da Umminsu sak lokaci ɗaya shima yashiga hawaye tashi Ummita tayi tare da buɗemasa hannuwanta ya tafi da gudu ya rungumeta bubbuga bayansa tashiga yi alamar lallashi har seda yayi shiru nan suka zauna suka gaisa suka shiga hira segasu Al’ameen suma nan suma sukayi joining kowa zuciyarshi cikeda farinciki.

A main falo yasamu su Adam sunata shan shisha sallama yayimusu a ƙasan maƙoshi amsa masa sukayi ya haura sama abinsa yana shiga bedroom ɗinsa ya wuce gurin drower madubi yasaka files ɗinda ya shigo dasu sannan ya cire kayan jikinsa ya ɗaura towel yashiga toilet seda ya jima sannan yafito sanye da rigar wanka da ɗan ƙaramin towel yana goge kansa ya zauna ya jona hand dryer ya busar da gashin kansa ya gyarashi tsaf sannan ya ɗaureshi da wani band yashiga shafa lotions ɗinsa masu daɗin ƙanshi yana gamawa yasaka kayan daya sabawa sakawa har sarƙa ya saka takalmi ya ɗauki phones ɗinsa harze fita sekuma yakoma gaban mirrior ya kalli kansa wani ƙasaitaccen mirmushi ne ya suɓucemsa ya furta “I love you My Angel inama zakiga wannan wankan nasan dolene ya tafi dake”.
yana faɗin haka yaƙara kallon madubi seyaga Hafsat kusa dashi ta sakarmasa murmushi yakai hannu zevtaɓata yaji wayam tsaki yayi tare da cewa”Allah ka temakeni inganta konaji daɗi a raina na bayyanamata soyayyata”.
yanata maganarsa har yafita babban falonsu inda yabarsu nan yasamesu kallon Adam yayi tare da cewa”ni zanje Saudiyya”.
“toh Allah ya tsare”.
“Ameen”.
nan yafita yashiga mota driver yajashi yakaishi Airport yashiga Jet ɗinsu suka tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button